Gwamna Abba Ya Nada Mace Ta Farko a Matsayin Shugabar Jami'ar Gwamnati a Kano

Gwamna Abba Ya Nada Mace Ta Farko a Matsayin Shugabar Jami'ar Gwamnati a Kano

  • Farfesa Amina Salihi Bayero ta zama mace ta farko a tarihi da za ta jagoranci jami'ar Northwest mallakin gwamnatin jihar Kano
  • Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya sanar da cewa Gwamna Abba ya amince da nadin Farfesa Amina
  • Abba ya bukaci masu ruwa da tsaki a jami'ar da sauran al'ummar Kano su taya sabuwar shugabar da addu'a domin sauke nauyin da aka dora mata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Farfesa Amina Salihi Bayero a matsayin shugaban jami'ar Northwest mallakin gwamnatin jihar.

Wannan nadi da Gwamna Abba ya yi, ya riga ya fara aiki tun a ranar 1 ga watan Disamba, 2025 bayan cika dukkan sharuddan zaben shugaban jami'ar.

Kara karanta wannan

Majalisa ta shiga tsakani, da yiwuwar a yafewa mutane bashin COVID 19

Gwamna Abba Kabir.
Gwamna Abba Kabir Yusuf a fadar gwamnatinsa da ke Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Alhamis, 11 ga Disamba, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba ya nada shugabar jami'ar Northwest

Nadin, wanda zai ɗauki shekaru biyar, ya biyo bayan shawarar Majalisar Gudanarwa na Jami’ar, inda aka gudanar da tsari mai cike da bincike da tantancewa cikin gaskiya da amana.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yaba wa shugaban majalisar gudanarwa ta jami’ar da mambobinta kan yadda suka tsaya kan cancanta da gaskiya wajen gudanar da zabin.

Ya kuma yi kira da a yi wa sabuwar shugabar jami’ar addu’ar Allah ya taimaka mata a sabon nauyi da ta ɗauka.

Takaitaccen bayani kan Farfesa Amina Bayero

Farfesa Amina Bayero babbar malama ce a fannin Analytical Chemistry kuma ita ce mace ta farko da ta kammala dogirin PhD a fannin Chemistry daga Jami'ar Bayero da ke Kano (BUK).

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Kanwar tsohon shugaban Najeriya ta riga mu gidan gaskiya

Ta rike manyan mukamai a harkar ilimi, ciki har da shugabar sashen koyar da ilimin na sinadarai da shugabar tsangayar kimiyya ta Jami'ar Bayero.

Haka zalika, Farfesa Amina Salihi Bayero ta rike mukamin Mataimakiyar Shugabar Jami’a (DVC) a bangaren gudanarwa da harkokin ilmi a Jami'ar Yusuf Maitama Sule, Kano.

Gwamna Abba da Farfesa Amina.
Gwamna Abba Kabir Yusufa da sabuwar shugabae jami'ar Northwest, Farfesa Amina Salihi Bayero Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Sanarwar gwamnatin Kano ta kara da cewa Farfesa Amina ta shahara saboda jajircewarta wajen bincike, shugabanci, da kula da ci gaban matasa masana kimiyya.

"Ana girmama ta sosai saboda gudummawarta a fannin bincike, ƙwarewar jagoranci, da jajircewarta wajen tallafa wa matasa masana kimiyya.
"Ana sa ran naɗinta zai ƙarfafa ingancin ilimi, ya kuma bunƙasa rawar da mata ke taka wa a manyan mukamai a fannin ilimi na Jihar Kano," in ji sanarwar.

Gwamna Abba ya ziyarci Kwankwaso

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai wa Kwankwaso ziyara har gida a Abuja domin nuna masa lambar yabon da aka ba shi saboda kyakkyawan jagoranci.

Jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso ya taya Gwamna Abba murna bisa wannan gagarumar nasara da ya samu, yana mai jinjina ci gaban da jihar Kano ke samu a karkashin jagorancinsa.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya jagoranci tawaga ta musamman zuwa gidan Sheikh Dahiru Bauchi

An dai bai wa Gwamna Abba lambar yabon ne bisa sauyin da ya kawo da kuma kyakkawan jagorancin da ya kafa a Kano tun bayan hawansa mulki a 2023.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262