An Tsorata Bello Turji Ya Mika Wuya bayan Sojoji Sun Kashe Mataimakinsa
- Kungiyar matan Arewa maso Yamma ta bukaci dan ta'adda mai garkuwa da mutane, Bello Turji ya ajiye makamai
- Matan sun yaba wa rundunar sojin Najeriya kan hallaka mataimakin Turji, Kallamu Buzu da wasu ‘yan bindiga a Sabon Birni
- Gwamnatin Sokoto ta jinjinawa sojoji bisa ƙwarewar da suka nuna wajen kare rayuka da dukiyoyi a farmakin da suka kai
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Wata ƙungiya mai zaman kanta ta mata a Arewa maso Yamma ta yi kira ga shugaban ‘yan bindiga Bello Turji da ya mika wuya tare da ajiye makamai.
Kungiyar ta ce matakin ya dace da tsarin da sojojin Najeriya ke bi na haɗa dabarun sulhu da na tsaro domin dawo da doka da oda a yankunan da rikici ya shafa.

Kara karanta wannan
Halin da Bello Turji ke ciki bayan hallaka na kusa da shi a Sokoto, ya zargi wasu mayaka

Source: UGC
Blueprint ta rahoto cewa matan sun yi wannan kiran ne bayan sun gudanar da addu’o’i a Abuja domin yankin Arewa maso Yamma, Najeriya baki ɗaya da kuma rundunar sojin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kira ga Bello Turji ya mika wuya
Jami’ar hulda da jama’a ta ƙungiyar, Salamatu Bello, ta bayyana cewa mata da al’umma sun gaji da tashin hankali da rashin tsaro da ke addabar yankin.
Ta ce:
“Ba za mu iya ci gaba da zama a haka ba. Mun taru domin roƙon Allah Ya kawo mana zaman lafiya a yankinmu da ƙasar nan baki ɗaya.”
Salamatu Bello ta ƙara da cewa mata a matsayin iyaye suna ganin lokaci ya yi da Bello Turji zai rungumi zaman lafiya kafin abin ya ƙara tsananta.
Ta kara da cewa:
“A matsayimmu na iyaye, muna kira ga Bello Turji ya mika wuya kafin lokaci ya kure masa, domin rayukan jama’a su tsira.”
An yabi sojoji kan kashe aminin Turji
Kungiyar ta kuma yaba wa rundunar sojin Najeriya kan nasarar da ta samu wajen hallaka babban mataimakin Turji, Kallamu Buzu, a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.
Rahotanni sun nuna cewa dakarun runduna ta 8 na rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadarin Daji ne suka kashe Buzu da wasu ‘yan bindiga.
Daily Nigerian ta wallafa cewa Salamatu Bello ta ce matan yankin na farin ciki da yadda sojoji ke rage karfin ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda, tana cewa hakan na kara wa jama’a kwarin gwiwa.
Tasirin kisan Buzu da martanin Turji
Rahotanni sun nuna cewa kisan Kallamu Buzu ya girgiza Bello Turji matuka, inda ake cewa ya yi barazanar daukar fansa.
An ce Turji ya zargi wani daga cikin mataimakansa kan kuskuren da ya janyo mutuwar Buzu bayan wani yunkuri da bai yi nasara ba kan ‘yan kasuwa a Sabon Birni.

Source: Facebook
Kungiyar matan ta ce irin wannan martani ba zai kawo mafita ba, face ƙara jawo asarar rayuka da durkusar da al’umma.
A nasa bangaren, gwamnatin jihar Sokoto ta yaba wa jarumta da ƙwarewar jami’an tsaro a farmakin da suka kai kan mayakan Turji.
An sace shanu 168 a jihar Filato
A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai farmaki kan wasu makiyaya a jihar Filato.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar Filato ya ce lamarin ya faru ne a wasu kananan hukumomi biyu na jihar.
Kungiyar ta sanar da cewa ta sanar da jami'an tsaro domin a gaggauta kamo wadanda suka sace mata shanu 168.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

