Hukumar NAHCON Ta Bude Shafin Daukar Ma'aikata a Najeriya, Ta Gindaya Sharudda

Hukumar NAHCON Ta Bude Shafin Daukar Ma'aikata a Najeriya, Ta Gindaya Sharudda

  • Hukumar NAHCON ta bude shafin daukar ma'aikatan lafiya da za su shiga tawagarta a lokacin aikin hajjin shekara mai zuwa, 2026
  • A wata sanarwa da ta fitar ranar Juma'a, NAHCON ta bayyana sharudda da ka'idojin da ake bukatar wadanda za su nemi aikin su cika
  • NAHCON ta ce an bude shafin da mutane za su cike neman aikin a daren Jiya Juma'a, kuma za a rufe shi a ranar Litinin, 15 ga watan Disamba, 2025

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar Kula da Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta bude shafin daukar ma'aikata a wani bangare na shirye-shiryen aikin hajjin 2026.

NAHCON, karkashin jagorancin Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan, ta bude shafin daukar ma'aikatan lafiya, wanda za su yi aiki a matsayin tawagar kula da lafiyar alhazan Najeriya (NMT).

Kara karanta wannan

EFCC ta fara shari'a da ministan Buhari a kotu kan tuhume tuhumen rashawa 8

Shugaban NAHCON.
Shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan Hoto: Prof. Abdullahi Saleh Pakistan
Source: Twitter

NAHCON za ta dauki malaman lafiya

Jaridar Leadership ta tattaro cewa a jiya Juma'a, 12 ga watan Disamba, 2025 aka bude shafin da mutane za su cike takardar neman aikin a shafin yanazar gizo na NAHCON.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Yaɗa Labarai da Wallafa Bayanai ta NAHCON, Fatima Sanda Usara ta rattaba wa hannu.

NAHCON ta gayyaci ma’aikatan lafiya da ke sha’awar wannan aiki da su shiga shafin intanet da ta tanada domin cike fam din neman aikin.

Hukumar ta nemi ma'aikatan lafiya musamman likitoci, masana harkokin magunguna, malaman jinya da ma’aikatan kula da lafiyar muhalli da su garzaya shafin domin cike fam.

Sharuddan da NAHCON ta gindaya

Sanarwar ta bayyana cewa za a bude shafin daukar ma'aikatan lafiya ne daga ƙarfe 11:00 na dare a ranar 12 ga Disamba zuwa ƙarfe 11:59 na dare ranar Litinin, 15 ga Disamba, 2025.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da muka sani game da daukar sababbin 'yan sanda 50,000 da za a yi a Najeriya

NAHCON ta kara da cewa duk wadanda za su nemi aikin dole su kasance ma'aikata, sannan kuma ba su yi irin wannan aiki ba a ayyukan Hajji uku na baya-bayan nan (2023, 2024 da 2025).

Domin ƙarin bayani da ka’idoji, an shawarci masu nema da su ziyarci shafin NAHCON a nahcon.gov.ng.

Hukumar NAHCON.
Mahajjatan Najeriya a lokacin da suke shiga jirgin sama zuwa kasar Saudiyya Hoto: @NAHCON
Source: Facebook

Hukumar ta ƙarfafa gwiwar duk wadanda suka cika ka'idojin da ake bukata da su duba dukkan sharudda da kyau tare da cike fom ɗin neman aikin yadda ya dace domin kauce wa matsalar da ka iya sa su rasa damar.

An kuma shawarci masu sha’awar aikin da su cike dukkan bayanan da ake bukata shafin yanar gizo a cikin lokacin da aka tanada.

NAHCON ta fitar da wasu tsare-tsare

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar NAHCON ta umarci kamfanonin jirage da su fara bai wa mahajjata tikitin tafiya tun kafin lokacin tashin su domin rage matsaloli.

Hukumar ta bayyana cewa daga Hajjin 2026, duk mahajjacin da ya rasa jirginsa zai fuskanci hukunci mai tsanani, domin tikitin tafiya zai kasance a hade da katin Nusuk.

NAHCON ta ce bayan fitowar biza, babu wani mahajjaci da zai sake canza rukuni. Rukunin zai kasance na mutum 45, kuma za su tafi tare.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262