Nentawe: Shugaban Jam'iyyar APC Na Kasa Ya Samu Sarautar Gargajiya

Nentawe: Shugaban Jam'iyyar APC Na Kasa Ya Samu Sarautar Gargajiya

  • Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, zai samu sarautar gargagiya a jihar Benue
  • Mai martaba Tor Tiv, Farfesa James Iorzua Ayatse, zai nada rawani ga Farfesa Nentawe Yilwatda da matarsa a ranar Asabar
  • Za a nada Nentawe sarautar ne saboda jajircewarsa wajen samar da hadin kai da fafutukar kawo gyare-gyare masu ma'ana

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda zai samu sarautar gargajiya.

Farfesa Nentawe Yilwatda zai samu babbar sarautar gargajiya a masarautar Tiv mai daraja, wato Zegbar-u-Tiv tare da matarsa, Dr. Martina Yilwatda.

Farfesa Nentawe ya samu sarauta
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Hoto: Prof Nentawe Yilwatda
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai ba da shawara na musamman ga Yilwatda, Abimbola Tooki, ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe za a nada Nentawe kan sarauta?

Sanarwar ta bayyana cewa Tor Tiv, mai martaba Farfesa James Iorzua Ayatse, ne zai yi nadin sarautar, wadda za ta samu halartar majalisar sarakunan gargajiya ta Tiv, a yau Asabar, a filin wasa na J.S. Tarka da ke Gboko, jihar Benue.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya nada mace ta farko a matsayin shugabar jami'ar gwamnati a Kano

A cewar Abimbola Tooki, an bada wannan sarauta ne domin girmama gagarumar gudummawar da ma’auratan suka bayar wajen haɗin kan kasa, zaman lafiya a tsakanin al’umma, da ci gaban al’umma, jaridar The Guardian ta kawo labarin.

“Ga al’ummar jihohin Plateau da Benue, wannan sarauta ba wai girmamawa ta al’ada kaɗai ba ce, tana wakiltar kakkarfar alaka mai ɗorewa tsakanin al’ummomi biyu ‘yan uwa, da ke da alaka ta kyawawan ɗabi’u, girmama juna, da dogon tarihin mu’amalar zamantakewa da al’adu."
“Kyakkyawar alakar da Farfesa Nentawe ke da ita da al’ummar Tiv, tare da sunan da ya yi wajen haɗa kai, fafutukar kawo gyare-gyare, da inganta zaman lafiya, sun sa ya samu karɓuwa sosai a faɗin yankin Middle Belt.”
"Hakazalika ana girmama Dr. Martina Nentawe Yilwatda saboda irin tasirin aikinta a fannin ilimi, ƙarfafa mata, da shirye-shiryen kiwon lafiya."
"Haka kuma ana yaba mata bisa jajircewarta wajen ayyukan jin ƙai da goyon bayan iyalai da rukunin al’umma masu rauni.”
“Iyalan Yilwatda, tare da abokai, ‘yan siyasa, shugabannin gargajiya, da masu fatan alheri daga sassa daban-daban na Najeriya da ma ƙasashen waje, suna gayyatar jama’a da hannu bibbiyu domin halartar wannan muhimmin biki."

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Sanata Ahmed Lawan ya yi babban hasashe kan makomar Tinubu a Arewa

"Ana sa ran bikin zai kasance cike da al’adun Tiv, haɗin kai, da girmamawa ga shugabanci nagari mai jan hankalin jama’a.”

- Abimbola Tooki

Farfesa Nentawe Yilwatda ya samu sarautar gargajiya a Benue
Shugaban jam'iyyar APC, Farfesa Nentawe Yilwatda na jawabi Hoto: Prof Nentawe Yilwatda
Source: Twitter

Hasashe shugaban APC kan zaben 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya yi hasashe kan zaben shekarar 2027.

Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi hasashen cewa jam’iyyar za ta samu cikakkiyar nasara a zaben 2027 da ake tunkara.

Hakazalika, shugaban na APC na kasa ya bayyana cewa karɓuwar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke samu a faɗin kasa na kara karuwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng