"Sojoji ba Za Su Iya ba": Ciyaman a Zamfara Ya Samo Hanyar Kawo Karshen 'Yan Bindiga
- Jihar Zamfara na ci gaba da fuskantar matsalar rashin tsaro sakamakon hare-haren da 'yan bindiga suke kai wa kan bayin Allah
- Shugaban karamar hukumar Bukkuyum ya ba gwamnatin tarayya mafita kan hanyar shawo kan matsalar da ta dade tana cin yankin
- Abubakar Umar Faru ya bayyana cewa ya gayawa sojoji wuraren da 'yan bindiga ke boye a cikin daji amma sun kasa tunkarar su
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Shugaban karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara, Abubakar Umar Faru, ya ba gwamnatin tarayya shawara kan matsalar rashin tsaro.
Abubakar Umar Faru ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ba jami’an tsaro makamai na zamani domin su iya kaddamar da cikakken farmaki kan ‘yan bindigan da ke fakewa a Dajin Gando.

Source: Twitter
Shugaban karamar hukumar ta Bukkuyum ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a wata hira da DCL Hausa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An sanar da sojoji wuraren buyar 'yan bindiga
Abubakar Faru ya ce tun tuni ya bai wa hukumomin tsaro cikakkun bayanan wuraren ɓuyar ‘yan bindiga a cikin dajin.
Sai dai, ya nuna damuwa cewa jami’an ba su da karfin makaman da za su iya tunkarar 'yan bindigan yadda ya kamata.
“Ni da kaina na ba su dukkan bayanan wurare da za su iya kawar da wadannan mutane gaba ɗaya, amma ba su da makaman da za su kai farmaki zuwa gare su."
- Abubakar Umar Faru
Abubakar Faru ya bayyana Dajin Gando a matsayin sabuwar cibiyar ‘yan bindiga, yana mai cewa matsalar ta ƙara tsananta ne bayan wasu gungun ‘yan bindiga da suka kulla yarjejeniyar zaman lafiya a wasu sassan jihar Katsina da Birnin Gwari a Jihar Kaduna sun koma Zamfara.
“Yanzu Dajin Gando ya zama babbar mafaka. Wasu daga cikin ‘yan bindigan da suka yi sulhu a wasu wurare sun shigo Zamfara sun kafa sansani a nan."
- Abubakar Umar Faru
Ya za a kawo karshen 'yan bindiga?
Duk da yabawa da ya yi wa kokarin jami’an tsaro da aka tura yankin, shugaban karamar hukumar ya jaddada cewa ba za a kawo ƙarshen ‘yan bindiga ba sai an yake su kai tsaye cikin daji.
“Jami’an tsaron da muke da su suna iya bakin kokarinsu wajen kare rayuka da dukiyoyi, amma idan ana son a kawo karshen wannan ta’addanci, dole ne a kai farmaki cikin dajin inda ‘yan bindigan suke."
- Abubakar Umar Faru

Source: Original
Da aka tambaye shi wa yake ganin ya gaza kawo karshen ‘yan bindiga a jihar, Abubakar Faru ya nuna yatsa kan karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle, yana mai cewa bai cika tsammanin jama’a ba.
“Matawalle ɗan jihar Zamfara ne, kuma a matsayinsa na karamin Ministan tsaro, yana da damar da za ta sa a kawo karshen ‘yan bindiga a nan. Ban san abin da ke faruwa ba, amma ya kasa yin hakan."
- Abubakar Umar Faru
'Yan bindiga sun kashe mataimakin ciyaman
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'ya n bindiga dauke da makamai sun yi aika-aika a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma.
Miyagun 'yan bindigan sun kashe mataimakin shugaban karamar hukumar Bukuyum ta jihar Zamfara bayan sun yi awon gaba da shi.
Mutanen marasa imani sun yi ajalin Hon. Mu’azu Muhammad Gwashi, duk da cewa an biya su kudin fansa har Naira miliyan 15.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


