'Yan Sanda Sun Kama Mutane 627, a Jiha 1 kadai An Kwato Bindigogin AK 47 Guda 27

'Yan Sanda Sun Kama Mutane 627, a Jiha 1 kadai An Kwato Bindigogin AK 47 Guda 27

  • Rundunar ’yan sandan Delta ta kama mutane sama da 627 tare da kwato makamai 144, ciki har da bindigogin AK-47 da AK-49
  • Kwamishinan ’yan sanda ya ce nasarorin sun samu ne ta hanyar dabarun tsaro na rarraba bayanan sirri da hadin kan al’umma
  • ’Yan sanda sun kuma kama manyan wadanda ake zargi da kisan tsohuwar alkaliya Ifeoma Okogwu, yayin da bincike ke gudana

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Delta – Rundunar ’yan sandan jihar Delta ta bayyana cewa ta kama mutane sama da 627 tare da kwato makamai 144 daban-daban a cikin shekara guda.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Abaniwonda Olufemi, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin taron manema labarai da aka gudanar a hedkwatar rundunar da ke Asaba.

'Yan sanda sun kama masu laifi 627 a shekara daya a Delta
Kwamishinan 'yan sandan jihar Delta, CP Abaniwonda Olufemi. Hoto: @DeltaPoliceNG
Source: Twitter

Jami'an 'yan sanda sun kwato makamai 144

Kara karanta wannan

Dakarun sojojin Najeriya sun bi sawun 'yan bindiga, sun gano mutane 3 a jihar Kano

CP Olufemi ya ce an shirya taron ne domin bayyana wa duniya irin ayyuka da nasarorin da rundunar ta samu daga watan Janairu 2025 zuwa yanzu, in ji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce, bisa umarnin Sufeto Janar na ’yan sanda, IGP Kayode Egbetokun, rundunar ta umarci jami’anta da su kasance masu taka-tsantsan, kwarewa da jajircewa wajen kare lafiyar al’umma.

A cewarsa, kokarin da aka yi ya haifar da kwato bindigogi 144, ciki har da bindigogin AK-47/AK-49 guda 27, bindigogin Beretta 25, bindigogin da aka kera su a gida 56 da harsasai guda 6,930.

Ya ce hakan ya rage karfin aikata laifuka na miyagun mutane a fadin jihar.

'Yan sanda sun cafke mutane 627

Kwamishinan ya kara da cewa daga cikin mutanen 627 da aka kama, akwai mutum 140 da ake zargi da fashi da makami da 113 masu garkuwa da mutane.

Ya kuma ce an kama wasu 125 da ake zargi da kisan kai, 187 ’yan daba ko ’yan kungiyar asiri, da kuma mutane 62 da aka kama kan laifin fyade.

Haka kuma, kwamishinan ya ce rundunar 'yan snadan ta kwato Naira miliyan 36 daga hannun masu garkuwa da mutane da suka karba matsayin kudin fansa.

Kara karanta wannan

Da gaske Tinubu na amfani da EFCC wajen kama 'yan adawa a Najeriya?

'Yan sanda sun ce sun kama wadanda suka kashe tsohuwar alkaliya a Delta.
Taswirar jihar Delta, inda aka kama masu laifuffuka 627 a shekara daya kadai. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An cafke makasan Mai shari'a Ifeoma

Rundunar 'yan sandan ta ce an kama manyan wadanda ake zargi da kisan tsohuwar alkaliya, Justice Ifeoma Okogwa, wadda aka kashe a gidanta ranar 24 ga Nuwamba 2025, in ji rahoton TVC.

A cewarsa CP Olufemi, jami’an sashen kisan kai na CID sun kama wani mai gadi mai suna Godwin Mngumi, wanda aka ce yana aiki a gidan tsohuwar alkalin, bayan an same shi da daya daga cikin wayoyinta.

Ya ce bayan bincike, wanda ake zargin ya amsa laifinsa tare da bayyana cewa ya gayyato wani abokinsa mai suna Nnaji Obalum, dan shekaru 21, domin aikata kisan.

CP Olufemi ya ce wadanda ake zargin sun amsa cewa a ranar 23 ga Nuwamba 2025, su uku sun shiga gidan marigayiyar, suka daure ta da igiya da kyalle sannan suka kashe ta.

Bututun mai ya yi bindiga a Delta

A wani labari, mun ruwaito cewa, kamfanin NNPCL ya tabbatar da fashewar bututun mai a kusa da kauyukan Tebijor, Okpele da Ikporo a Gbaramatu da ke jihar Delta.

Kara karanta wannan

An yi wa babban dan sanda dukan kawo wuka kan zargin sata? Rundunar ta magantu

Fashewar bututun ta tada hankalin jama’a, ganin irin muhimmancin yankin a harkar iskar gas da man fetur, da rashin sanin abin da zai biyo bayan karar da aka ji.

NNPC ta bayyana cewa abin da ya fi muhimmanci a wannan lokaci shi ne kare rayukan mazauna yankin da kuma kiyaye muhalli daga duk wata illa da fashewar ka iya haifarwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com