Mataimakin Gwamnan Bayelsa Ya Mutu? An Gano Gaskiyar Halin da Yake Ciki a Asibiti
- An samu sabani kan halin da mataimakin gwamnan Bayelsa, Lawrence Ewhrudjakpo yake ciki bayan an garzaya da shi asibiti
- Majiyoyi daga asibiti sun ce an kwantar da Sanata Ewhrudjakpo a ICU bayan ya yanke jiki ya fadi a lokacin da yake aiki a ofishinsa
- Wasu rahotannin kuma sun nuna cewa mataimakin gwamnan ya rasu, sai dai gwamnati ba ta tabbatar da wadannan rahotanni ba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bayelsa - Yayin da ake rade radin cewa mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo ya rasu, wasu rahotanni sun nuna cewa yana nan raye.
Legit Hausa ta rahoto cewa an garzaya da Sanata Lawrence zuwa asibitin gwamnatin tarayya (FMC) da ke Yenagoa, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa mintuna bayan isarsu.

Source: Twitter
Halin da mataimakin gwamna yake ciki
Jaridar Leadership ta rahoto cewa, Sanata Lawrence yana nan da rance, amma yana cikin mawuyacin halin da ba ya iya gane wanene a kansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce mataimakin gwamnan ya yanke jiki ya fadi a ofishinsa da misalin karfe 1:30 na rana, lamarin da ya jefa ma'aikatan gidan gwamnatin jihar a tashin hankali.
Masu tallafa masa ta fuskar tsaro da sauran hadimansa ne suka gaggauta kai shi asibiti, inda likitoci suka fara duba lafiyarsa nan take.
Bayan ba shi agajin farko a bangaren marasa lafiya da ke bukatar agajin gaggawa, sai kuma aka mayar da shi sashen marasa lafiya da ke bukatar kulawa ta musamman (ICU).
Wani hadimin mataimakin gwamnan, Mr. Doubara Atasi, ya tabbatar da lamarin, kuma ya ce mai gidansa yana cikin mawuyacin hali, amma yana samun kulawar likitoci.
Mataimakin gwamna 'yana aiki ba hutu'
Amma dai Mr. Doubara Atasi ya ce har yanzu ba a bayyana musabbabin wannan yanayi da mataimakin gwamnan ya shiga ba, in ji rahoton Vanguard.
Wasu majiyoyi daga gidan gwamnati sun ce Sanata Lawrence ya kasance yana aiki babu hutu a 'yan makonnin nan, lamarin da ake zargin ya jawo faduwarsa.
Wata majiyar gwamnatin Bayelsa, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa manema labarai cewa:
“Ya yanke jiki ya fadi ne ba tare da wata alamar rashin lafiya ba. Jikinsa ya yi tsanani tun ma kafin a samu damar kai masa dauki.”
Rahotanni na farko sun nuna yiwuwar mataimakin gwamnan ya kamu da matsalar zuciya ta farat daya, lamarin da ya sanya ya suma a ofishinsa.
Sai dai, hukumomin asibitin dai har yanzu ba su fitar da wata sanarwa ba, yayin da ake jiran sanarwar gwamnatin jihar a hukumance.

Source: Twitter
Rade-radin mataimakin gwamna ya mutu
Jaridar Sahara Reporters dai ta rahoto cewa mataimakin gwamnan Bayelsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo, ya mutu a asibiti jim kadan bayan da aka kai shi.
Jaridar ta ce wata majiya daga iyalan mataimakin gwamnan ne ta tabbatar da mutuwar, ba tare da ba da wani karin bayani a kai ba.
Sai dai, Legit Hausa ba ta iya tabbatar da wannan rahoto na mutuwar mataimakin gwamnan ba, don haka, ana jiran sanarwa daga gwamnatin Bayelsa a hukumance.
Mataimakin gwamna na shirin barin PDP
A wani labarin, mun ruwaito cewa, mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Lawrence Ewhrudjakpo, da Sanata Seriake Dickson na dab da barin PDP.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa Lawrence Ewhrudjakpo da tsohon gwamna kuma sanata mai ci, Seriake Dickson, na shirin ficewa daga jam'iyyar PDP.
Yayin da Sanata Dickson ya kasance mai sukar APC sosai a majalisar dattawa, Ewhrudjakpo ya ki bin Gwamna Douye Diri, wanda ya koma APC a Nuwamban 2025.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


