'Yan Bindiga Sun kai Hari Kano cikin Dare, Sun Sace Wani Adadi na Mutane
- Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a yankin Lakwaya da ke karamar hukumar Gwarzo, inda suka yi awon gaba da mazauna yankin
- Rahoto ya nuna cewa harin ya faru ne da daddare a kauyen Zurin Mahauta, lamarin da ya jefa al’umma cikin fargaba da tashin hankali
- Hukumomin tsaro sun tabbatar da sace wani adadi na mutane a harin tare da fara kokarin ceto su daga hannun masu garkuwa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Tsaro ya sake tabarbarewa a wani bangare na jihar Kano bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai sabon hari a yankin Lakwaya da ke karamar hukumar Gwarzo, inda suka sace akalla mutum biyar.
Rahotanni daga yankin sun nuna cewa harin ya faru ne da daddare a kauyen Zurin Mahauta, inda maharan suka shigo cikin duhu suka firgita mazauna yankin kafin su tafi da wasu mutane zuwa inda ba a sani ba.

Source: Original
Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya sake tayar da hankalin al’ummar yankin, musamman ganin cewa ba wannan ne karo na farko da ake samun irin wadannan hare-hare ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka kai sabon hari a jihar Kano
Shugaban kauyen Zurin Mahauta, Murtala Mai Unguwa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun shigo kauyen ne cikin duhun dare.
A cewarsa, maharan sun yi anfani da rashin haske da kuma rashin zirga-zirgar jama'a wajen kai harin, inda suka yi awon gaba da mutum biyar ba tare da samun wata gagarumar turjiya ba.
Rahoton Aminiya ya nuna cewa ya ce bayan faruwar lamarin, an gaggauta sanar da jami’an tsaro domin daukar mataki cikin hanzari.
Murtala Mai Unguwa ya kara da cewa jami’an tsaro sun amsa kiran gaggawa da wuri, kuma aka fara kokarin bin sawun ‘yan bindigar domin gano inda suka kai mutanen da aka sace.
Martanin jami’an tsaro kan harin Kano
A martanin da sojoji suka yi, kakakin rundunar sojin runduna ta 3, Kyaftin Babatunde Zubairu, ya tabbatar da cewa mutum biyar ne aka sace a harin.
Kyaftin Babatunde Zubairu ya bayyana cewa dakarun soji da ke yankin sun tashi tsaye wajen ganin an ceto wadanda aka sace cikin koshin lafiya.
“Mutum biyar ne kawai aka sace, kuma muna kokarin ganin mun dawo da su lafiya. Dakarunmu suna yin iya bakin kokarinsu,”
Inji shi

Source: Facebook
A halin yanzu, idon al’umma na kan kokarin da jami’an tsaro ke yi domin ceto mutanen da aka sace, tare da fatan ganin an dakile irin wadannan hare-hare a nan gaba.
'Yan bindiga sun kai hari jihar Kogi
A wani labarin, kun ji cewa wasu 'yan bindiga masu garkuwa da mutane sun kai hari wani coci a jihar Kogi sun sace mutane.
Wani da ya shaida harin ya bayyana cewa maharan sun bude wuta kan jama'a kafin daga bisani su nufi coci su sace mutum daya.
Kwamishinan yada labaran jihar ya tabbatar da cewa sun yi Allah da harin tare da bukatar jami'an tsaro su ceto wadanda aka sace.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


