Najeriya: An Bankado 'Wani Shiri' na Kashe Kiristocin Arewa a Ranar Kirsimeti

Najeriya: An Bankado 'Wani Shiri' na Kashe Kiristocin Arewa a Ranar Kirsimeti

  • Watan kungiya, Equipping The Persecuted ta yi zargin cewa za a kai hare-hare kan Kiristoci a ranar Kirsimeti a wasu sassan Arewa
  • Fadar shugaban kasa ta nuna shakku kan gargadin, tana mai cewa rahoton na iya haddasa fargaba da firgici a tsakanin ’yan Najeriya
  • Sai dai, wasu majiyoyi daga DSS sun tabbatar da cewa hukumar na da bayanan sirri kan yiwuwar hare-haren, kuma har an dauki matakai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar Equipping The Persecuted ta yi ikirarin cewa ana shirin kai hare-haren ta’addanci a wasu garuruwan Kiristoci a Arewacin Najeriya a ranar Kirsimeti.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa ta samu bayanan sirri masu inganci da ke nuna cewa ’yan ta’adda na sake taruwa domin kai hare-hare a wasu jihohin Plateau, Nasarawa, Benue da Kaduna.

Kara karanta wannan

Ana rade radin Yakubu Gowon ya mutu, an hango tsohon shugaban kasa a Aso Rock

DSS ta tabbatar da cewa ta samu bayanan sirri na kai hare-hare a ranar Kirsimeti
Jami'an hukumar DSS a bakin aiki. Hoto: @OfficialDSSNG
Source: Facebook

Kungiya ta yi gargadi a taron Washington DC

Sai dai fadar shugaban kasa ta yi gaggawar mayar da martani, inda ta nuna shakku kan sahihancin zargin tare da cewa rahoton na iya jefa jama’a cikin fargaba ba tare da hujja ba, in ji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanda ya kafa Equipping The Persecuted, Judd Saul, ne ya bayyana gargadin yayin wani taron tattaunawa da Kwamitin Duniya kan Najeriya da African Jewish Alliance suka shirya a Washington DC, Amurka.

Taron, wanda aka gudanar ranar Laraba, tsohon dan majalisar wakilai ta Amurka Frank Wolf ne ya jagoranta, tare da halartar wasu sanatoci da ’yan majalisar dokoki.

Rahotanni sun nuna cewa taron ya samu halartar Riley Moore, Chris Smith, Sanata James Lankford, da wakilan hukumar Amurka ta kasa da kasa kan 'yancin addini, tare da wasu ’yan Najeriya.

Zargin shirin kai hari a ranar Kirsimeti

A cewar Judd Saul, ’yan ta’adda sun fara sake taruwa a yankuna daban-daban domin kai hare-hare a ranar Kirsimeti, a cewar Sahara Reporters.

Kara karanta wannan

"A bayyane yake": An hango abin da Tinubu zai yi wa Shettima a zaben 2027

Ya ce an gano motsinsu a kan iyakokin Plateau da Nasarawa, Nasarawa da Benue, da kuma Nasarawa da Kaduna, inda ake zargin suna shirin kai hari a Riyom, Bokkos, Kafanchan da Agatu.

Saul ya ce sun samu bayanai masu karfi da ke nuna ana tara makamai domin kisan jama’a a ranar Kirsimeti, yana mai rokon gwamnatin Najeriya da Shugaban Amurka Donald Trump su dauki mataki cikin gaggawa.

Daga cikin garuruwan da ake zargin za a farmaki Kiristoci akwai Filato.
Taswirar jihar Filato. Hoto: Legit.ng
Source: Original

DSS ta ce ta riga ta dauki matakan kariya

Wani babban jami’in Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) a Abuja ya tabbatar da cewa hukumar ta samu bayanan sirri kan yiwuwar hare-haren Kirsimeti.

Jami'in wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa jaridar Punch cewa DSS ta riga ta fara daukar matakan kariya domin dakile duk wani shiri na kai hari.

Wani jami’in ya kara da cewa hare-haren a yankin Middle Belt kan faru ne musamman a lokutan bukukuwa, amma ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro na kan lamarin tun kafin fitowar rahoton kungiyar agaji.

Amurka ta fara saukowa kan zargin kisan Kiristoci

A wani labari, mun ruwaito cewa, 'dan majalisar Amurka Riley Moore ya ce ganawarsa da Nuhu Ribadu ta buɗe sabuwar kofar fahimtar juna game da zargin kisan Kiristoci a Najeriya.

Kara karanta wannan

NLC: 'Yan kwadago sun saka ranar zanga zanga a jihohi 36 da Abuja

Moore ya ce matakai da shirye-shiryen da aka tattauna tsakaninsa da jami’an gwamnati, wadanda idan aka aiwatar da su za su inganta tsaro ga dukkanin ‘yan Najeriya.

Ya kara da cewa damuwar Amurka game da rikice-rikicen Najeriya ta samu karɓuwa, yana yabawa gwamnati saboda bisa yadda ta amince a tattauna game da matsalar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com