Da Gaske Tinubu na Amfani da EFCC wajen Kama 'Yan Adawa a Najeriya?

Da Gaske Tinubu na Amfani da EFCC wajen Kama 'Yan Adawa a Najeriya?

  • Manyan jagororin adawa sun zargi gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da amfani da hukumomin tsaro wajen raunana jam’iyyun hamayya
  • Hakan na zuwa ne bayan kama wasu manyan 'yan adawa kamar tsohon minista, Abubakar Malami da ya ce zai yi takarar gwamna a ADC a 2027
  • Fadar shugaban kasa ta karyata zargin 'yan adawa, tana mai cewa EFCC na aiki ne bisa doka ba tare da tsoma bakin shugaba Bola Tinubu ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ana musayar yawu tsakanin fadar shugaban kasa da ‘yan adawa bayan zargin da aka yi cewa Bola Ahmed Tinubu na amfani da ikon gwamnati domin matsin lamba kan jam’iyyun adawa.

Zargin ya fito ne daga bakin manyan ‘yan siyasa ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyya LP a 2023 Peter Obi, da dattijo a PDP, Bode George.

Kara karanta wannan

APC: Atiku da manyan 'yan adawa sun taso Tinubu a gaba game da mamaye Najeriya

"Yan adawar Najeriya da Tinubu
Atiku Abubakar, Peter Obi da shugaba Bola Tinubu. Hoto: Paul O Ibe, Peter Obi, Bayo Onanuga
Source: Facebook

A martani, hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X cewa wadannan zarge-zarge ba su da tushe.

Zargin da ‘yan adawa ke yi wa Tinubu

A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da aka fitar ranar Lahadi, jagororin adawar sun ce ana karkatar da ikon kasa domin gallazawa da tsoratar da abokan hamayya maimakon yakar cin hanci.

Sanarwar, wadda David Mark, John Odigie-Oyegun da Lawal Batagawara suka sanya wa hannu, ta bukaci a gudanar da cikakken bincike kan asusun tarayya, jihohi da kananan hukumomi daga 2015 zuwa 2025.

Sun yi zargin cewa hukumomi kamar EFCC, ‘yan sanda da ICPC na nuna bangaranci, suna tsananta wa ‘yan adawa yayin da ake sassauta wa ‘ya’yan jam’iyya mai mulki.

'Yan hamayya sun ce ana ganin yawaitar sauya sheka zuwa APC, ciki har da gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara, a matsayin alamar matsin lamba ba wai sauyin akida ba.

Kara karanta wannan

Ana rade radin Yakubu Gowon ya mutu, an hango tsohon shugaban kasa a Aso Rock

Sun kara da cewa akwai wata manufa ta boye na kwace ikon jihohi daga hannun 'yan adawa kafin zaben 2027, lamarin da ka iya barazana ga dimokuradiyya a Najeriya.

Zargi kan EFCC da martanin wasu jihohi

'Yan adawa sun kuma yi nuni da abin da suka kira zaben wanda za a gurfanar, suna ambaton kalaman tsohon shugaban APC, Adams Oshiomhole da ya taba cewa idan mutum ya shiga APC “an yafe masa laifuffukansa”.

A Kebbi, jam’iyyar ADC ta soki tsare tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami, tana cewa matakin ya sabawa doka kuma siyasa ce ta haifar da shi.

Tsohon ministan Najeriya da EFCC ta kama
Tsohon minista kuma dan adawa da EFCC ta kama. Hoto: Abubakar Malami SAN
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa Malami ya karyata dukkan zarge-zargen da ake yadawa a kansa, yana cewa karya ne.

Martanin fadar shugaban kasa kan zargin

Fadar shugaban kasa ta yi watsi da dukkan zarge-zargen, tana mai bayyana su a matsayin yunkurin neman uzuri daga jam’iyyun da ke neman rugujewa.

Bayo Onanuga ya jaddada cewa EFCC hukuma ce mai cin gashin kanta, wadda ke gudanar da aikinta bisa doka ba tare da umarni daga shugaban kasa ba.

Onanuga ya ce ya kamata duk wanda ake tuhuma ya tsaya ya kare kansa a gaban kotu, yana mai cewa babu wanda ya fi karfin doka.

Kara karanta wannan

"A bayyane yake": An hango abin da Tinubu zai yi wa Shettima a zaben 2027

EFCC ta cafke tsohon minista, Ngige

A wani labarin, kun ji cewa hukumar EFCC ta kama tsohon minista a lokacin Muhammadu Buhari, Dr Chris Ngige.

Hadimin tsohon ministan ne ya bayyana haka bayan an fara rade-radin cewa 'yan bindiga ne suka sace shi.

Wasu rahotanni sun ce an kama Ngige ne bisa zarge-zarge da ke da alaka da makudan kudin kwangila da aka karkatar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng