Lamari Ya Munana: An Hallaka Matashi bayan Zargin Daɓawa Mahaifiyarsa Wuƙa a Niger

Lamari Ya Munana: An Hallaka Matashi bayan Zargin Daɓawa Mahaifiyarsa Wuƙa a Niger

  • Wani matashi ya rasa ransa bayan jama’a sun yi masa duka a Suleja, jihar Niger, kan zargin kashe mahaifiyarsa
  • Rahotanni sun ce rikicin ya barke ne kan rabon gadon mahaifinsu, inda mahaifiyar ta rike rabon saboda tsoron zai lalata shi
  • Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da lamarin, ta ce ya kashe mahaifiyar da wuka, yayin da ake ci gaba da farautar mutanen da suka yi kisan gilla

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Suleja, Niger - Wani matashi mai shekaru 25 mai suna Adamu Abdullahi ya mutu bayan jama’a sun yi masa duka a garin Suleja a jihar Niger.

Lamarin ya faru ne a hedikwatar karamar hukumar Suleja ta jihar bayan zarginsa da kisan mahaifiyarsa kan gado a yau Asabar 13 ga watan Disambar 2025.

Kara karanta wannan

Sababbin jakadu: Mutane 5 da Tinubu ya nada da suka fuskanci manyan zarge zarge

An hallaka matashi bayan kisan mahaifiyarsa a Niger
Taswirar jihar Niger da ke makwabtaka da birnin Abuja. Hoto: Legit.
Source: Original

'Dalilin matashin na kashe mahaifiyarsa'

Daily Trust ta ce ana zargin Adamu ya daba wa mahaifiyarsa, Hauwa Sanusi mai shekaru 45, wuka har lahira, sakamakon sabani kan rabon gadon mahaifinsa da ya rasu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun ce mahaifiyar ce ke rike da rabon gadon ɗanta, tana mai cewa ta yi hakan ne don hana shi lalata kadarorin.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa matashin ya dawo Suleja ne bayan dogon lokaci bai zauna a garin ba, inda ba a san inda yake ba.

Yaushe lamarin ya faru a jihar Niger?

A safiyar Asabar 13 ga watan Disambar 2025, ana zargin ya kai wa mahaifiyarsa hari da wuka, inda ya daba mata wuka sau da dama a gidansu.

Kukan mahaifiyar ne ya ja hankalin makwabta, wadanda suka zo suka same ta kwance cikin jini a yayin da matashin ke kokarin tserewa.

Jama’an yankin sun kama shi, suka fara yi masa duka saboda fushin abin da ya aikata, kafin daga bisani ‘yan sanda su iso wurin.

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: Matawalle ya tafi kotu, ya saka sunan malamin Musulunci

Yan sanda sun fara bincike da matashi ya kashe mahaifiyarsa
Sufeta-janar na yan sanda, Kayode Egbetokun. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

Abin da yan sandan Niger suka ce

Wani mazaunin garin, Ibrahim Hassan, ya ce mahaifiyar ita ce uwarsa da ta haife shi, kuma rikicin gadon ne ya jawo hatsaniyar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Niger, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Ya ce an samu rahoto da misalin karfe 1:30 na dare cewa wani matashi ya kashe mahaifiyarsa da wuka yayin wata rashin fahimta.

A cewarsa, bayan faruwar kisan, wasu mutane sun kai wa wanda ake zargi hari, inda suka yi masa kisan gilla kafin ‘yan sanda su shiga tsakani.

'Yan sanda sun kwashe gawarwakin biyu, sun kuma kwato wukar da aka yi amfani da ita, yayin da ake kokarin cafke ‘yan daba da suka aikata kisan.

Matashi ya buge mahaifiyarsa da sanda

Mun ba ku labarin cewa yan sanda sun kama Mathias Amunde bisa zargin kashe mahaifiyarsa da sanda a karamar hukumar Obudu, jihar Cross River.

Kara karanta wannan

Abin da Kiristoci suka fadawa dan majalisar Amurka da ya ziyarce su a Najeriya

An ce wanda ake zargin tare da wani abokinsa sun yi amfani da sanda wajen kashe tsohuwar, sannan suka jefa gawarta cikin rijiya.

’Yan sanda sun tabbatar da cewa za a ci gaba da bincike domin gano gaskiyar lamarin da kuma daukar matakin da ya dace a bisa doka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.