'Ba a ba Mu Tsoro da Bindiga,' Sheikh Zakzaky Ya Fadi Wata Karama Ta Ƴan Shi'a

'Ba a ba Mu Tsoro da Bindiga,' Sheikh Zakzaky Ya Fadi Wata Karama Ta Ƴan Shi'a

  • Sheikh Ibraheem Zakzaky ya zargi gwamnatin Najeriya da gazawa wajen warware kisan da aka yi wa mambobin kungiyar Shi'a a Zaria a 2015
  • Jagoran 'Yan Shi'ar ya yi ikirarin cewa ƙungiyar na da miliyoyin mambobi, ya kuma ce mabiyansa mutane ne da 'ba a basu tsoro da bindiga'
  • El-Zakzaky ya bayyana hakan ne a lokacin da suke shirye-shiryen bikin cika shekaru 10 da 'kisan gillar' da ya ce sojoji sun yi wa 'Yan Shi'a

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Shugaban kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) da aka fi sani da Shi'a, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky, ya sake tabo batun kisan da aka yi wa 'yan kungiyar a Zaria a 2015.

A yayin da ya zargi gwamnatocin da suka gabata da na yanzu da gaza daukar mataki kan 'kisan gillar' da ya ce an yi masu, Sheikh Zakzaky ya ce "ba za a taba tsoratar da 'Yan Shi'a da bakin binda ba".

Kara karanta wannan

Kisan Zaria: Sheikh Zakzaky ya fadi abin da ya rage tsakaninsa da Buhari duk da ya rasu

Shugaban kungiyar Shi'a a Najeriya, El-Zakzaky ya ce mabiyansa ba sa jin tsoron bindiga.
Jagoran mabiya akidar Shi'a a Najeriya, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky. Hoto: @am_ghoulam.
Source: Twitter

'Yan Shi'a ba sa tsoron bindiga' - Zakzaky

El-Zakzaky ya yi wannan jawabi ne a wani taron manema labarai a ranar Laraba, gabanin babban taron cika shekara 10 da faruwar kisan 'Yan Shi'a a Zaria, in ji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana kungiyar IMN da 'ya'yan kungiyar bisa ƙarfin gwiwar da suke nunawa duk da suna ci gaba da fuskantar karfin jami’an tsaro.

Jagoran Shi'ar ya ce:

“A yawan mutane, ko da kana ƙinmu, ka san muna da miliyoyin mabiya. A bangaren jajircewa kuma, mun nuna wa duniya cewa bindigogi ba za su tsoratar da mu ba, domin mun fuskance su.
"Hotuna sun nuna yadda mutanenmu, wadanda ba sa rike da makami ko daya, suke ci gaba da dumfarar wadanda ke harbinsu da bindigogi.”

2015: Rikicin sojoji da 'yan shi'a a Zaria

Rikicin 2015 a Zaria ya faru ne lokacin bikin Maulud, inda mambobin IMN suka mamaye babban titin da ya ratsa garin, inda aka yi zargin sun hana hafsan sojoji na lokacin, Laftanar Janar Tukur Buratai, wucewa.

Kara karanta wannan

'Allah bai haramta ba,' Sheikh Gumi ya ce babu laifi yin sulhu da 'yan bindiga

Abin da ya fara a matsayin takaddama ya rikide zuwa tashin hankali bayan sojoji sun fara harbe-harbe, yayin da suka yi zargin cewa toshe hanyar ya jefa Buratai cikin hadari.

IMN ta musanta zargin toshe hanyar da hafsan sojan zai wuce ko jefa shi a hadari, tana mai cewa mambobinta ba sa dauke da makamai, kuma sojojin sun yi amfani da karfi fiye da kima.

A watan Yulin 2021 ne wata kotu a Kaduna ta sallami El-Zakzaky da matarsa Zeenat.
Jagoran mabiya akidar Shi'a a Najeriya, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky ya yi taron manema labarai. Hoto: @am_ghoulam.
Source: Facebook

Kotu ta wanke Zakzaky da matarsa Zeenat

A cikin sa’o’i bayan wannan, sojoji sun kaddamar da jerin hare-hare a wuraren IMN, ciki har da gidan El-Zakzaky, in ji rahoton Arise News.

Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam daga baya sun ce an kashe daruruwan mabiya akidar Shi'a, zargin da rundunar soji ta ƙaryata, in ji rahoton Punch.

Bayan shekaru da dama a tsare da rigingimun shari’a, a watan Yuli 2021 wata babbar kotun Kaduna ta sallami El-Zakzaky da matarsa Zeenat daga duk tuhumar da ake musu.

'Za mu hadu da Buhari a lahira' - El-Zakzaky

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky ya yi magana game da ko 'Yan Shi'a za su iya yafewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan faruwar 'waki'ar Zaria'.

Kara karanta wannan

Ta fasu: Muhuyi Magaji ya fadi dalilin da ya sa 'yan sanda suka cafke shi

Jagoran akidar Shi'a ya ce shi da Buhari za su tsaya a gaban Allah domin ya yi hisabi kan abin da ya faru a rikicin Zaria shekaru 10 da suka gabata, tun da yanzu tsohon shugaban ya rasu.

El-Zakzaky ya kuma zargi gwamnatin Buhari da ma gwamnati mai ci yanzu, da kin fitar da rahoton bincike na gaskiya, ko tausayawa iyalan 'Yan Shi'ar da abin ya shafa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com