Gwamna Ahmad Aliyu Zai Kashe Naira Biliyan 8.4 a Sake Gina Kasuwa

Gwamna Ahmad Aliyu Zai Kashe Naira Biliyan 8.4 a Sake Gina Kasuwa

  • Gwamnatin jihar Sokoto ta amince da kashe sama da Naira biliyan 8.4 domin sake gina babbar kasuwar Sokoto da gobara ta lalata
  • An yanke shawarar ne a zaman majalisar zartarwa karo na 16, inda aka amince ‘yan kasuwa 38 ‘yan asalin jihar za su aiwatar da aikin
  • Kwamishinan gidaje ya ce Gwamna Ahmed Aliyu ya kuduri aniyar cika alkawarin da ya daukana dawo da martabar kasuwar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Gwamnatin jihar Sokoto ta amince da kashe Naira biliyan 8.4 domin sake ginawa da kuma inganta babbar kasuwar Sokoto, wacce ta lalace sakamakon gobara a shekarun baya.

An yanke wannan shawara ne a ranar Alhamis yayin zaman majalisar zartarwa ta Sokoto karo na 16 da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar.

Gwamna Ahmad Aliyu ya amince ya sake gina babbar kasuwar Sokoto kan N8.4bn
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu yayin da ya jagoranci taron majalisar zartarwa (SEC). Hoto: @Ahmedaliyuskt
Source: Facebook

Gwamnan Sokoto zai gina kasuwa kan N8.4bn

Kara karanta wannan

Abba ya yi ta maza, ya murkushe yunkurin Ganduje na kafa sabuwar Hisbah a Kano

Bayan kammala taron, kwamishinan filaye da didaje, Nasiru Dantsoho, ya yi wa manema labarai karin haske kan muhimman shawarwarin da aka dauka, in ji rahoton The Guardian.

Nasiru Dantsoho ya bayyana cewa majalisar ta amince da aikin sake gina kasuwar kan kudin da ya kai Naira 8,499,855,347, inda ya ce gwamnati za ta dauki nauyin aikin gaba daya.

Ya kara da cewa ‘yan kwangila 38 daga cikin ‘yan kasuwar Sokoto ne za su aiwatar da aikin, domin tallafa wa tattalin arzikin cikin gida.

A cewarsa:

“Gwamnatin jihar za ta dauki nauyin aikin gaba daya domin tabbatar da kasuwar ta dawo da darajarta ta baya a matsayin cibiyar kasuwancin jihar.”

Gwamna Aliyu ya gabatar da daftarin kasafi

Ya jaddada cewa Gwamna Ahmed Aliyu na ci gaba da cika alkawuran da ya dauka ga al’ummar jihar tun a lokacin yakin neman zabe.

Baya ga hakan, majalisar zartarwar ta amince da daftarin kasafin kudin shekarar 2026 domin mikawa majalisar dokoki ta jihar Sokoto.

Kwamishinan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Abubakar Zayyana, ya ce an tsara kasafin ne bisa tsarin kashe kudi na matsakaicin zango domin tabbatar da gaskiya da daidaito wajen kashe kudaden gwamnati.

Kara karanta wannan

NLC: 'Yan kwadago sun saka ranar zanga zanga a jihohi 36 da Abuja

Zayyana ya bayyana cewa majalisar ta tattauna sosai kan daftarin kasafin kafin amincewa da shi domin mika wa majalisar dokoki.

Gwamnatin Sokoto za ta yi manyan ayyuka

Gwamnatin Sokoto ta ce za ta gina sababbin ofisoshi a hukumar alhazai ta jihar.
Gwamna Ahmad Aliyu na jihasr Sokoto ya na jawabi a wani taro. Hoto: @Ahmedaliyuskt
Source: Facebook

A wani bangare na daban, majalisar SEC din ta amince da bayar da kwangilar gina sabon ginin ofisoshi da kuma gyaran tsofaffin gine-gine a hukumar jin dadin alhazai ta jihar Sokoto.

Kwamishinan yada labarai da wayar da kai, Sambo Bello Danchadi, ya ce aikin zai lakume Naira 469,140,662.28.

Danchadi ya bayyana cewa kamfanin Assist-Me Solution General Services Ltd ne ya samu kwangilar, inda aka ware wa’adin watanni shida domin kammala aikin.

Kwamishinan ya ce an tanadi kashi 50 cikin 100 na kudin fara aiki, kuma babu tanadin karin kudi idan aka samu canji a aikin.

Ya kara da cewa wadannan ayyukan da aka amince da su na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na inganta harkokin kasuwanci da kuma karfafa ayyukan hukumomin gwamnati.

Gobara ta tashi a babbar kasuwar Sokoto

Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto cewa, mummunar gobara ta tashi a wani bangare na babbar kasuwar Sokoto da Asubahin ranar Talata 19 ga watan Janairun 2021.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya yi wa malamai babban gata a jihar Katsina

Bidiyon gobarar ya nuna ma'aikatan kwana kwana, yan sanda da jami'an hukumar kiyayye haddura ta kasa, FRSC da wasu yan kasuwa na kokarin kashe wutar.

A cikin bidiyon, an ga dandazon al'umma sun taru wasu sun hau kan motocci suna kallon yadda ake kokarin kashe wutar yayin da ake kokarin gano musabbabin gobarar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com