'Jami'ai 20 Suka Kutsa Gidansa,' An Ji Yadda EFCC Ta Cafko Ministan Buhari a Abuja
- Jami’an hukumar EFCC kusan 20 ne aka ce sun kutsa gidan tsohon ministan kwadago, Chris Ngige a Abuja, suka tafi da shi ofishinsu
- Fred Chukwuelobe, tsohon hadimin Ngige, ya ce jami'an ba su bari tsohon ministan ya sauya ko da kayan barcin da ke sanye jikinsa ba
- Tsohon hadimin ya ce akwai yiwuwar EFCC ta gurfanar da Ngige a gaban kotu a ranar Alhamis, inda lauyoyinsa za su gabatar da bukata
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Fred Chukwuelobe, tsohon hadimin tsohon ministan kwadago Chris Ngige, ya yi magana kan yadda jami'an EFCC suka cafke Ngigge a gidansa.
Tsohon hadimin ya yi zargin cewa hukumar EFCC na iya gurfanar da Ngige, tsohon gwamnan Anambra a gaban kotu bayan kama shi da aka yi a Abuja.

Source: Facebook
Yadda EFCC ta damko ministan Buhari
A wata sanarwa da Fred Chukwuelobe ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Ahamis, 11 ga Disamba, 2025, ya ce kusan jami’an EFCC 20 suka kutsa gidan Ngige.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Chukwuelobe ya ce gomman jami'an da suka zo daga ofishin EFCC na Wuse II sun mamaye gidan tsohon ministan da ke titin Justice Mohammed Bello, Asokoro, a ranar Talata.
Ya yi zargin cewa an “yi waje” da Ngige daga gidansa ba tare da an bar shi ya canza ko da kayan barcin da ke jikinsa ba
Chukwuelobe ya ce:
“Hukumar EFCC na iya gurfanar da tsohon ministan kwadago, kuma tsohon gwamnan jihar Anambra, Dr. Chris Ngige, a gaban kotu yau.
"Wasu jami'an hukumar EFCC kusan 20 da suka zo daga ofishin su na Wuse II ne suka 'damko' Dr. Ngige daga gidansa jiya a Abuja. Ba su bar shi ya canja kayansa ba, aka tafi da shi cikin kayan barcinsa.”
Tsohon minista ya rasa fasfonsa a Burtaniya
A kwanakin baya ne aka ba da Ngige “beli” bayan wata gayyata da EFCC ta yi masa, inda aka yi masa tambayoyi kan wasu batutuwa da ba a bayyana ba.
A cewar sanarwar, tsohon gwamnan, Ngige ya kasance yana hulɗa da masu binciken kuma yana bin dukkan sharuddan belinsa, ciki har da mika takardun tafiye-tafiyensa.
Chukwuelobe ya yi bayani cewa Ngige ya tafi ƙetare ne domin dalilan lafiya, amma dole ya dakatar da tafiyar bayan ya rasa fasfonsa a Ingila, in ji rahoton Punch.
Sanarwar ta kara da cewa:
“Ya kama hanya zuwa Amurka domin jinya, amma da ya isa Burtaniya yayin da yake kan hanya, ya rasa fasfonsa. Don haka sai ya dawo Najeriya. Ya samo takardun tafiya daga ofishin jakadancin Najeriya a Burtaniya da suka ba shi damar dawowa Abuja.”

Source: Twitter
EFCC za ta gurfanar da ministan Buhari
Ya ce bayan dawowarsa, Ngige ya rubuta wasiƙar sanar da EFCC game da rasa takardun tafiyarsa da dalilin da ya sa ba zai iya mika su nan da nan ba. Sai dai kafin ya mika wasiƙar, EFCC ta isa gidansa ta kama shi.
Chukwuelobe ya ce:
“Dr. Ngige ya bayyana mamakinsa kan kama shi, ganin cewa bai karya sharuddan belinsa ba, kuma yana taimakawa hukumar a aikinta yadda ya dace.
"An tattaro cewa za a gurfanar da shi gaban kotu, inda lauyoyinsa za su gabatar da hujjoji domin kotu ta ba da shi beli da kanta.”
Ya ƙara da cewa tsohon ministan bai yi tsammanin zuwan jami'an ba, kuma ya tabbatar da cewa Ngige ya kasance cikin sahun masu bin dukkan umarnin EFCC tun farko
'Yan bindiga sun farmaki tawagar Ngige
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu ‘yan ta'adda dauke da miyagun bindigogi sun bude wuta kan ayarin tsohon gwamnan Anambra, Dr. Chris Ngige.
Maharan sanye da kayan soja da ‘yan sanda sun bude wuta kan motar jami'an tsaro, suka kashe dan sanda, suka sace bindigarsa kamar yadda shaidu suka sanar.
Wani mai shago da ya fito da gaggawa don ganin abin da ke faruwa ya sha harbin harsasai, lamarin da ya sa ya yi asarar jini mai yawa aka kai shi asibiti.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


