NNPCL: Bututun Mai Ya Yi Bindiga, Ya Kama da Wuta a Delta
- Kamfanin mai na kasa NNPCL ya tabbatar da fashewar bututun mai a kusa da kauyukan Tebijor, Okpele da Ikporo a Gbaramatu, Jihar Delta
- An gano matsalar biyo bayan raguwar matsin iskar gas a bututun NGIC, amma har yanzu ba a san musabbabin fashewar ba
- Kamfanin ya ce ta fara daukar matakan gaggawa tare da hadin gwiwar hukumomi da shugabannin al’umma domin kare muhalli
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Delta – Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL) ya tabbatar da aukuwar fashewar bututun mai da 5.50 na yamma a kusa da kauyukan Tebijor, Okpele da Ikporo na masarautar Gbaramatu da ke Jihar Delta.
Fashewar bututn ta tada hankalin jama’a, ganin irin muhimmancin yankin a harkar iskar gas da man fetur, da rashin sanin abin da zai biyo bayan karar da aka ji.

Source: Getty Images
Nigerian Tribune ta wallafa cewa babban jami'in hulda da jama'a na kamfanin NNPC, Andy Odeh, ya ce binciken farko ya nuna cewa an samu raguwar matsin iskar gas a kan bututun Kamfanin Iskar Gas na NNPC (NGIC).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bututun mai ya fashe a Delta
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa ana zaton raguwar iskar gas da ke kai wa bututun na NGIC na daga cikin abin da ya haddasa fashewar bututn.
Sai dai Odeh ya ce har yanzu ba a tabbatar da ainihin musabbabin afkuwar lamarin ba, domin za a kammala cikakken bincike kafin sanar da sakamakon hukuma.
NNPC ta bayyana cewa abin da ya fi muhimmanci a wannan lokaci shi ne kare rayukan mazauna yankin da kuma kiyaye muhalli daga duk wata illa da fashewar ka iya haifarwa.
NNPCL ta dauki mataki kan bututn Delta
Odeh ya kara da cewa kamfanin yana da cikakken kudirin bin ka’idojin tsaro da kare muhalli a duk ayyukansa, kuma za a rika sanar da jama’a duk wani karin bayani da aka tabbatar yayin da bincike ke ci gaba.

Source: Twitter
A cewar sanarwar:
“Mun dauki dukkanin matakan gaggawa, kuma muna aiki tare da hukumomin tsaro, ma’aikatan kashe gobara da shugabannin al’ummomi domin daukar matakai cikin hanzari da hadin kai.”
NNPC ta bukaci jama’ar yankin da su kasance cikin shiri su kuma bi dukiyar jami’an tsaro da na gaggawa domin kauce wa duk wata barazana ga lafiyarsu.
Za a sayo da kadarorin NNPCL
A baya, mun wallafa cewa kungiyoyin kwadago biyu mafi karfi a fannin mai da gas a Najeriya, PENGASSAN da NUPENG, sun fito fili wajen sukar kudirin gwamnatin tarayya a kan zargin shirin sayar da kaya a NNPCL.
Kungiyoyin sun bayyana cewa akwai tsoro da takaici a kan yadda gwamnati ke shirin rage hannun jarinta a cikin kadarorin hadin gwiwa da kamfanin NNPCL ke kula da su, wanda zai jefa sashen a wahala.
Shugabannin kungiyoyin, Festus Osifo na PENGASSAN da Williams Akporeha na NUPENG, sun bayyana matsayinsu ne a wani taron manema labarai da aka yi a Abuja, tare da gargadin gwamnati.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

