Kotu Ta Shirya, Za Ta Zartar da Hukuncin a kan Abba Kyari da 'Yan Uwansa

Kotu Ta Shirya, Za Ta Zartar da Hukuncin a kan Abba Kyari da 'Yan Uwansa

  • Kotun tarayya ta sa rana domin yanke hukunci a kan shari’ar rashin bayyana kadarori da gwamanti ke yi da Abba Kyari da ’yan’uwansa
  • Hukumar NDLEA na zargin Abba Kyari da ɓoye kadarori da kudi sama da N207m da €17,598 a asusun banki daban-daban
  • Sai dai Abba Kyari ya musanta zarge-zargen NDLEA, inda ya bayyana cewa wasu daga cikin kadarorin na mahainfsu ne da ya rasu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 26 ga Fabrairu, 2026 domin yanke hukunci a shari’ar rashin bayyana kadarori da hukumar NDLEA ta shigar kan dakataccen Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda, Abba Kyari.

Kara karanta wannan

EFCC ta fara shari'a da ministan Buhari a kotu kan tuhume tuhumen rashawa 8

Hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi ta NDLEA na tuhumar Kyari, tsohon shugaban sashen IRT na rundunar yan sanda, tare da kannesa biyu, Mohammed Kyari da Ali Kyari.

Kotu za ta yanke hukunci a kan shari'ar NDLEA da Kyari
DCP Abba Kyari, dakataccen jami'in 'dan sandan Najeriya Hoto: Abba Kyari
Source: Facebook

Premium Times ta wallafa cewa lauyoyin dukkannin bangarori sun gabatar da hujjojin karshe, alkalin kotun, Mai shari’a James Omotosho, ya sanya ranar yanke hukunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana ci gaba da shari'a da Abba Kyari

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa NDLEA ta gabatar da tuhume-tuhume 23, tana zargin cewa Kyari da ’yan’uwansa ba su bayyana dukkan kadarorinsu ba kamar yadda doka ta tanada.

NDLEA ta ce ta gano kadarori 14 da suka hada da shaguna, gidajen zama, fili na wasan polo, filaye da gonaki da ake dangantawa da Kyari.

Haka kuma, an zarge shi da gaza bayyana wasu kadarori da ya mallaka a wurare daban-daban na Babban Birnin Tarayya (Abuja) da Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: Matawalle ya tafi kotu, ya saka sunan malamin Musulunci

Hukumar ta kuma ce an gano kudi sama da N207m da €17,598 a asusun banki daban-daban a GTBank, UBA da Sterling Bank.

Zarge-zargen NDLEA a kan Kyari

A cewar NDLEA, wadanda ake tuhuma sun yi kokarin ɓoye mallakar kadarori da kuma juya kudi ta hanyoyi daban-daban.

EFCC na shari'a da DCP Abba Kyari
Shugaban hukumar NDLEA na kasa, Buba Marwa (D) Hoto: NDLEA
Source: Facebook

Hukumar ta ce laifuffukan suna da hukunci a karkashin Sashe na 35 (3) (a) na Dokar NDLEA da Sashe na 15 (3) (a) na Dokar Hana Safarar Kudi ta 2011.

Dukkan wadanda ake tuhuma sun musanta zarge-zargen yayin da hukumar EFCC ta kira shaidu 10 tare da gabatar da akalla hujjoji 20.

Kyari dai ya nemi kotu ta ce babu shari’a a kansa a wannan batu, yana cewa ba a gabatar da hujjar cewa shi ne ya mallaki kadarorin ba.

Kara karanta wannan

Ta leko ta koma: Yadda Abdullahi Ramat ya rasa kujerar shugabancin hukumar NERC

Sai dai a ranar 28 ga Oktoba, alkalin ya yi watsi da bukatar, yana mai cewa an kafa hujjar farko, don haka dole su kare kansu.

Kyari ya fara kare kansa a ranar 4 ga Nuwamba, yana jaddada cewa ya bayyana kadarorinsa da na matarsa bisa doka, tare da musanta mallakar wasu kadarorin.

Ya ce wasu kadarorin na mahaifinsa ne marigayi wanda ya haifi ’ya’ya kusan 30. Ya kuma musanta mallakar filin wasan polo a Borno.

An roki Tinubu alfarma game da Kyari

A baya, mun wallafa cewa hukumar kare hakkin dan adam ta duniya (IHRC), reshen Najeriya, ta tura wata bukata ta musamman ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu dangane DCP Abba Kyari.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya za ta dauki 'yan sanda 50,000, an fitar da sharudan aikin

Hukumar ta bukaci a yi wata tattaunawa ta kasa domin duba yiwuwar yi wa Abba Kyari afuwa ta musamman, tana mai jaddada cewa kiran nata ba don tsoma baki a shari’ar da ake yi ba ne.

Wannan bukata na kunshe ne cikin wata sanarwa da Jakada (Dr.) Duru Hezekiah, shugaban IHRC a Najeriya, ya fitar a Abuja, inda ya ce suna fatan afuwan zai amfani kasa baki daya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng