Ana Wata ga Wata: Gwamnatin Tinubu Za Ta Karbo Sabon Rancen Naira Tiriliyan 17.8
- Sababbin bayanai sun nuna cewa gwamnatin tarayya na shirin karɓar bashin N17.89tn a 2026 domin cike gibin kasafi a 2026
- Rahoton gwamnati ya nuna kudaden shiga za su ragu daga N38.02tn a 2025 zuwa N29.35tn a 2026, don haka dole a ciyo bashi
- A 2026, gwamnati na shirin neman N14.31tn daga cikin gida da N3.58tn daga waje, yayin da za ta ciyo bashin N54.91tn a shekaru uku
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Sababbin bayanai daga ma’aikatar kasafi da tsare-tsare sun nuna cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta karbo sabon bashi na Naira tiriliyan 17.89.
Bayanan sun nuna cewa gwamnatin tarayya za ta karbo rancen ne a shekarar 2026 domin rufe gibin kasafin kudi da ke kara faɗaɗa saboda ƙarancin kudaden shiga.

Source: Twitter
Gwamnati za ta karbo bashin N17.89trn a 2026
Wannan adadi ya yi tashin gwauron zabi idan aka kwatanta da N10.42tr da aka tanada a 2025, wanda ke nufin karin bashin N7.46tr cikin shekara guda, in ji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wata takardar bayanin kasafi ta 2026 ABC-Circular, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa gibin kasafin kudi zai karu daga N14.10tr a 2025 zuwa N20.12tr a 2026.
Wannan karin N6.02tr ya nuna cewar matsa lambar kudi da bukatun gwamnati sun yi yawa fiye da abin da ake tsammani na shigar kudi a kasar.
Sai dai duk da wannan karin da aka samu, an kiyasta cewa gibin kasafi idan aka kwatanta da GDP zai ragu daga 4.17% zuwa 3.61%, saboda hasashen karin GDP a shekarar 2026. Ana sa ran ragin zai ci gaba da sauka zuwa 3.24% a 2027 da 1.92% a 2028.
Bashin da Najeriya za ta karbo a 2027-2028
A bangaren kudaden shiga kuwa, rahoton ya nuna raguwar N8.67tr daga N38.02tr a 2025 zuwa N29.35tr a 2026 — raguwar kusan 23%.
Ko da yake ana sa ran kudaden shiga za su dan murmure zuwa N31.53tr a 2027 da N34.90tr a 2028, hakan ba zai wadatar wajen rage dogaro da ciwo bashi ba.
Yadda za a ciro bashin N17.89tr: – N14.31tr daga cikin gida – N3.58tr daga masu bayar da lamuni na waje, kamar yadda Legit Hausa ta gani a shafin Budget Office na gwamnatin tarayya.
Binciken ya kuma nuna cewa daga 2026 zuwa 2028, gwamnatin tarayya na shirin karɓar bashin N54.91tr, inda kashi mafi yawa — N43.92tr — zai fito daga 'yan kasuwar cikin gida, yayin da bashin waje zai kai N10.98tr.

Source: Twitter
Masu sharhi sun gargadi gwamnatin Najeriya
Masu sharhi sun ce karin dogaro ga bashin cikin gida na iya kara matsa lamba kan kasuwar hada-hadar kudi da kuma tasiri ga ribar gwamnati da masu zaman kansu.
Shugaban cibiyar tallata kamfanoni masu zaman kansu, Dr. Muda Musa, ya ce ya zama wajibi Najeriya ta yi hattara da irin bashin da take karbowa.
Dr. Muda Musa ya ce ci gaba da karbo bashi na iya sanya wa a kasa iya sarrafa kasafin kasa ba tare da bashi ba, kuma a batar da kudaden kasar wajen biyan basussukan.
Tinubu ya karbo bashin $9.65bn
A wani labari, mun ruwaito cewa, Najeriya ta lullube kanta da bashin Bankin Duniya daga shekarar 2023 zuwa 2025, inda ta karbo kimanin dala biliyan 9.65.
Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin Bola Tinubu za ta karbi sabon rancen dala miliyan 500 daga Bankin Duniya karfin 19 ga watan Disamba, 2025.
Daga shekarar 2023 zuwa 2025 bashin da aka karbo karkashin IDA ya kai $7.30bn yayin da bashin IBRD ya kai $2.35bn da kuma tallafin $122.19m daga bankin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


