"Sako Ya Kai ga Shugaban Ƙasa:" Sheikh Asada Ya Shirya Zuwa Kotu da Matawalle
- Malamin addini, Sheikh Murtala Asada, ya ce sakonsa game da zarge-zargen da ya yi wa Bello Matawalle, ya kai ga Fadar Shugaban Ƙasa
- Sheikh Asada ya jaddada cewa a shirye ya ke ya gurfana a gaban kotu, yana mai cewa yana da hujjoji kan zarge-zargen da yake yi wa tsohon gwamnan
- Ya bayyana takaici game da yadda duk da irin waɗannan munanan zarge-zarge, Matawalle ya ci gaba da zama a kujerarsa ta Minista
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara – Malamin Musulunci, Sheikh Murtala Asada ya sake jaddada zarge-zargen da ya dade yana yi kan Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, yana mai cewa sakonsa ya kai ga Fadar Shugaban Ƙasa.
Wannan martani na zuwa ne bayan Ministan tsaro ya yi hira da wani gidan jarida, inda ya ƙalubalanci duk mai da'awar yana da alaka da ƴan ta'adda ya kai shi kotu.

Source: Facebook
A wani rubutu da Musa Kiliya ya wallafa a shafinsa na X, Sheikh Asada ya ce Matawalle ya tura tsohon kwamishinansa don mayar da martani kan zarge-zargen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Murtala Asada ya yi martani ga Bello Matawalle
Fitaccen Malamin ya kara da cewa daga bisani an ruwaito Bello Turji ya fito yana musanta dukkanin ikirarin, amma ya jaddada cewa hakan bai isa ya soke abin da ya fada ba.
A cewarsa, wannan batu ba sabon abu ba ne, domin tun a shekarar farko ta mulkin Matawalle a matsayin gwamnan Zamfara ya fara bayyana irin wadannan zarge-zarge, kusan shekaru biyar da suka wuce.

Source: Original
Malamin ya ce ya kalli wani bidiyo mai tsawon mintuna 42 inda aka ga Matawalle yana cewa an raba abincin dabbobi ga ‘yan bindiga a madadin tattaunawar zaman lafiya.
Ya kuma dage ce dole Matawalle ya amsa tambayoyi kan abubuwan da ake zarginsa da aikatawa na aiki da ƴan ta'addan da ke jefa jama'a a matsala.

Kara karanta wannan
Bello Turji ya fadi gaskiya kan alakanta shi da Matawalle, ya kira sunaye a bidiyo
Sheikh Asada ya shirya zuwa kotu
Sheikh Murtala Asada ya bayyana cewa yana shirye ya je kotu domin kare kansa da zarge-zargen da ya yi, domin ba haka kawai ya yi kalaman ba.
Ya ce babu wani Kwamishinan Matawalle da ya ƙaryata duk abin da ya fada a cikin zarge-zargen da ya yi.
A cewarsa, yana da hujjoji masu zaman kansu da zai gabatar idan aka kai batun gaban shari’a.
Haka kuma, ya yi ikirarin cewa Matawalle ya yi yunkurin hana Musa Kamarawa bayyana a kotu a matsayin shaida tare da Sheikh Murtala Asada, ta hanyar yi masa alkawarin ba shi duk abin da yake bukata.
Malamin ya yi tambaya, yana neman dalilin da ya sa, duk da ikirarin cewa ba shi da alaka da ‘yan bindiga, ake ci gaba da bibiyar Musa Kamarawa.
Ya kuma dage kan zargin cewa Matawalle ya sayi motoci ga wasu fitattun ‘yan bindiga da suka hada da Bello Turji, Halilu Sububu da Haru Doli.
Ahmad Gumi ya goyi bayan Matawalle
A baya, kun ji cewa fitaccen malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi, ya yi magana kan muhawarar da ke tattare da kujerar karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle.
Malamin ya ce Matawalle na daga cikin shugabannin da suka fahimci ainihin tushen matsalolin tsaro, kuma suka yi ƙoƙarin magance su ta hanyoyi masu zurfi tun a baya. A cewarsa, Matawalle ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaro, musamman a lokacin da yake rike da mukamin gwamnan Jihar Zamfara.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

