Dama Ta Samu: Gwamna Abba Zai Dauki Sababbin Ma'aikata 4,000 a Jihar Kano

Dama Ta Samu: Gwamna Abba Zai Dauki Sababbin Ma'aikata 4,000 a Jihar Kano

  • Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta shirya daukar sababbin malamai 4,000 domin inganta koyarwa a makarantun firamare na fadin Kano
  • A taron da ya samu tallafin Birtaniya, an bayyana cewa fiye da kashi 40 na dalibai a Kano ba sa zuwa makaranta yadda ya kamata
  • Gwamnatin Abba dai ta dauki sama da malamai 15,000 daga 2023 zuwa 2025, matakin da ke nuni da jajircewarta wajen farfado da ilimi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano — Hukumar kula da ilimin firamare ta jihar Kano (SUBEB) ta bayyana cewa za ta dauki karin malamai 4,000 domin karfafa koyon karatu da lissafi a makarantun firamaren jihar.

Shugaban SUBEB, Yusuf Kabir, ya bayyana haka yayin taron duba sakamakon nazarin karatu na zango-zango na shekarar 2025 da aka gudanar a Kano.

Kara karanta wannan

Ta leko ta koma: Yadda Abdullahi Ramat ya rasa kujerar shugabancin hukumar NERC

Gwamna Abba Yusuf zai dauki sababbin malamai 4,000 a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na daga hannu ga matasan Kano a taron ba su tallafin N150,000. Hoto: @Kyusufabba
Source: Twitter

Za a dauki malamai 4,000 aiki a Kano

Jaridar Tribune ta rahoto cewa wannan taron ya samu tallafi daga gwamnatin Burtaniya a karkashin shirin PLANE, wanda ke aikin inganta karatu a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yusuf Kabir, wanda sakatariyar SUBEB, Hajiya Amina Umar, ta wakilta, ya ce duk da daukar sababbin malamai 4,343 a baya-bayan nan, har yanzu Kano na fama da karancin nagartattun malamai.

Shugaban hukumar ilimin firamaren ya ce an riga an tura bukatar daukar karin malamai 4,000, kuma masu neman aikin sun fara nuna sha'awarsu.

“Mun shirya bude cibiyoyi bakwai na rubuta jarabawar CBT a Wudil da Bichi da wasu kananan hukumomi domin gudanar da jarabawar cancantar shiga aikin cikin gaskiya."

- Yusuf Kabir.

Rashin zuwan dalibai makaranta a Kano

Yusuf Kabir ya kara da cewa jihar na kokarin rage rashin malamai da ke koyar da dalibai, inda yanzu ake samun malami daya yana koyar da dalibai 132, da fatan za a samu sassauci zuwa malami 1 ga dalibai 60.

Kara karanta wannan

Jami'in kwastam da ya yi fatali da cin hancin $50,000 ya samu karin girma

A yayin tattaunawar, masana sun nuna damuwa kan yadda rashin zuwan dalibai makaranta ke kara karuwa a wasu sassan jihar.

Fitaccen masani, Dr. Miswaru Bello, ya bayyana cewa kimanin 40% na daliban Kano ba sa zuwa makaranta akai-akai, yayin da rashin halartar malamai ya kai 12%.

Domin magance matsalar, Hajiya Amina Umar ta tabbatar da cewa ana duba yiwuwar samar da wurin kwana ga sababbin malamai musamman a yankunan karkara da ke fama da karancin ma’aikata.

Gwamnatin Abba da dage wajen inganta karatun yara a jihar Kano
Abba Kabir Yusuf tare da daliban makarantun sakandare na jihar Kano. Hoto: @Kyusufabba
Source: Twitter

Kokarin Abba kan inganta ilimi a Kano

A watan Satumba 2025, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dauki tsofaffin malamai 4,315 na shirin BESDA zuwa cikakken aikin gwamnati wanda ke dauke da albashi da fansho, in ji rahoton tashar Channels TV.

Tun hawansa mulki, Gwamna Yusuf ya amince da daukar malamai 5,500 a 2023, 5,632 a 2024, da 4,000 a Mayun 2025, domin cike gibi a fannin ilimin jihar.

Abba Yusuf ya sha nanata cewa daukar malamai ta zama ginshikin manufar gwamnatin sa ta farfado da ilimi bayan ayyana dokar ta-baci a bangaren ilimi.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba Kabir ya ciri tuta, an zakulo fannin da Kano ta zarce sauran jihohi

An karrama Abba kan zuba jari a ilimi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Kano ta zama jiha ta farko a Najeriya da ta ware 30% na kasafin kuɗinta na 2026 ga ilimi, wanda ya kai fiye da Naira biliyan 400.

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ce kasafin zai mayar da hankali kan gine-gine, horar da malamai, da gyaran tsarin ilimi baki ɗaya a fadin jihar.

Taron kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ya yaba wa gwamnatin Kano tare da ba ta lambar yabo, yayin da aka jinjinawa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com