Gwamnatin Najeriya za Ta Dauki 'Yan Sanda 50,000, an Fitar da Sharudan Aikin

Gwamnatin Najeriya za Ta Dauki 'Yan Sanda 50,000, an Fitar da Sharudan Aikin

  • Hukumar PSC da rundunar ‘yan sanda ta kasa sun sanar da ranar buɗe shafin daukar sababbin jami'ai har 50,000 a Najeriya
  • Sanarwar ta nuna cewa masu neman aiki za su fara cike fom daga ranar 15, Disamba, 2025 har zuwa ranar 25, Janairu, 2026
  • Gwamnati ta tabbatar da cewa ba sai an biya kudi za a nemi aikin ba, kuma za a gudanar da shi cikin gaskiya da ka'ida

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar kula da 'yan sanda ta ƙasa (PSC), tare da rundunar ‘yan sandan Najeriya sun sanar da shirin fara daukar sababbin jami’ai 50,000 domin ƙarfafa tsaron cikin gida.

Wannan mataki na zuwa ne bisa umarnin shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu wanda ya bukaci a faɗaɗa yawan ma’aikatan rundunar.

Kara karanta wannan

Da gaske sojojin Najeriya su harbe mata masu zanga zanga har lahira a Adamawa?

Wasu masu neman aikin 'yan sanda
Masu masu neman aikin dan sanda a 2024. Hoto: Mahid Muazu Abuabakar
Source: Facebook

A cikin sanarwar da PSC ta wallafa a Facebook a ranar 11, Disamba, 2025, ta bayyana cewa za a bude shafin daukar ma’aikata a mako mai zuwa ga dukkan ‘yan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sharudan neman aikin 'dan sanda

A cewar sanarwar, masu neman shiga rukuni na General Duty su kasance masu takardun GCE, SSCE/NECO ko makamantansu da akalla cin darusa biyar ciki har da Turanci da Lissafi.

Ga rukuni na Specialists, ana buƙatar cin darusa hudu ciki har da Turanci da Lissafi, tare da samun gogewa ta akalla shekaru uku da takardun Trade Test a fannin da ya dace.

Wasu jami'an yan sanda a Abuja
Wasu jami'an 'yan sanda a birnin tarayya Abuja. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

An fayyace cewa dole mai neman aiki ya kasance cikakken ɗan ƙasa, kuma tsakanin shekaru 18 zuwa 25 a rukuni na General Duty, sai kuma shekaru 18 zuwa 28 a rukuni na Specialists.

Haka kuma, ana bukatar su kasance suna da lafiyar jiki da kwakwalwa, tare da tsayin da ya kai aƙalla tsayin 1.67m ga maza da 1.64m ga mata.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya yi zazzafar addu'a kan 'yan ta'adda da masu taimakonsu

Wata sanarwar shugaban sashen hulda da jama’a na PSC, Torty Njoku Kalu, ta ce:

“Hukumar tana kira ga dukkan ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa da suka cika sharuda su yi amfani da wannan damar domin ba da gudunmuwa wajen tsaron ƙasa.”

Punch ta wallafa cewa za a bude shafin daukar aiki a hukumance daga ranar 15, Disamba, 2025, tare da rufe shi a ranar 25, Janairu, 2026.

Yadda za a nemi aikin dan sanda a Najeriya

Dukkan masu neman aiki da rundunar za su tura bayanan su ne ta hanyar shafin hukumar da aka tanada a nan wanda za a bude a ranar 15, Disamba, 2025.

Hukumar ta ce a lokacin da ake samun ƙalubalen tsaro, ɗaukar sababbin jami’ai 50,000 zai taka muhimmiyar rawa wajen rage gibin ma’aikata, ƙarfafa tsaron unguwanni.

PSC ta sake tunatar da cewa:

“Aikin daukar sababbin ‘yan sanda ba ya buƙatar wani nau’in kuɗi a kowane mataki. Duk wanda ya shiga hannun masu yaudara ya yi kuka da kan kansa.”

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun kai mummunan hari garuruwan Fulani 4 a Kaduna

'Yan sanda sun kama mai safarar makami

A wani labarin, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta cafke wani mutum da ake zargi da safarar makamai a Abuja.

Bayan masa tambayoyi, wanda ake zargin ya bayyana cewa yana da niyyar mika makaman ne ga 'yan bindiga a Zamfara.

Jami'an 'yan sanda sun bayyana cewa ana bincike domin gano sauran mutanen da suke da alaka da wanda aka kama.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng