Tsohon shugaban kasa Gowon ya rasu?

Tsohon shugaban kasa Gowon ya rasu?

Ana ta faman yada cewa tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon ya samu cikawa. Sai dai wannan labari ya rudar da ‘Yan Najeriya. Shin da gaske ne Gowon din ya cika ko kuwa?

Tsohon shugaban kasa Gowon ya rasu?
Tsohon shugaban kasa Gowon ya rasu?

Gidan yada labarai na NTA na kasa ya sanar da cewa tsohon shugaban kasar Najeriya Yakubu Gowon ya samu cikawa gidan gaskiya. NTA ta ce shugaban ya bar Duniya ne yana mai shekaru 79 da haihuwa yayin da ake haska labarai.

Sai dai da alamu subuta ce aka yi don kuwa wata mata ce mai suna Martha Kande Audu ta cika. Martha tayi aiki da gidan rediyo da talabijin na Jihar Kaduna wanda asali ma ita ce macen farko da aka fara jin muryar ta a gidan rediyon.

KU KARANTA: PDP ta maidawa Obasanjo martani

Tsohon shugaban kasa Gowon ya rasu?
Tsohon shugaban kasa Gowon ya rasu?

Martha Kande Audu ‘yar uwar tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon ce kuma ta rasu tana da shekaru 79 a Duniya. Wannan kuskure dai ya sa jama’a da dama cikin rudu. Yakubu Gowon ya mulki kasar na shekaru kusan 9 a lokacin yakin basasa na Biyafara.

A jiya ne kuma shugaba Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban kasa Obasanjo murnar cikan sa shekara 80 a Duniya. Shugaba Muhammadu Buhari ya jinjinawa Olusegun Obasanjo ta wayar tarho daga Landan. Shugaba Buhari ya kira Obasanjo ya cigaba da kokarin kawo hadin-kai.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel