Abba Ya Yi Ta Maza, Ya Murkushe Yunkurin Ganduje na Kafa Sabuwar Hisbah a Kano
- Gwamnatin jihar Kano ta fitar da umarnin haramta kafa kungiyar ‘Independent Hisbah Fisabilillahi’ bisa zargin aikata ayyuka ba bisa ka’ida ba
- Hukumomin tsaro sun samu umarnin bincike da dakile masu daukar matasa, horaswa ko shirya ayyuka da sunan kungiyar Hisbar a fadin jihar
- Gwamnati ta gargadi jama’a da su kaurace wa kungiyar, tana mai cewa duk wanda ya shiga ko ya mara mata baya zai fuskanci hukunci bisa doka
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Gwamnatin jihar Kano ta dauki matakin haramta ‘Independent Hisbah Fisabilillahi’ da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ya ce zai kafa.
Wannan umarni ya biyo bayan rahotannin da suka nuna ana cigaba da daukar matasa, horaswa da shirya su domin gudanar da ayyuka ba tare da amincewar hukuma ba, lamarin da gwamnati ta ce ya na barazana ga zaman lafiya.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ne ya sanya wa umarnin hannu a ranar 8, Disamba, 2025 kuma ya fara aiki nan take, tare da umartar hukumomin tsaro su dauki matakin gaggawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin haramta Hisbar Ganduje a jihar Kano
Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce gwamnatin ta gano cewa kungiyar na gudanar da ayyuka ba bisa ka’ida ba, tare da karya dokar Hukumar Hisbah ta jihar Kano.
Ya bayyana cewa Hukumar Hisbah ta jihar Kano ce kadai hukuma da doka ta amince da ita wajen tsara wa, jagoranta da aiwatar da ayyukan Hisbah a fadin jihar.
A cewarsa, fitowar wata kungiya ta daban da ke ikirarin yin irin wadannan ayyuka na iya haddasa rudani da barazana ga zaman lafiya.
A cikin umarnin zartarwar, gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce:
“Ba zai halatta ga kowane mutum ko kungiya su dauki matasa, tara su, horas da su ko tura mutane domin gudanar da wata Hisbah ta dabam a jihar ba.”
'Hisbar Ganduje ta karya doka' - Abba Kabir Yusuf
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa kafa wata runduna ta daban da ke dauke da siffofi irin na Hisbah na iya rushe tsarin doka da oda, tare da raunana ikon hukuma da dokar da ta kafa Hukumar Hisbah.
Umarnin ya kuma ayyana dukkan ayyukan kungiyar a matsayin “haramtattu, ba bisa doka ba kuma babu inganci,” yana mai gargadin cewa duk wanda ya kwaikwayi kayan Hisbah, alamomi ko ikonta zai fuskanci hukunci.

Source: Facebook
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci rundunar ‘yan sanda, hukumar DSS, NSCDC da sauran hukumomin tsaro da su binciki shugabanni da masu daukar nauyin kungiyar, tare da dakatar da duk wani horo ko daukar mutane da ake yi.
Hisbah: Gwamna Abba ya gargadi jama'an Kano
BBC Hausa ta rahoto cewa gwamnatin jihar ta sanar da jama’a cewa shiga, tallafa wa ko alakanta kai da kungiyar da aka haramta karya doka ne.
Ta bukaci mutanen da aka riga aka dauka cikin kungiyar da su fice nan take, su kuma kai rahoto ga ofishin tsaro mafi kusa, ofishin Hisbah ko karamar hukuma.
Umarnin ya kuma tanadi hukunci ga duk wanda ya saba, ciki har da gurfanarwa kan yin haramtacce taro, sojan gona da kafa rundunar tsaro ba tare da izini ba.
An yi karar Ganduje wajen Shugaba Tinubu
A wani labarin, mun kawo muku cewa kungiyar lauyoyin Kano ta mika wa shugaba Bola Tinubu korafi game da Abdullahi Ganduje.
Lauyoyin sun mika korafi ne a kan shirin kafa sabuwar Hisbah da tsohon gwamnan ya ce zai kirkiro a jihar Kano a kwanan nan.
Cikin wandanda kungiyar ta bukaci su shiga lamarin domin takawa Abdullahi Ganduje burki akwai NSA, Malam Nuhu Ribadu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


