Gwamna Zai Zuba Jarin Naira Biliyan 3.5 domin Inganta Makarantun Musulmai a Jiharsa

Gwamna Zai Zuba Jarin Naira Biliyan 3.5 domin Inganta Makarantun Musulmai a Jiharsa

  • Gwamnatin Jigawa karkashin Umar Namadi ta dauri damar gyarawa da inganta makarantun haddar Alkur'ani da aka fi sani da Tsangaya
  • Shugaban hukumar kula da makarantun Tsangya na Jigawa, Abubakar Maje ne ya tabbatar da haka yayin kare kasafin kudin 2026 a Majalisa
  • Maje ya lissafa muhimman ayyukan da gwamnatin ta tsara yi da Naira biliyan 3.5 da aka ware wa ilimin Tsangaya a kasafin kudin shekarar 2026

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jigawa, Nigeria - Gwamnatin Jigawa karkashin Gwamna Umar Namadi ta bayyana cewa ta ware Naira biliyan 3.5 a kasafin kuɗin 2026 domin inganta makarantun koyar da Alkur'ani Mai Girma watau Tsangaya.

Tsarin Tsangaya, wanda ya mayar da hankali kan haddar Alƙur’ani da koyar da ilimin addini, ya sha fama da kalubalen zamani, musamman rashin kayan aiki da ingantaccen tsari.

Kara karanta wannan

Dama ta samu: Gwamna Abba zai dauki sababbin ma'aikata 4,000 a jihar Kano

Gwamna Umar Namadi.
Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi a wurin taro Hoto: Umar Namadi
Source: Twitter

Shugaban Hukumar Ilimin Tsangaya ta Jigawa, Abubakar Maje, ne ya bayyana hakan yayin kare kasafin kuɗin hukumar a gaban kwamitin Majalisar Dokokin jihar, cewar The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda za a kashe N3.5bn a makarantun Tsangaya

Ya ce za a yi amfani da wani bangare na wadannan kuɗi wajen kammala manyan makarantun Tsangaya guda uku da ake ginawa a Kafin Hausa, Ringim da Dutse.

Abubakar ya ce a wadannan makarantu, gwamnati za ta samar da cibiyoyin koyon sana’o’i, gidajen malamai, masallatai, wadataccen ruwa da wutar lantarki.

Ya ce za kuma a ci gaba da ayyuka a tsofaffin makarantu bakwai da aka gada daga gwamnatin tarayya da gina sabbin ɗakunan karatu da ajujuwa a makarantu 60 da ke mazabu 30 a Jigawa.

Shugaban hukumar ya kara da cewa gwamnatin Jigawa za ta gina dakunan ba-haya a Tsangaya 30 a muhimmin mataki ne domin rage matsalar wurin ba-haya da almajirai ke fama da shi.

Kara karanta wannan

Jami'in kwastam da ya yi fatali da cin hancin $50,000 ya samu karin girma

Dubban dalibai za su amfana a Jigawa

A rahoton TVC, Abubakar Maje ya ce:

"Wannan shiri an yi shi ne don samar da damar ilimi ga yara sama da 6,000 a faɗin jihar jigawa."

Ya ce Naira biliyan 3.5 na kasafin kudin ya ƙunshi kuɗin shirin Hukumar Kula da ilimin Larabci da Musulunci ta Ƙasa (NBAIS) da kuma Shirin Inganta Ilimi a matakin farko (ABEP) wanda gwamnatin tarayya ta gabatar.

"Za a yi amfani da wani bangare na kudin wajen siyan ƙarin kayan koyarwa, gadaje da katifu da sauran makamantan su," in ji shi.
Makarantar Tsangaya.
Wasu dalibai suna daukar darasi a makarantar Tsangaya Hoto: Kamal A. Yahaya
Source: Facebook

An gano ma'aikatan bogi a jihar Jigawa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Jigawa ta samu nasarar bankaɗo ma'aikatan bogi waɗanda ke karɓar albashi daga cikin asusunta ba bisa ka'ida ba.

Da take zantawa da manema labarai a Dutse, kwamishinar kuɗi ta jihar, Hannatu Sabo ta bayyana cewa tuni aka kori ma'aikatan daga cikin jerin masu karɓar albashi.

Kara karanta wannan

Zambar N5bn: Gwamnatin Tinubu ta gurfanar da tsohuwar minista a kotun Abuja

Hannatu Sabo ta yi bayani kan yadda gwamnatin ke biyan albashi mai tsoka ga ma’aikatanta, tana mai cewa jihar na biyan kashi 100 cikin 100 na sabon mafi karancin albashi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262