NYSC: An taba satifiket din Lawrence Ewhrudjakpo inji Jami’in Hukumar DSS

NYSC: An taba satifiket din Lawrence Ewhrudjakpo inji Jami’in Hukumar DSS

Hukumar DSS ta kasa ta ce an yi wasu canji a takardar shaidar bautar kasa na NYSC da aka ba mataimakin gwamnan jihar Bayelsa mai-ci watau Sanata Lawrence Ewhrudjakpo.

Shugaban sashen harkar shari’a na DSS, ya shaidawa kotun sauraron karar zaben jihar Bayelsa wannan yayin da ake sauraron korafin badakalar da ke kan Lawrence Ewhrudjakpo.

Babban jami’in DSS na kasa, Abdulsalam Ibrahim ya halarci wani zama da kotun ke yi a babban birnin tarayya Abuja, inda ya gabatar da takardun da aka bukaci hukumar ta kawo.

Lauyan da ke tuhumar Lawrence Ewhrudjakpo da yin karya game da takardunsa ya bukaci DSS su zo su bada shaida a kotu. A dalilin haka ne Ibrahim ya zo a madadin hukumar kasar.

‘Dan takarar jam’iyyar LM a zaben gwamnan jihar Bayelsa, Vijah Opuama, ya na zargin sanata Ewhrudjakpo da yi wa hukumar zabe na kasa, INEC, karya a takardun da ya mika mata.

KU KARANTA: Aji guda ya fito da Shugabannin kasa 2, Gwamnoni da Ministoci da-dama

NYSC: An taba satifiket din Lawrence Ewhrudjakpo inji Jami’in Hukumar DSS
Sanata Lawrence Ewhrudjakpo
Asali: UGC

Ibrahim ya fadawa Alkalin kotu cewa: “Ya mai girma, mai shari’a, a ranar 22 ga watan Fubrairu, 2020 mu ka samu takarda daga kotun Lugbe a Abuja, ana neman DSS ta yi bincike a game da takardar shaidar kauracewa bautar kasa da NYSC ta ba wani Lawrence Ewhrudjakpo, mataimakin gwamnan jihar Bayelsa a yau.”Jam’in ya ce sun gudanar da binciken.

Hukumar NYSC ta shaidawa DSS cewa an canza sunan dangin Ewhrudjakpo a jikin satifiket din. Sai dai Ibrahim ya ce Ewhrudjakpo ne ya nemi ayi masa wannan canjin suna da kansa.

Alkali Ibrahim Sirajo ya dakatar da wannan shari’a zuwa yau Talata inda za a saurari rokon da sanata Ewhrudjakpo ya ke yi na kokarin hana a gayyaci shaidar wanda ya ke tuhumarsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel