Bayan Ganin Bidiyon Bello Turji, APC Ta Hango Dalilin Alakanta Matawalle da 'Yan Bindiga
- APC ta yi martani kan zargin da ake yi wa karaminin ministan tsaro, Bello Muhammad Matawalle na cewa yana alaka da 'yan bindiga
- Mai magana da yawun APC reshen jihar Zamfara, Yusuf Idris Gusau ya ce bidiyon da dan bindiga, Bello Turji ya saki ya fallasa komai
- Jam'iyyar ta zargi gwamnatin Zamfara da daukar nauyin wasu mutane domin yada wannan zargi da nufin raba Matawalle da mukaminsa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Jam'iyyar APC ta kare karamin ministan tsaro, Bello Matwalle daga zargin da ake masa na alaka da ayyykan 'yan bindiga a Zamfara.
APC ta yi fatali da zarge-zargin da ake jinginawa tsohon gwamnan Zamfara, ta ce kulle-kulle ne na siyasa da aka kirkiro ba don komai ba sai don bata sunan ministan.

Kara karanta wannan
Matawalle: Kungiya ta ba Tinubu shawarar abin da ya dace da karamin Ministan tsaro

Source: Original
APC ta yi martani kan zargin Bello Matawalle
Leadership ta ruwaito cewa hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na APC reshen jihar Zamfara, Yusuf Idris Gusau, ya fitar a ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam’iyyar ta ce karyata zargin da shugabannin ’yan bindiga suka yi a fili game da duk wata alaƙa da Matawalle, ya nuna ikirarin da ake yaɗawa a kansa karya ne.
Idan ba ku manta ba, hatsabibin dan bindigar nan, Bello Turji ya fito ya karyata zargin cewa yana da alaka da Matawalle, ya ce bai taba karbar kudi a hannun tsohon gwamnan ba.
APC ta kafa hujja da maganganun Bello Turji, tana mai cewa ya nuna a fili cewa zargin da ake yi wa Bello Matawalle ba gaskiya ba ne, shiri ne na siyasa, in ji rahoton Guardian.
Jam'iyyar APC ta zargi Gwamnatin Dauda Lawal
A cewar APC, duk da haka, gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal na ci gaba da yaɗa labaran da ke zargin Matawalle, da nufin matsa wa Shugaba Bola Tinubu lamba ya cire shi daga mukaminsa.
APC ta kuma yi zargin cewa gwamnatin Zamfara na amfani da kuɗaɗen jama’a wajen tara mutane da ƙungiyoyi, ciki har da malaman addini, ’yan siyasa da masu zanga-zanga, domin ƙarfafa zargin da ke alaƙanta Matawalle da ’yan bindiga.
Ta ce an tura wasu daga cikin waɗannan mutane zuwa yankunan Arewa da Kudu domin yaɗa wannan labari na karya inda ta ƙara da cewa ɗaya daga cikin mutanen ya amsa cewa ya karɓi kuɗi daga gwamnatin Zamfara.

Source: Facebook
APC ta Zamfara ta yi kira ga hukumomin tsaro, Hukumar Shari’a ta Ƙasa (NJC), Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) da ƙungiyoyin farar hula da su binciki yadda aka saki Musa Kamarawa alhali shari’arsa na gaban kotu.
Matawalle ya musanta zargin alaka da yan bindiga
A wani labarin, kun ji cewa Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya sake fitowa tare da kare kansa game da zargin alaka da 'yan ta'adda.
Matawalle ya ce duk wani zargi da bai tabbata ba, bai zama gaskiya ba har sai an je kotu an yi shari'a kafin sanin gaskiyar al'amarin.
Tsohon gwamnan na Zamfara ya kuma zargi masu alakanta shi da ta'addanci da cewa suna kokari ne kawai domin ganin ya bar ma'aikatar tsaro.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
