An Shiga Tashin Hankali a Kano: An Yi wa Ladani Yankan Rago cikin Masallaci
- Al’ummar Hotoro Maraba a Kano sun shiga firgici bayan wani matashi ya kashe ladanin masallaci a lokacin sallar Asubahi
- Rahotanni sun ce rikici ya fara ne bayan ladani ya ce lokacin sallah bai yi ba, lamarin da ya fusata matashin ya yanke makogoronsa
- ‘Yan sanda sun mamaye yankin domin hana barkewar tarzoma bayan fusatattun matasa sun yi kukan kura sun kashe matashin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano – An shiga firgici da tashin hankali a unguwar Hotoro Maraba da ke birnin Kano bayan wani matashi ya kashe ladanin masallaci a lokacin sallar Asubahin ranar Litinin.
Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da Asubah, inda matashin ya zo masallaci domin yin Sallah, ya tarar da ladan da wasu mutane uku a ciki.

Source: Facebook
Matashi ya kashe Ladani a Kano
Bisa bayanan da aka samu, matashin ya bukaci a tayar da sallah, amma ladan ya sanar da shi cewa lokacin sallar Asuba bai yi ba tukuna, in ji rahoton Aminiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nan take, aka ce matashin ya fusata, inda ya zaro wuƙa daga aljihunsa ya kai wa ladanin hari, ya soka masa a maƙogwaro, wanda ya yi sanadin mutuwarsa nan take.
Rahotanni sun ce bayan faruwar lamarin, matashin ya yi yunkurin tserewa, amma jama’ar unguwar suka cafke shi tare da yi masa duka har ya mutu.
An kashe matashin da ya kashe ladani
A halin yanzu, jami’an rundunar ‘yan sandan Kano sun mamaye unguwar Hotoro Maraba domin kwantar da tarzomar da ke shirin barkewa, bayan matasan yankin sun yi dandazo a gaban gidan matashin da ake zargi da aikata laifin, da nufin ƙone gidan.
Sai dai wasu rahotanni sun ce tuni fusatattun matasa suka kama matashin, suka yi ta dukansa har suka kashe shi shima.
Jami’an tsaro sun yi kokarin kwantar da hankulan jama’a tare da hana daukar doka a hannu, kuma an ce sun kwashe gawarwakin mutanen biyu.
Wani mazaunin Kano, Hon. Umar Mai Wayo, ya wallafa a shafinsa na Facebook yadda ya ce lamarin ya faru, inda ya bayyana cewa wanda ake zargi dan unguwar ne, ba bako ba.

Source: Facebook
Yadda abin ya faru a masallacin Kano
Ya ce bayan faruwar lamarin, jama’a sun yi jana’izar ladanin kamar yadda addinin Musulunci ya koyar, tare da yin addu’o’i na neman tsari daga sharrin miyagun mutane.
"Wannan shi ne bawan Allahn da wani mara imani ya kashe yau da Asubar Fari a Unguwar Hoton Maraba. Mutum ya zo har cikin masallaci da wuka, ya shake ladanin a makogoro, nan take ya cire makogoron ya sanya a aljihu.
"Zai fita sai Allah cikin ikonsa jama'a suka yi kukan kura suka dafe shi, sauka yi ta dukansa suna bugamar abu amma komai ya ki hawansa, da kyar Allah ya ba su nasara suka kwace wukar hannunsa suka kashe shi nan take."

Kara karanta wannan
Lamari ya munana: An hallaka matashi bayan zargin daɓawa mahaifiyarsa wuƙa a Niger
- Hon. Umar Mai Wayo.
Kalli hoton ladanin a kasa:
'Yan bindiga sun kai hari masallaci
A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kashe mutane akalla 13 su na tsakiyar sallar Asubah a kauyen Unguwan Mantau da ke jihar Katsina.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Katsina, Dr. Nasir Mu'azu ya bayyana harin a matsayin na ramuwar gayya da 'yan bindigar suka kai.
Dr. Nasir Mu'azu ya ce kwanaki biyu kafin harin mazauna kauyen suka yi wa yan bindiga kwantan bauna, suka kashe da dama, tare da suka ceto yan uwansu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
