Farashin Fetur Zai Dawo Kasa da N800 bayan Matatar Dangote Ta Tausaya Wa 'Yan Najeriya

Farashin Fetur Zai Dawo Kasa da N800 bayan Matatar Dangote Ta Tausaya Wa 'Yan Najeriya

  • Farashin man fetur zai kara araha a Najeriya bayan matatar Dangote ta rage N129 kan kowace lita a watan Disamba, 2025
  • Rahoto ya nuna rumbunan ajiya na 'yan kasuwa sun bi sahun matatar Dangote, sun fara sauke farashin feturin da suke sayarwa
  • Duk da har yanzun saukin bai gama isa gidajen mai ba, amma ana hasashen wannan ragi zai kawo sauki ga 'yan Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ana hassshen cewa 'yan Najeriya za su samu sauki sosai a farashin man fetur bayan rangwamen da matatar man Dangote ta yi a cikin makon da ya shige.

Matatar hamshakin attajirin ta sauke farashin kowace litar fetur daga N828 zuwa N699 domin saukakawa yan kasa musamman a lokacin bukukuwan kirismeti da farkon shekara.

Kara karanta wannan

"A bayyane yake": An hango abin da Tinubu zai yi wa Shettima a zaben 2027

Fetur.
Ana zuba man fetur a cikin wata mota a gidan mai Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Matatar Dangote ta rage N129 a litar fetur

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa rangwamen N129 da matatar Dangote ta yi, ya sa farashin litar fetur ya sauko zuwa kasa da 800 a karon farko bayan tsawon lokaci.

Wannan rangwame ya nuna cewa an samu sauki da kashi 15.58 cikin 100 na farashin feturin matatar Dangote.

Rahoto ya nuna cewa wannan sabon farashi ya fara aiki ne daga ranar 11 ga watan Disamba, 2025 a rumbunan ajiya, wurin da matatar Dangote ke sayar wa 'yan kasuwa da fetur.

Mai magana da yawun matatar Dangote, Tony Chiejina, ya tabbatar da rage farashin lokacin da aka tuntube shi.

Majiyoyi sun ce an yi wannan ragi ne domin rage kuɗin sufuri gabanin bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara, lokacin da miliyoyin ’yan Najeriya ke yin tafiye-tafiye domin haɗuwa da iyalansu.

Kara karanta wannan

Matatar Dangote ta yi babban rangwame, ta canza farashin litar fetur a Najeriya

Wannan ci gaba ya zo ne kwanaki biyar kacal bayan shugaban matatar, Aliko Dangote, ya sake jaddada ƙudurinsa na ci gaba da sayar da fetur a farashi mai sauƙi da rahusa.

'Yan kasuwa sun fara sauke farashinsu

Bayan sanar da sabon farashin Dangote, masu sa ido kan kasuwa sun bayyana cewa wasu rumbunan ajiyar man fetur masu zaman kansu sun bi sahu wajen rage farashinsu.

Ma’ajiyar Sigmund ta rage farashi da ₦4 zuwa ₦824; Bulk Strategic ta yi ragin ₦3; yayin da TechnoOil ta yi ɗaya daga cikin manyan ragi na ₦15.

Sauran wuraren ajiya kamar A.A. Rano, NIPCO da Aiteo suma sun rage farashinsu, kamar yadda Vanguard ta kawo.

Aliko Dangote.
Shugaban rukunin kamfaninin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote Hoto: @Dangotegroup
Source: Getty Images

Sai dai bincike ya nuna cewa har yanzu wannan ragi bai bayyana a gidajen sayar da mai ba.

A halin yanzu, ana sayar da litar fetur tsakanin ₦890 da ₦910 a wasu jihohi, yayin da a Arewa ake sayar da ita sama da ₦950 a kowace lita.

Dangote ya ce layin neman mai ya kare

A wani rahoton, kun ji cewa hamshakin ɗan kasuwa kuma shugaban matatar Dangote , Aliko Dangote ya bayyana cewa zamanin dogayen layukan neman mai ya ƙare har abada a Najeriya.

Kara karanta wannan

Majalisa ta shiga tsakani, da yiwuwar a yafewa mutane bashin COVID 19

Dangote ya faɗi haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Fadar Aso Rock bayan ganawa da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Attajirin ya bayyana cewa a karo na farko, matatar feturin da ya gina tana samar da man zuwa Turai da Amurka, yana mai cewa Najeriya na samun wadataccen mai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262