Dakarun Sojojin Najeriya Sun Bi Sawun 'Yan Bindiga, Sun Gano Mutane 3 a Jihar Kano
- Dakarun sojojin rundunar Operation MESA da hadin gwiwar 'yan sanda sun bi sawun 'yan bindigan da suka sace mutane biyar a jihar Kano
- Rahotanni daga rundunar sojojin kasa sun tabbatar da cewa zuwa yanzu jami'an tsaro sun ceto mutane uku, kuma sun matsa kaimi wajen ceto sauran
- Wannan nasara na zuwa ne bayan wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da mutane biyar lokacin da suka kai hari yankin karamar hukumar Gwarzo a Kano
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun samu nasara yayin da suka bi sawun 'yan bindigar da suka kai hari tare da sace mutane a karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano.
Dakarun Operation MESA da suka haɗa da sojojin kasa da na sama tare da haɗin gwiwar Rundunar ’Yan Sanda sun gano tare da ceto mutane uku daga cikin biyar da aka sace a kauyen Lakwaya a Kano.

Source: Original
Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kai sabon hari a garin Lakwaya, inda suka sace mutane biyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'an tsaro sun ceto mutum 3 a Kano
Da yake zantawa da manema labarai, Kyaftin Babatunde Zubairu, Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Kasa ta 3 Brigade, ya ce, “an riga an ceto mutane uku zuwa yanzu.”
A cewar majiyoyin daga yankin, lamarin ya faru ne a daren Lahadi a ƙauyen Zurin Mahauta, wanda hakan ya jefa al’ummar yankin cikin fargaba da tashin hankali.
Dagacin ƙauyen Zurin Mahauta, Murtala Mai Unguwa, ya ce 'yan ta'adda sun shiga yankin ne da dare, inda suka tafi da mutanen da aka sace zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Sojoji sun dauki matakin gaggawa
Ya ce an sanar da jami’an tsaro nan take, kuma abin farin ciki sun kawo dauki cikin gaggawa domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su, kamar yadda Tribune ta rahoto
Basaraken ya ƙara da cewa jami'an tsaron na ci gaba da ƙoƙarin bin sawun masu garkuwa da mutanen domin ceto sauran waɗanda aka sace.

Source: Twitter
Mazauna yankin da abin ya shafa sun nuna damuwa kan yawan hare-haren da ake fama da su a yankin, tare da kiran a ƙara tsaurara tsaron da zai kare rayuka da dukiyoyi.
Tun da farko, Kyaftin Zubairu ya tabbatar da cewa dakarun tsaro na yin iya ƙoƙarinsu domin tabbatar da dawowar waɗanda aka sace gida cikin koshin lafiya.
Sojoji sun hallaka kwamandan 'yan bindiga
A wani rahoton, kun ji cewa jiragen sojoji sun samu nasarar hallaka daya daga cikin manyan jagororin 'yan bindiga da suka addabi al'umma a jihar Neja.
An ruwaito cewa luguden wutan jiargen sojojin Najeriya ya hallaka Babangida, ɗaya daga cikin sanannun kwamandojin ’yan bindiga a karamar hukumar Shiroro.
Bayanai sun nuna cewa 'dan ta'addan na daya daga cikin jagorori kuma na hannun daman kasurgumin dan bindigar nan, Dogo Gide.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

