Halin da Bello Turji Ke ciki bayan Hallaka Na kusa da Shi, Ya Zargi Wasu Mayaka

Halin da Bello Turji Ke ciki bayan Hallaka Na kusa da Shi, Ya Zargi Wasu Mayaka

  • Majiyoyi sun bayyana cewa hatsabibin dan ta’adda, Bello Turji ya shiga tashin hankali a Sokoto bayan yi masa ta'asa
  • Hakan na zuwa ne bayan sojojin Najeriya sun kashe kwamandansa, Kallamu Buzu a kwanton-bauna da aka yi
  • Rahotanni sun nuna cewa Turji ya zargi wani kwamandansa saboda kuskuren da ya jawo mutuwar Buzu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - An ruwaito cewa fitaccen ta’adda, Bello Turji ya shiga damuwa sosai bayan kashe wani na kusa da shi.

Hakan ya biyo bayan kokarin sojojin Najeriya na kashe babban kwamandansa, Kallamu Buzu a jihar Sokoto.

Yanayin da Turji ya shiga bayan kashe kwamandansa
Hafsan tsaro, Olufemi Oluyede da Bello Turji. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Halin da Bello Turji yake ciki yanzu

Premium Times ta ce Turji ya fusata, inda ya yi barazanar ramawa, tare da zargin wani kwamandansa kan lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi suka ce hakan ya faru ne saboda kuskuren da ya kai ga mutuwar Buzu a farmakin da bai yi nasara ba.

Kara karanta wannan

Ganduje na fuskantar barazanar shari'a game da yi wa Hisbah kishiya a Kano

Mazauna yankin sun ce Buzu na taka rawa a matsayin wakilin Turji, yana tsoratar da manoma da karɓar haraji a madadinsa.

Yadda sojoji suka kashe Kallamu

Sojojin Runduna ta takwas da Operation Hadarin Daji sun yi kwanton-bauna inda suka kashe ’yan ta’adda 11 tare da kwato makamai da harsasai.

Sanarwar sojoji ta bayyana cewa aikin an yi shi ne kusa da Kurawa, inda kungiyoyin ta’addanci ke amfani da yankin wajen ketare hanya da kai hare-hare.

Sojojin sun sami sahihin bayanan sirri, suka shirya kwanton-bauna cikin sauri, suka fatattaki ’yan ta’addan cikin musayar wuta mai tsanani.

An kashe ’yan ta’adda 11 yayin da wasu suka gudu da raunukan harbi, sannan an kwace bindigogi AK-47, harsasai da sauran kayayyaki.

Yanayin da Bello Turji ya shiga bayan kashe na kusa da shi
Dan ta'adda, Bello Turji da ministan tsaro, Christopher Musa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Twitter

Fargabar da ake yi bayan mutuwar Kallamu

Mutuwar Buzu da wasu daga cikin mayakan Turji ta sa mazauna Sabon Birni farin ciki, domin sun sha wahala a hannunsa tsawon shekaru.

Wani mazauni Basharu Altine ya ce Buzu da Dan Jargaba sun dade suna tare da manyan makamai suna barazanar kai farmaki yankuna.

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: Matawalle ya tafi kotu, ya saka sunan malamin Musulunci

Ya ce bayan samun bayanan sirri, ’yan sa-kai da sojoji suka yi musayar wuta, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Buzu, Dan Jargaba da wasu.

Altine ya gargadi jama’a da jami’an tsaro su kasance cikin shiri saboda yiwuwar ramuwar gayya daga Bello Turji da mayakansa.

Gwamnatin Sokoto ta yaba da jarumtakar sojoji kan dakile harin da ake shirin kai wa ’yan kasuwa daga Tarah zuwa kasuwar Sabon Birni.

Mai ba gwamna shawara kan tsaro ya ce aikin sojoji ya hana mummunan lamari, ya nuna sadaukarwar da rundunar ke yi don kare rayuka.

An gano Turji da mayakansa a Sokoto

Mun ba ku labarin cewa rahotanni sun ce an hango fitaccen dan bindiga, Kachalla Bello Turji, tare da mayaka da dama.

Hakan na zuwa ne bayan daukar lokaci mai tsawo ba a ji duriyarsa ba duk wasu rahotanni na cewa yaransa na kai hari.

An tabbatar da cewa an gano mayakin ne a yankin Fadamar Kanwa na Sabon-Birni a jihar Sokoto da ke fama da rashin tsaro.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.