Magana Ta Kare: Kotun Koli Ta Fayyace Ikon Tinubu wajen Dakatar da Zababben Gwamna

Magana Ta Kare: Kotun Koli Ta Fayyace Ikon Tinubu wajen Dakatar da Zababben Gwamna

  • Kotun Koli ta yanke hukunci game da ikon shugaban kasa na na ayana dokar ta-baci a jihohi da dakatar da zababbun jami'an gwamnati
  • Kotun ta yi watsi da karar da jihohin PDP 11 suka shigar, na adawa da dokar ta-baci da Shugaba Bola Tinubu ya ayyana a jihar Rivers
  • Sai dai, an samu alkali daya da ya yi adawa da cikon shugaban kasa na dakatar da zababbun gwamnoni da 'yan majalisun jihohi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Kotun Koli ta tabbatar da cewa shugaban kasa na da cikakken ikon kundin tsarin mulki na ayana dokar ta-baci a jihohin Najeriya.

A hukuncin da ta yanke, Kotun Koli ta ce shugaban kasa zai iya ayyana dokar ta baci idan jihohi na fuskantar rushewar doka ko fadawa cikin rikici.

Kara karanta wannan

Da gaske Tinubu na amfani da EFCC wajen kama 'yan adawa a Najeriya?

Kotun Koli ta tabbatar da cewa Tinubu na da ikon ayyana dokar ta baci a jihohi.
Shugaba Bola Tinubu ya na jagorantar taron majalisar zartarwa (FEC) a fadar shugaban kasa, Abuja. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Da wannan hukunci da aka yanke, jaridar The Nation ta rahoto cewa kotun koli ta kawo karshen shari'ar da gwamnonin PDP suka shigar gabanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta tabbatar da ikon shugaban kasa

Kotun ta yi watsi da karar, tana mai cewa wadanda suka shigar da karar—jihohi 11 da jam’iyyar PDP ke mulki (a lokacin)—sun kasa nuna wata hujja da za ta bai wa kotun damar amfani da ikon shari’arta na asali.

Alkalai biyar ne suka amince da watsi da wannan kara yayin da alkali daya kawai ya nuna adawa da wani bangare na shari'ar.

Idan ba a manta ba, Jihar Adamawa da wasu jihohi 10 na PDP ne suka shigar da karar, domin kalubalantar ayyana dokar ta baci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a jihar Rivers.

Jihohin sun kalubalanci matakin ayyana dokar, wanda ya hada da dakatar da zababbun jami’an jihar na tsawon watanni shida, ciki har da Gwamna Siminalayi Fubara.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamna Abba ya dauki sabon mataki don kare rayuka a Kano

Sashen da kotu ta dogara da shi a hukunci

Da farko dai kotun ta fara amincewa da ƙorafe-ƙorafen farko kan ikon yin shari’ar, amma duk da haka ta zurfafa nazari kan batun, inda daga bisani ta yanke hukuncin watsi da karar gaba daya.

Alkali Mohammed Idris, wanda ya jagoranci karanta hukuncin, ya ce masu karar sun kasa nuna cewa akwai wata takaddama ta shari’a tsakaninsu da tarayya da za ta wajabta wa kotun amfani da ikon shari’arta na asali.

Ya jaddada cewa sashe na 305 na kundin tsarin mulkin 1999 ya bai wa shugaban kasa ikon daukar matakan gaggawa domin dawo da zaman lafiya a lokacin da ake fuskantar matsanancin hali.

Kotun Koli ta ce shugaban kasa zai ayyana dokar ta baci a jihohi idan za a samu rushewar doka da oda.
Ginin Kotun Koli da ke babban birnin tarayya Abuja. Hoto: @segalink
Source: Facebook

Alkali 1 ya nuna adawa kan ikon Shugaban kasa

Kotun ta bayyana cewa ko da yake sashe na 305 bai fayyace dukkan matakan da za a iya dauka ba, ya bada damar daukar matakai na musamman, in ji rahoton The Cable.

Daga cikin matakan da kotun ta ce shugaban kasa zai iya dauka, har da dakatar da zababbun jami’ai na wani lokaci, muddin matakan ba su wuce iyakar lokaci ba.

Kara karanta wannan

Matawalle: Kungiya ta ba Tinubu shawarar abin da ya dace da karamin Ministan tsaro

Da yake nuna adawa, Mai shari'a Obande Ogbuinya ya ce duk da cewa shugaban kasa na da ikon ayyana dokar ta-baci, wannan ikon bai kai ga dakatar da zababbun jami’an dimokuradiyya ba, ciki har da gwamna, mataimakinsa da ‘yan majalisa.

Tinubu ya nemi a kori karar gwamnonin PDP

Tun da fari, mun ruwaito cewa, shugaban kasa ya bukaci kotun koli ta yi watsi da karar gwamnonin PDP da ke kalubalantar dokar ta baci da dakatar da gwamnan Rivers.

Lauyan gwamnatin Najeriya, kuma ministan shari'a ya ce kotun koli ba ta da hurumin sauraron karar, domin ba ta shafi rikici tsakanin jihohi da tarayya kai tsaye ba.

A takardar ƙin yarda da karar da ministan ya gabatar a ranar 9 ga Mayu, 2025, ya ce ihohin ba su bayyana wani rikici tsakaninsu da Tarayya ba, ko wata doka da aka karya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com