Dubu Ta Cika: An Kama Wanda Ya Jagoranci Kashe 'Dan Majalisa a Najeriya, Ya Fara Bayani

Dubu Ta Cika: An Kama Wanda Ya Jagoranci Kashe 'Dan Majalisa a Najeriya, Ya Fara Bayani

  • Hatsabibin dan ta'adda da ake zargi ya jagoranci kashe dan Majalisa a jihar Anambra ya shiga hannun dakarun 'yan sandan Najeriya
  • Rundunar 'yan sandan Anambra ta tabbatar da cewa ta kama wanda ake zargi da hannu a kisan Hon. Justice Azuka kuma har ya fara bayani
  • A watan Disamba, 2024, wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da dan Majalisar, daga bisani kuma suka kashe shi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Anambra, Nigeria - Rundunar ‘yan sanda ta jihar Anambra ta kama wani da ake zargi da kasancewa ɗaya daga cikin fitattun masu garkuwa da mutane da fashi da makami.

Kara karanta wannan

Majalisa ta shiga tsakani, da yiwuwar a yafewa mutane bashin COVID 19

Ana zargin dai hatsabibin mai garkuwa da mutanen, shi ne ya jagoranci kashe dan Majalisar dokokin jihar Anambra, Hon. Justice Azuka a bara.

Justice Azuka.
Tsohon dan Majalisar Dokokin Anambra, Hon. Justice Azuka da dakarun yan sanda Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

Tashar Channels tv ta tattaro cewa Hon. Azuka, mamba a Majalisar Anambra, ya fada hannun 'yan bindiga, sannan aka kashe shi a ranar 24 ga Disamba, 2024.

Wannann lamarin dai ya girgiza jihar Anambra tare da jawo ce-ce-ku-ce da Allah-wadai a fadin kasa.

An kama wanda ake zargi da kashe 'dan majalisa

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ikenga Tochukwu, ya ce dakaru sun kama wanda ake zargi, Ugochukwu Uzor, mai shekaru 26, yayin wani samame a Iyowa Odekpe, karamar hukumar Ogbaru, ranar 8 ga Disamba, 2025.

Ya tabbatar da samun nasarar kama dan ta'addan ne a wata sanarwa da ya fitar jiya Laraba, 10 ga watan Disamba, 2025.

Tochukwu ya ce jami'an sasshen RRT sun yi musayar wuta da Uzor kafin su rinjaye shi kuma su kama shi da ransa.

Kakakin rundunar yan sandan ya ce:

"Mun kwato karamar bindiga kirar cikin gida harsasai guda 11 daga wanda ake zargin."

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke wa dan sandan Najeriya hukuncin kisa, za a rataye shi har lahira

A cewar rundunar yan sanda, Uzor ya kasance shugaban wasu kungiyoyin ta’addanci da ke aikata laifuffuka a Anambra da jihohi makwabta.

Wanda ake zargi ya amsa laifinsa

Masu bincike sun lura da rubutun zane-zane a jikinsa da ke dauke da kalmomi kamar “ba yafiya” da “ba tausayi”, alamar halin ta’addanci da rashin tausayinsa.

A yayin bincike, Uzor ya amsa cewa shi ne ya jagoranci sace dan majalisar dokokin Anambra, Justice Azuka, sannan daga bisani suka kashe shi.

Kakakin rundunar yan sanda ya bayyana wannan kame a matsayin babbar nasara a kokarinta na tarwatsa kungiyoyin ta'addanci a jihar Anambra.

Sufetan sandan na kasa.
Sufeta-Janar na rundunar 'yan sandan Najeriya (IGP), Kayode Egbetokun
Source: Facebook

Tochukwu ya tabbatar da cewa ana ci gaba bincike domin gano sauran abokan aikinsa da suka tsere, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su kasance masu kai rahoto kan duk wani motsi ko abin da ba su yarda da shi ba domin taimakawa wajen tabbatar da tsaro.

'Yan bindiga sun kai hari kasuwa a Anambra

A wani labarin, kun ji cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai mummunan hari a kasuwar Afor da ke Nawfia a jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun kai mummunan hari garuruwan Fulani 4 a Kaduna

Shaidun gani da ido sun ce maharan sun bude wuta ba tare da kakkautawa ba, lamarin da ya jefa al’umma cikin tsananin tsoro da rudani.

Shugaban kungiyar Nawfia Progressive Union , Cif Daniel Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa hukumomin tsaro sun fara bincike.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262