Shugaba Tinubu Ya Karbi Bakuncin Gwamnoni 3, Ya Gana da Su Daya bayan Daya
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin gwamnonin jihohin Benuwai, Kaduna da Kuros Riba a fadarsa da ke Abuja
- Rahoto ya nuna cewa gwamnonin sun isa fadar shugaban kasa a lokuta daban-daban kuma kowane ya gana da Bola Tinubu a sirrince
- Wasu majiyoyi sun bayyana cewa gwamnonin sun tattauna kan matsalolin tsaro da tattalin arziki da shugaban kasa, amma babu sanarwa a hukumance
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnonin jihohi uku a Najeriya sun ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja.
Gwamnonin da aka gani sun isa fadar shugaban kasa da yammacin jiya Juma'a sun hada da Gwamna Uba Sani na Kaduna, Gwamna Hyacinth Alia na Benuwai da Gwamna Bassey Otu na Kuros Riba.

Source: Twitter
Tinubu ya yi ganawar sirri da gwamnoni 3
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya gudanar da ganawar sirri daban-daban da gwamnonin jihohin Kaduna, Benuwau da Kuros Riba a fadar gwamnati da ke Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar rahoton, Shugaba Tinubu ya gana da kowane gwamna shi kadai kuma a lokaci daban-daban, a jiya Juma'a, 12 ga watan Disamba, 2025.
Gwamnonin sun isa Fadar Shugaban Ƙasa a lokuta daban-daban, inda kowannen su ya shiga ganawa ta musamman da Shugaba Tinubu.
Wannan ganawa na zuwa ne yayin da ake fuskantar tabarbarewar tsaro a sassan kasar nan, kuma galibin jihohin da gwamnonin ke shugabanci na fama da kalubale na tsaro.
Ba a fitar da wani cikakken bayani a hukumance daga fadar shugaban ƙasa game da abin da gwamnonin suka tattauna da shugaban kasa ba.
Abubuwan da ake zaton sun tattauna
Sai dai majiyoyi da ke da masaniya kan ganawar sun ce an mayar da hankali ne kan matsalolin tsaro da sauran manyan batutuwan mulki da kalubale da ke addabar jihohin uku.
Daga cikin abubuwan da majiyoyin suka ce an tattaunawa akwai rikice-rikice tsakanin al’umma, ayyukan ’yan bindiga, da matsin tattalin arziki da ke ƙaruwa.
Bayan kammala ganawar, gwamnonin ba su tsaya sun yi magana da ’yan jarida ba, sun dai yi gajeriyar gaisuwa kawai da manema labarai kafin su shiga motocinsu su bar fadar shugaban kasa.

Source: Twitter
Har kawo yanzu da muke hada wannan rahoto, babu wata sanarwa daga fadar shugaban kasa ko daga bangaren gwamnonin Kaduna, Benuwai da Kuros Riba kan wannan ganawa da suka yi.
Bola Tinubu ya gana da gwamnonin APC 6
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnonin jam'iyyar APC shida a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja a ranar Litinin.
Rahoton ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya shiga ganawar sirri da gwamnonin bayan isarsu fadarsa, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a bayan fage.
An kuma rahoto cewa Mai Girma Tinubu da gwamnonin APC shida ba su shafe awa daya a wannan taron ba, kuma ba a yi wa 'yan jaridar fadar shugaban kasa wani bayani ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

