Tsohon Shugaban Kasa, Gowon Ya Mutu? Hadiminsa Ya Fito da Gaskiya

Tsohon Shugaban Kasa, Gowon Ya Mutu? Hadiminsa Ya Fito da Gaskiya

  • Hadimin tsohon shugaban mulkin soja, Janar Yakubu Gowon, ya yi karin haske bayan jita-jitar cewa dattijon ya riga mu gidan gaskiya
  • Adeyeye Ajayi ya musanta jita-jitar rasuwarsa, yana bayyana ta a matsayin labarin karya wanda bai kamata mutane suna yarda ba
  • Ajayi ya ce Gowon na cikin koshin lafiya kuma har yanzu yana halartar tarukan jama’a domin bayar da gudunmawa ga ci gaban Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - An yi ta yada wasu rahotanni a Najeriya game da tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Yakubu Gowon.

Kamar yadda aka saba, an yada cewa tsohon shugaban kasar ya yi bankwana da duniya yana da shekaru 91 a duniya.

An karyata mutuwar Yakubu Gowon
Tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon. Hoto: @ArcSadam.
Source: Twitter

Sai dai hadiminsa ya fito musamman ya yi bayani kan jita-jtar da ake yadawa kan mai gidansa inda ya shawarci al'umma, cewar rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

"A bayyane yake": An hango abin da Tinubu zai yi wa Shettima a zaben 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka yi ta yada mutuwar Gowon

Wannan ba shi ne karon farko ba da wasu tsiraru ke tashi kawai su yada cewa tsohon shugaban kasar ya yi bankwana da duniya.

Na baya-baya da ake yada shi ne tsohon shugaban kasa na mulkin soja wanda aka yi rade-radin cewa ya mutu a ranar Litinin, 9 ga watan Oktoban 2023.

Sai dai kuma, Gowon ya yi watsi da jita-jitar cewa yana nan da ransa kuma ba gaggawan tafiya yake yi ba.

Hakan ya kuma faruwa a 2017 inda wasu kafofin yada labarai suka yi kuskuren yada cewa Gowon ya rasu yana da shekaru 79.

Hadimin Gowon ya musanta labarin mutuwar mai gidansa
Tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon yayin taro. Hoto: Yakubu Gowon.
Source: Facebook

Hadimin Gowon ya magantu kan jita-jitar mutuwar

Mista Adeyeye Ajayi ya musanta mutuwar Janar Yakubu Gowon (mai ritaya) yana bayyana ta a matsayin labarin karya.

Ajayi ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya bukaci al’ummar Najeriya su yi watsi da jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

Gwamna Adeleke zai cigaba da cire kunya yana tika rawa a bainar jama'a

A cewarsa, Janar Yakubu Gowon na cikin koshin lafiya, kuma har yanzu yana halartar tarukan jama’a daban-daban, inda yake ci gaba da taka rawarsa a matsayin muryar hankali, hadin kai da goyon bayan ci gaban Najeriya.

Ya ce tsohon shugaban na nan daram, yana bayar da shawarwari masu ma’ana da gudunmawa wajen karfafa zaman lafiya, hadin kai da cigaban kasa, sabanin labaran karya da ake yadawa a shafukan sada zumunta.

Ajayi ya jaddada cewa babu gaskiya a cikin labarin rasuwar Gowon, yana mai kira ga jama’a da su rika tantance sahihancin labarai kafin yada su, musamman a wannan zamani na yaduwar labaran bogi.

Gowon ya halarci bukukuwan Kirsimeti a Abuja

Mun ba ku labarin cewa tsohon shugaban ƙasa Yakubu Gowon ya halarci taron sharar fagen bukukuwan Kirsimeti a Aso Rock, ana tsaka da jita-jitar ya mutu.

Ganin Yakubu Gowon a fadar shugaban kasa ya karyata rahotannin da ake yadawa a soshiyal midiya cewa ya mutu a Landan.

Manyan mutane ciki har da Obasanjo, Akume da Ooni na Ife sun halarci carols, inda Gowon ya karanta darasi na farko daga Injila.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.