Bayan Malami, EFCC Ta Sake Cafke Wani Ministan Buhari

Bayan Malami, EFCC Ta Sake Cafke Wani Ministan Buhari

  • An yi ta rade-radin cewa an sace tsohon Ministan Kwadago, Chris Ngige, lamarin da ya tayar da hankulan wasu jama'ar kasa
  • Sai dai hadiminsa, Chris Chukwuelobe ya fito ya ce ba sace shi aka yi ba, a hannun hukumar EFCC yake saboda wasu abubuwa
  • A daya bangaren, hukumar EFCC ta ki tabbatarwa ko musanta batun kama Ngige, duk da neman karin bayani da aka yi mata

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – A ranar Laraba, wata jita-jita ta bazu cewa an sace tsohon gwamnan jihar Anambra kuma tsohon ministan kwadago, Dr Chris Ngige.

Wannan ya tayar da hankali musamman a tsakanin 'yan siyasa da mazauna Kudu maso Gabas, lura da harin da aka kai masa a watan da ya wuce.

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya kwana a hannun EFCC, hukumar ta fara binciken asusun banki 46

Chiris Ngige da EFCC ta cafke
Tsohon minista, Ngige da EFCC ta kama. Hoto: Imran Mohammed
Source: Facebook

Sai dai Vanguard ta rahoto cewa daga baya hadiminsa, Chris Chukwuelobe, ya fito fili ya bayyana cewa ba a sace Ngige ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan karyata sace shi, a bayanin da ya yi, hadiminsa ya tabbatar da cewa Ngige yana hannun Hukumar EFCC.

EFCC ta kama ministan Buhari, Ngige

A cikin sanarwar da Chukwuelobe ya fitar, ya ce ya shafe sa’o’i yana amsa wayoyi daga ‘yan jarida da abokai da ke neman sanin ko gaskiya ne an dauke Ngige.

Ya bayyana cewa:

“Na shafe sa’o’i ina amsa kira daga mutane da dama suna tambayar gaskiyar labarin da ke yawo cewa an sace Dr. Chris Ngige.”

Ya ce wannan jita-jita ce kawai, amma gaskiyar magana ita ce:

“Ngige yana hannun EFCC. Ba a sace shi ba, ba wanda ya yi garkuwa da shi.”

Zarge-zargen da ake dangantawa da Ngige

Punh ta rahoto cewa Ngige ya taba fuskantar zarge-zarge masu nauyi tun bayan gudanar da mulkinsa a matsayin gwamnan Jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: EFCC ta kulle gidan tsohon minista, iyalansa na ciki a Abuja

Rundunar EFCC ta taba wallafa rahoto da ke zarginsa da karkatar da fiye da Naira biliyan 46 da aka ware wa kananan hukumomin jihar.

Ngige tare da marigayi Buhari
Ngige yana gaisawa da marigayi Buhari. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

A matsayinsa na ministan kwadago, hukumar ICPC tare da EFCC sun kuma taba tambayarsa game da zargin magudi a kwangiloli da kuma rade-radin almundahanar guraben ayyukan gwamnati.

EFCC ti yi shiru kan cafke Ngige

Duk da yayata labarin kama Ngige a ranar Laraba, hukumar EFCC ta ki fadin komai. Kakakin ta, Dele Oyewale, bai amsa tambayoyin da aka tura masa ba.

Chukwuelobe ya ce karin bayani zai fito daga baya idan an kammala wasu abubuwan da hukumomi ke aiki a kai, yana mai nuni da cewa a halin yanzu lamarin yana hannun masu bincike.

Malami ya kwana hannun EFCC

A wani rahoton, mun kawo muku cewa tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami ya kwana a hannun hukumar EFCC.

Rahotanni sun ce tsare Malami da EFCC ta yi nada alaka da wasu makudan kudi da aka kwato a lokacin yana gwamnati.

Tun a lokacin da hukumar ta gayyaci tsohon ministan, ya fito fili ya nuna cewa ba shi da wani laifi kuma zai wanke kansa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng