Abin da Ministan Tsaro Ya Ce ga Sojoji bayan Yunkurin Juyin Mulki a Benin

Abin da Ministan Tsaro Ya Ce ga Sojoji bayan Yunkurin Juyin Mulki a Benin

  • Ministan Tsaro, Christopher Musa ya yi magana game da matakin sojojin Najeriya bayan yunkurin juyin mulki a Benin
  • Musa ya yaba da saurin daukar matakin sojojin wurin dakile juyin mulkin da aka yi shirya yi a karshen mako
  • Ya ce dole rundunonin tsaro su kasance cikin shiri a ko da yaushe tare da yin aiki tare domin kare Najeriya da ƙasashen makwabta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya ya yabawa rundunar sojojin Najeriya game da lamarin Benin.

Musa ya yabawa dakarun ne bisa saurin daukar mataki lokacin yunkurin juyin mulki da aka yi a Jamhuriyar Benin wanda ya dauki hankali a Nahiyar.

Ministan tsaro ya yabawa sojoji kan yunkurin juyin mulki a Benin
Ministan tsaro, Christopher Musa da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Benin: Ministan tsaro ya yabi sojojin Najeriya

Musa ya yi wannan jawabi ne a birnin Abuja yayin bikin karin girma ga wasu manyan sojoji, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

'Za a kamo shi,' Benin ta gano kasar da sojan da ya so juyin mulki ya buya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce irin wannan aiki ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin yunkurin bai yi nasara ba domin kara kare kasa.

Ya bayyana cewa abin da ya faru ya sake nuna muhimmancin kasancewa cikin shiri a kowane lokaci domin kare Najeriya da abokanta makwabta.

A cewarsa:

"Ina jinjinawa rundunar sojoji bisa saurin martani da kwararrun matakan da kuka dauka wajen dakile juyin mulkin Jamhuriyar Benin. Wannan shi ne matakin da ‘yan Najeriya ke tsammani daga gare ku.”

Ya kara da cewa babu bangaren tsaro da zai iya yin nasara shi kadai, don haka ana bukatar hadin kai tsakanin Sojan Kasa, Sojan Ruwa, Sojan Sama da sauran hukumomin tsaro.

“Kalubalen da muke fuskanta na kasa ne, dole mu fuskance su tare da cikakken hadin kai."

- Christopher Musa

Hafsan sojoji ya jinjinawa jami'ansa a Najeriya
Sabon hafsan sojoji, Lafatanar-janar Waidi Shaibu. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Twitter

Hafsan sojoji ya jinjinawa dakaru a Najeriya

A nasa bangaren, Hafsan Sojin Kasa, Laftanal Janar Waidi Shaibu, ya ce Najeriya na da rawar takawa wajen kare tsaro da zaman lafiya a yankin Yammacin Afrika.

Kara karanta wannan

'Za a iya kara fuskantar juyin mulki a Afirka ta Yamma,' Femi Falana

Ya ce dole kasar ta ci gaba da tallafawa yakin da ake yi da tsattsauran ra’ayi da kuma kare dimokuraɗiyya.

Shaibu ya jaddada cewa rundunar sojojin kasa muhimmin ginshiƙi ce ta tsarin mulkin Najeriya, don haka sababbin hafsoshin da aka kara wa girma su sani cewa duk wani matakin da suka dauka yana da tasiri kan tsaron kasa.

Ya bukace su da su kara himma, su inganta dabarun aiki da kuma tabbatar da cewa sojojin da ke fagen fama suna amfana da jagorancinsu.

Channels TV ta ce Waidi ya shawarci wadanda ba a kara wa girma ba su kwantar da hankalinsu, yana cewa matsayi a rundunar sojoji ba ya zuwa sai da cancanta.

Benin: An gano maboyar dan tawaye

Kun ji cewa majiyoyi sun ce shugaban yunkurin juyin mulkin Benin ya gudu zuwa Togo bayan barin wuta da dakarun Najeriya suka yi.

Gwamnatin Benin na shirin neman a mika mata sojan, yayin da ECOWAS ta tura sojoji domin tabbatar da tsaro a muhimman wurare.

Rahotanni sun ce dakarun Faransa sun bada gudunmuwa bayan rundunar Benin ta yi fafutukar korar sojojin da ke son kifar da gwamna.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.