‘Yana kan Daidai’: Gumi Ya Goyi Bayan Matawalle, Ya Fadi Tasirinsa a Zamfara

‘Yana kan Daidai’: Gumi Ya Goyi Bayan Matawalle, Ya Fadi Tasirinsa a Zamfara

  • Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya yabawa karamin ministan tsaro, Bello Matawalle kan taka rawar gani wajen samar da tsaro a Zamfara
  • Sanannen malamin fikihun ya bayyana cewa a zamanin Matawalle, manyan hanyoyin Gusau–Anka–Gummi sun kasance lafiya
  • Gumi ya ce nada tsohon gwamnan na jihar Zamfara a matsayin karamin ministan tsaro ya dace, yana kira da a kauce wa siyasantar tsaro

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya yi magana game da kujerar karamin ministan tsaro, Bello Matawalle.

Malamin ya ce Matawalle na daga cikin mutane da suka taka rawa wurin tabbatar da an samu tsaro tun a baya.

Gumi ya yabawa kokarin Matawalle
Malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi. Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi.
Source: Twitter

Ahmad Gumi ya goyi bayan Bello Matawalle

Sheikh Gumi ya bayyana haka a cikin wani rubutu a shafinsa na Facebook a yau Asabar 13 ga watan Disambar 2025.

Kara karanta wannan

Gwamna Bago ya goyi bayan wa'adi 1 a mulki, ya fadi amfaninsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya ce masana harkar tsaro na sojoji sun yi gargadi cewa rikice-rikicen al’umma ba a magance su yadda ya kamata ta hanyar amfani da ƙarfi kaɗai ba.

Ya ce bangaren amfani da soja bai wuce kashi 25 cikin 100 wurin yaki da ta'addanci.

Ya ce:

"Ministan nan yana daga cikin gwamnonin da suka fahimci wannan gaskiya tun lokacin da yake gwamnan Jihar Zamfara, inda kare rayukan al’umma ya kasance abin da ke damunsa.
"Ta hanyar tuntubar bangarorin da ke rikici da juna, ya kusa kawo karshen ayyukan ’yan bindiga a jihar."
Sheikh Gumi ya yaba kokarin Matawalle kan tsaro
Sheikh Ahmad Mahmud Gumi da Bello Matawalle. Hoto: Dr. Bello Matawalle, JIBWIS Nigeria.
Source: Facebook

'Kokarin da Matawalle ya yi a Zamfara'

Sheikh Gumi ya ce a zamanin mulkin Matawalle, ya bada gudunmawa sosai musamman hanyoyin Gusau zuwa Anka da Gumi sun kasance lafiya.

Ya tabbatar da cewa ya yi tafiya daga Wurno zuwa Shinkafi har Gusau inda ya ce tsawon shekaru hanyoyin sun kasance lafiya.

"A zamaninsa, hanyar Gusau–Anka–Gummi ta kasance lafiya. Ni kai na na bi wannan hanya.

Kara karanta wannan

Allura ta tono garma: Tsohon hadimin Matawalle ya shirya yi masa fallasa gaban kotu

"Na yi tafiya daga Wurno–Isa–Shinkafi zuwa Gusau, hanyoyin da tsawon shekaru suka kasance wuraren da ba a iya bi. Kasuwannin shanu sun sake budewa, rayuwa ta fara dawowa daidai.
Sai dai an sake samun matsala ne bayan rashin hadin kai daga bangaren sojoji, inda rikici ya sake barkewa."

- Shiekh Ahmad Mahmud Gumi

Malamin ya ce yanzu da aka samu mai sulhu a Ma’aikatar Tsaro a matsayin karamin minista, hakan na nuna an saka shi a inda ya dace.

Har ila yau, Sheikh Gumi ya yi fatan nasara ga gwamnatin tarayya kan dabarun tsaro da ta kawo a yaki da ta'addanci.

Ya kara da cewa:

"Ina yi wa sabon sauyin dabarun gwamnatin tarayya wajen magance matsalar tsaro fatan samun cikakkiyar nasara, tare da yi wa dukkan ’yan Najeriya fatan hadin kai, zaman lafiya da cigaba. Amin."

'Yan bindiga: Sheikh Gumi ya magantu kan sulhu

Mun ba ku labarin cewa Sheikh Ahmad Gumi ya ce babu wata koyarwar addini ko tsarin tsaro na duniya da ke haramta tattaunawa da ’yan bindiga.

Malamin ya ce manyan ƙasashen duniya suna irin wannan tattaunawa, inda ya yi misali da tattaunawar Amurka da Dalai Lama.

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: Matawalle ya tafi kotu, ya saka sunan malamin Musulunci

Gumi ya kuma bayyana dalilin da ya sanya ya daina ganawa da 'yan bindiga tuna a 2021 da kuma alakar hakan da gwamnati.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.