Amurka: Trump Ya Kwace Babbar Tankar mai Mallakar Kamfanin Najeriya

Amurka: Trump Ya Kwace Babbar Tankar mai Mallakar Kamfanin Najeriya

  • Jami’an tsaron ruwan Amurka sun cafke tankar mai ta Skipper bayan samun bayanan sirri da ke zargin ta da satar danyen mai da wasu abubuwa
  • Amurka ta ce tankar na amfani da tutar Guyana ba bisa ka’ida ba, lamarin da ya kara jawo tambayoyi game da mallaka da ayyukanta
  • Masu ruwa da tsaki a harkar sufuri da man fetur sun nuna damuwa kan raunin dokokin kula da jiragen ruwa a Najeriya bayan kwace mai din

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Rundunar tsaron ruwan Amurka tare da hadin gwiwar sojojin ruwan kasar ta kama wata babbar tankar mai mallakar kamfanin Najeriya mai suna Skipper.

Rahoto ya ce an kama tankar mai din ne bayan zargin cewa tana da alaka da harkar satar danyen mai da wasu manyan laifuffuka na kasa da kasa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tarwatsa Fulani makiyaya da harbi, an sace shanu 168 a Filato

Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Business Insider Africa ta rahoto cewa an cafke jirgin da ya dauko tankar ne bayan wani dogon bincike da ya tattara bayanan sirri game da shi, nau’in kayayyakin da ya dauka da kuma shakku kan masu mallakar man.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da aikin a ranar 10, Disamba, 2025, yana mai cewa matakin na cikin kokarin Amurka na murkushe aikata laifuffukan teku da barazana ga tsaron kasa da tattalin arzikin man duniya.

Amurka ta kwace tankar man Najeriya

Rahoton Vanguard ya bayyana cewa Skipper, wacce tsohuwar tankar mai ce mai shekaru 20, ta shafe dogon lokaci tana yawo a tekun Yammacin Afirka da Kudancin Amurka.

Kodayake ana danganta mallakar ta da Thomarose Global Ventures da ke Legas, rajistar kasa-da-kasa ta nuna Triton Navigation Corp na Marshall Islands a matsayin mamallakinta.

Hukumomin kasar Guyana sun tabbatar cewa tankar ta yi amfani da tutar kasar ba tare da izini ba, abin da suka kira karya da yaudara.

Kara karanta wannan

Najeriya ta shigo da kayan abincin $15m daga kasar Amurka

An ce salon sauya tutar jirgi na daga cikin dabarun da masu laifin teku ke amfani da su don kauce wa dokoki ko sanya jami’an tsaro su kasa gano su.

Jami’an Amurka sun ce sun yi amfani da ikon doka wajen kwace tankar bayan gano yiwuwar kasancewarta cikin satar mai, fasa-kwabri da kuma safarar miyagun kwayoyi.

Martanin masana bayan kwace tankar man Najeriya

Shugaban CMS, Akin Olaniyan, ya bayyana cewa idan lamarin ya faru ne bayan tankar ta bar Najeriya, hakan na nuna rauni a tsarin harkokin jiragen ruwa na kasar.

Haka kuma, shugaban OGSPAN, Mazi Colman Obasi, ya bayyana cewa Najeriya na da babbar tankar mai irin wannan wacce za a ga ba ta aiki idan aka duba shafin CAC.

Shugaban SOAN, Otunba Sola Adewumi, ya ce ba zai yi tsokaci ba har sai ya samu cikakkun bayanai kan tankar da Amurka ta kwace.

Jirgin ruwa dauke da kayan mai
Wani babban jirgin ruwa dauke da danyen mai a teku. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Haka zalika, tsohon daraktan NIMASA, Temisan Omatseye, ya ce shi ma ya ji labarin ne kwanan kuma ba zai yi sharhi ba saboda karancin bayanai.

A nata bangaren, NIMASA ta ce ba ta da bayanai kai tsaye kan kama jirgin, inda kakakinta Edward Osagie ya bukaci a aiko da tambaya a hukumance domin a ba da amsa yadda ya dace.

Kara karanta wannan

Bello Turji ya sake bayyana, an gano shi da tulin mayaka a Sokoto

Bayan kwace mai, Trump ya gargadi Colombia

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya gargadi shugaban Colombiya da cewa zai kai masa farmaki.

Trump ya bayyana haka ne jim kadan bayan sojojin Amurka sun sanar da kwace wata tankar mai a kogin kusa da Venezuela.

Ya bayyana cewa idan shugaban Colombia bai mayar da hankalinsa ba, yana cikin wadanda zai saka kafar wando daya da su.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng