Jita Jita Ta Ƙare: Mataimakin Gwamna da Aka Garzaya da Shi Asibiti Ya Mutu
- PDP ta kawo karshen jita-jitar da ake yadawa game da mutuwar mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo
- A cikin wata sanarwa da ta fitar, jam’iyyar ta tabbatar da rasuwar Sanata Ewhrudjakpo jim kadan bayan ya yanke jiki ya fadi a ofishinsa
- Gwamnatin Bayelsa ba ta fitar da sanarwa ba tukuna, amma dai PDP ta miƙa ta’aziyya ga iyalai, gwamnati da jama’ar jihar baki daya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Jam’iyyar PDP ta tabbatar da rasuwar mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Lawrence Oboraw-Harievwo Ewhrudjakpo, a ranar Alhamis, 11 ga Disamba, 2025.
Legit Hausa ta rahoto cewa tun da sanyin safiyar Alhamis din ne aka fara samun tashin hankula kan lafiyar mataimakin gwamnan bayan rahotanni sun nuna cewa ya yanke jiki ya fadi a ofishinsa.

Source: Facebook
PDP ta tabbatar da mutuwar Mataimakin gwamna
A cikin wata sanarwa da ta fitar da yammacin Alhamis a shafinta na X, PDP ƙarƙashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki (SAN), ta bakin sakataren yaɗa labarai na ƙasa, Ini Ememobong, ta bayyana cewa mutuwar ta girgiza jam'iyyar.
Sai dai har yanzu gwamnatin jihar Bayelsa ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance game da rasuwar mataimakin gwamnan ba.
A cikin sanarwar, PDP ta bayyana Sanata Ewhrudjakpo a matsayin ɗan jam’iyya mai aminci da rikon amana, tana mai cewa rasuwarsa ta jefa jam’iyyar, musamman reshen Bayelsa, cikin tashin hankali da baƙin ciki.
PDP ta yi addu’ar Allah ya jiƙansa ya kuma bai wa iyalansa, gwamnatin jihar Bayelsa da al’ummar jihar haƙurin jure wannan babban rashi, in ji rahoton Channels TV.
Abin da PDP ta ce kan mutuwar Ewhrudjakpo
Sanarwar PDP ta ce:
“Jam’iyyar PDP ta girgiza matuka da samun labarin mutuwar mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Mai girma Sanata Lawrence Oborawharievwo Ewhrudjakpo. Wannan labari ya jefa mambobin NWC da daukacin jam’iyyar cikin baƙin ciki.”

Kara karanta wannan
Mataimakin gwamnan Bayelsa ya mutu? An gano gaskiyar halin da yake ciki a asibiti
Jam’iyyar ta bayyana cewa Ewhrudjakpo ya kasance ɗan siyasa nagari, mai tsayin daka ga gaskiya da akida, ba dan siyasar da ke canza ra’ayi saboda son kai ba.
PDP ta ce mataimakin gwamnan ya kasance “gwarzo a siyasa” wanda ya tsaya kan gaskiya har zuwa ƙarshen rayuwarsa.

Source: Twitter
Wanene mataimakin gwamnan jihar Bayelsa?
An haifi Sanata Lawrence Oborawharievwo Ewhrudjakpo a ranar 5 ga watan Satumba, 1965 kuma ya rasu a ranar 11 ga Disamba, 2025 yana da shekaru 60 a duniya.
Sanata Ewhrudjakpo ya kasance dan siyasa a Najeriya wanda ya zama mataimakin gwamnan jihar Bayelsa daga shekarar 2020 har zuwa lokacin mutuwarsa a 2025.
Shi ne kuma sanata mai wakiltar mazabar Bayelsa ta Yamma a majalisar Dattawa daga shekarar 2019 zuwa 2020, a majalisar dokokin kasa ta tara, kamar yadda Legit Hausa ta gani a shafin WikiPedia.
Mataimakin gwamna na shirin barin PDP
Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto cewa, Mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Lawrence Ewhrudjakpo, da Sanata Seriake Dickson na dab da barin PDP.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa Lawrence Ewhrudjakpo da tsohon gwamna kuma sanata mai ci, Seriake Dickson, na shirin ficewa daga jam'iyyar PDP.
Yayin da Sanata Dickson ya kasance mai sukar APC sosai a majalisar dattawa, Ewhrudjakpo ya ki bin Gwamna Douye Diri, wanda ya koma APC a Nuwamban 2025.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

