‘Duk da ba Jam’iyya Daya Muke ba’: Tinubu Ya Yaba Jajircewar Wike a Gwamnatinsa
- Shugaba Bola Tinubu ya yi magana game da jajircewar ministan Abuja, Nyesom Wike a gwamnatinsa tun bayan hawa mulki
- Tinubu ya taya Ministan murnar cika shekaru 58, yana yabonsa kan jajircewa da hidimar jama’a wanda ba za a manta ba
- Shugaban ya bayyana Wike a matsayin jajirtaccen jagora mai kafa tarihi, yana jaddada rawar da yake takawa wajen sauya fasalin Abuja
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya kwarara yabo ga ministan birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike game da jajircewarsa a gwamnati.
Tinubu ya taya Minista Nyesom Wike, murnar cika shekaru 58 a duniya wanda ya yi daidai da ranar 13 ga watan Disambar 2025 da muke ciki.

Source: Twitter
Tinubu ya yabawa kokarin Wike a Abuja
Shugaban ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yada labarai, Dada Olusegun ya wallafa a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sakon, Shugaba Tinubu ya yaba wa Wike wanda tsohon gwamnan Jihar Rivers, yana cewa rayuwarsa cike da manufa, jarumtaka da sadaukarwa wajen hidimar jama’a ba tare da wasa ba.
Ya bayyana Wike a matsayin shugaba mai iya shawo kan ƙalubale tare da samar da sakamako mai ma’ana a duk inda aka ba shi aiki.
Ya ce ministan ya tabbatar da jajircewarsa a kowane bangare wanda bai tsaya iya jihar Rivers ba kadai lokacin da yake gwamna.

Source: Facebook
Tinubu ya fadi gudunmawar Wike a gwamnati
Shugaban ya jaddada gudunmawar da ministan ke bayarwa wajen canza fasalin Babban Birnin Tarayya, musamman ta hanyar tsauraran ayyukan sabunta hanyoyi da manyan gine-gine.
Tinubu ya ambaci yadda Wike ya karya tsaikon shekaru 14 da aka yi ana ta fama da gina hanyar Apo–Karshi, wanda a cewarsa babbar nasara ce.
Ya kuma yabawa Wike bisa jajircewarsa, dabi'ar aiki da kuma ƙwazonsa wajen cimma inganci a dukkan ayyukan da aka dora masa ba tare da wata matsaa ba.
Tinubu ya ce Wike na daga cikin fitattun mambobin majalisar ministocinsa, yana tabbatar da cewa laƙabin sa na “Mr Project” bai tsaya ga Jihar Rivers kaɗai ba.
Shugaban ya kara da cewa Wike na daga cikin ginshiƙan Ajandar 'Renewed Hope', duk da kasancewarsa ɗan wata jam’iyya daban amma ya ba da gudunmawa fiye da misali.
A ƙarshe, Tinubu ya yi masa fatan samun lafiya, ƙarin ƙarfi da manyan nasarori yayin da yake ci gaba da yi wa ƙasa hidima a matsayin Ministan Abuja.
Wike ya musanta matsala tsakaninsa da Tinubu
A baya, kun ji cewa an yada wasu rahotanni masu nuna cewa sabani ya shiga tsakanin ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike da Shugaba Bola Tinubu
Nyesom Wike ya fito ya yi magana kan jita-jitar da ke cewa dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da shugaban kasan.
Ministan ya bayyana cewa abin da ake yadawa ko kadan babu gaskiya a cikinsa, inda ya yi bayani kan dalilin rashin ganinsa wajen taron majalisar koli ta kasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

