Babbar Magana: Wani Bam da Aka Dasa a kan Titi Ya Tashi da Mutane a Zamfara

Babbar Magana: Wani Bam da Aka Dasa a kan Titi Ya Tashi da Mutane a Zamfara

  • Wani bam da ake kyautata zaton 'yan ta'adda ne suka dasa shi ya tashi da matafiya a titin Gurasu zuwa Gwashi a jihar Zamfara
  • Rahotanni sun nuna cewa fasinjoji da dama sun jikkata da fashewar bam ta rutsa da su a yankin karamar hukumar Bukkuyum ranar Laraba
  • Tuni dai dakarun sojoji da jami'an sashen kwance bam suka dira yankin domin duba barnar da aka yi da kuma bincike

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Nigeria - Wani bam da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne suka dasa shi ya tarwatse da mutane a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya.

Lamarin dai ya auku ne a kan titin Gurusu zuwa Gwashi da ke yankin ƙaramar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara ranar Laraba da ta gabata, 10 ga Disamba, 2025.

Kara karanta wannan

Ganduje na fuskantar barazanar shari'a game da yi wa Hisbah kishiya a Kano

Jihar Zamfara.
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya, Zagazola Makama ya tabbatar da tashin wannan bam a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bam ya tashi da matafiya a Zamfara

Ya tattaro cewa fashewar bam din ta rutsa da fasinjoji da dama da ke cikin motar Toyota Eagle Eye, inda matafiyan suka ji raunuka amma har yanzu babu wanda ya mutu.

Rahoton ya ce bam ya tashi ne misalin ƙarfe 08:32 na safiyar Laraba, lamarin da ya sa direban motar da fasinjoji suka firgice kuma ya haddasa tsoro da fargaba ga sauran matafiya a hanyar.

Bayanai sun nuna cewa fasinjojin da ke cikin motar sun taso ne daga garun Gwashi zuwa wani wuri lokacin da al’amarin ya rutsa da su.

Dakarun sojoji sun kai dauki wurin

Dakarun sojojin rundunar Operation Fansan Yamma, tare da kwararrun jami’an sashen bincike da kwance bama-bamai, sun isa wurin cikin gaggawa.

Jami'an tsaro sun kai dauki wurin da bam din ya tashi domin bincike yankin don tabbatar da ba wani karin bam sun da aka dasa da kuma tantance barnar da fashewar ta yi.

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: Matawalle ya tafi kotu, ya saka sunan malamin Musulunci

Zagazola Makama ya kara da cewa ana ci gaba da ƙoƙarin tantance adadin mutanen da lamarin ya shafa, yayin da sojoji ke gudanar da aikin ceto tare da binciken ragowar nakiya.

Jami'an sojojin Najeriya.
Dakarun rundunar sojojin Najeriya a lokacin da suka fito aiki Hoto: @NigeriaArmy
Source: Facebook

Wa ya jagoranci dasa bam a Zamfara?

Ana zargin cewa wani fitaccen jagoran ‘yan bindiga mai suna Sadiku, wanda ke aiki tare da dabar Dogo Gide, shi ne ya jagoranci kai harin bam din, in ji rahoton The Cable.

Hukumomi sun gargadi matafiya da su yi taka-tsantsan tare da guje wa hanyoyi marasa cunkoso yayin da jami’an tsaro ke ƙara zurfafa sintiri a yankin.

Ba a samu jin ta bakin jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Zamfara, Yazid Abubakar ba lokacin da aka tuntube shi kan wannan lamari.

'Yan bindiga sun kashe mataimakin ciyaman

A wani labarin, kun ji cewa ’yan bindiga sun kashe mataimakin shugaban karamar hukumar Bukuyum ta jihar Zamfara, Hon. Mu’azu Muhammad.

Rahoto daga masu alaka da lamarin ya nuna cewa 'yan ta'adda sun kashe dan siyasar ne bayan sun karbi kudin fansa Naira miliyan 15.

Kwamishinan yaɗa labarai na Zamfara , Mahmud Muhammad Dantawasa, ya yi ta’aziyya ga iyalan mamacin da al’ummar Bukuyum, yana mai cewa kisan abin takaici ne matuƙa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262