EFCC Ta Fara Shari'a da Ministan Buhari a Kotu kan Tuhume Tuhumen Rashawa 8
- Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon Ministan Kwadago, Chris Ngige, kan tuhumar rashawa da almundahana a zarge-zarge takwas
- Ana zargin Ministan tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari da ba wa kamfanonin abokansa kwangiloli masu darajar sama da N2bn
- Hakanan ana tuhumarsa da karɓar kyaututtukan kuɗi sama da N119m daga wasu kamfanoni yayin da yake rike da mukamin minista
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC) ta gurfanar da tsohon Ministan Kwadago da Ayyuka, Dr Chris Ngige, a gaban kotu.
Ta gurfanar da shi gaban Mai Shari’a Mariam Hassan na Babbar Kotun Abuja da ke Gwarinpa inda ake tuhunmarsa a kan laifuffukan da suka danganci rashawa takwas, bisa shari’a mai lamba FCT/HC/CR/726/2025.

Source: Facebook
Channels TV ta wallafa cewa Ngige, wanda ya isa kotu da misalin 8:10 na safe tare da jami’an EFCC, shi kadai ne a jerin wadanda ake tuhuma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
EFCC ta fara shari'a da ministan Buhari
The Cable ta wallafa cewa a cewar takardar tuhuma da lauyoyin EFCC suka gabatar a ranar 9 ga Disamba 2025, ana zargin laifuffukan sun faru ne a lokacin da yake Ministan Kwadago a ƙarƙashin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
A tuhuma ta farko, ana zargin Ngige da amfani da matsayinsa na mai sa ido kan NSITF wajen ba wa Cezimo Nigeria Ltd kwangiloli bakwai da suka kai darajar N366.4m, saboda alakarsa da kamfanin.

Source: Facebook
A tuhuma ta biyu, ya kara ba wa Zitacom Nigeria Ltd kwangiloli takwas masu darajar ₦583.6m, duk ta hanyar amfani da mukaminsa don ba da fifiko ga abokansa.
A tuhuma ta uku kuma, an ce ya ba wa Jeff & Xris Ltd kwangiloli takwas masu darajar ₦362m, yayin da tuhuma ta hudu ta zarge shi da bai wa Olde English Consolidated Ltd kwangiloli hudu masu darajar ₦668m.

Kara karanta wannan
'Jami'ai 20 suka kutsa gidansa,' An ji yadda EFCC ta cafko ministan Buhari a Abuja
EFCC ta zargi Ngige da karban kyaututtuka
EFCC ta ce Ngige ya ba wa Shale Atlantic Intercontinental Services Ltd kwangiloli hudu da darajar ₦161.6m, lamarin da ya zama tuhuma ta biyar.
Dukkanin wadannan laifukan suna sabawa sashe na 19 na dokar yaki da rashawa ta 2000, wanda ya sa hukumar ta tafi gaban kotu.
A tuhuma ta shida, ana zarginsa da karɓar ₦38.6m ta hannun Cezimo Nig. Ltd ta cikin “Chris Ngige Campaign Organisation”, duk a lokacin da yake rike da mukaminsa na minista.
Tuhuma ta bakwai ta ce ya karɓi ₦55m daga Zitacom Nig. Ltd ta cikin “Chris Ngige Scholarship Scheme”, alhali kamfanin na da kwangila da NSITF.
A tuhuma ta takwas, an ce ya karɓi ₦26.1m daga Jeff & Xris Ltd ta cikin shirin tallafin karatunsa, duk a lokacin da yake gudanar da aikinsa a matsayin minista.
EFCC ta ce dukkannin wadannan laifuffuka sun sabawa sashe na 17(a) da 179(c) na dokar yaki da rashawa ta 2000. Ngige ya musanta tuhumar, sannan kotu ta dage zaman don ci gaba da sauraron shari’ar.
Jami'an EFCC sun kama Chris Ngige
A baya, mun wallafa cewa a ranar Laraba, aka samu jita-jita cewa an sace tsohon gwamnan Jihar Anambra kuma tsohon Ministan Kwadago, Dr Chris Ngige, lamarin da ya ja hankalin jama'a.
Wannan labari ya tada hankula musamman a tsakanin ’yan siyasa da mazauna yankin Kudu maso Gabas, ganin cewa an taba kai masa hari a watan da ya gabata, wanda ya jawo tsoro da damuwa a zukatan jama’a.
Amma hadimin Ngige, Chris Chukwuelobe, ya fito fili ya bayyana cewa babu wata sace mai gidansa, tare da tabbatar da cewa tsohon Ministan na hannun EFCC bayan jami'anta sun kama shi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

