Bayan Yunkurin Juyin Mulki a Benin, Aliko Dangote Ya Samu Babban Mukami a ECOWAS

Bayan Yunkurin Juyin Mulki a Benin, Aliko Dangote Ya Samu Babban Mukami a ECOWAS

  • ECOWAS ta nada Aliko Dangote shugaban farko na 'Majalisar Kasuwanci Ta ECOWAS' domin karfafa zuba jari Yammacin Afrika
  • Sabuwar majalisar za ta hada masu zuba jari da gwamnati don rage dogaro da kasashen waje da karfafa jari na kasashen kungiyar
  • ECOWAS ta jaddada bukatar hadin kan kasashenta wajen yakar ta’addanci, inganta tattalin arziki da kuma kare tsarin dimokiradiyya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Attajirin dan kasuwar Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya samu babban mukami a kungiyar raya kasashen Yammacin Afrika watau ECOWAS.

Kungiyar ECOWAS ta nada Aliko Dangote, a matsayin shugaban farko na sabuwar majalisar kasuwancinta (EBC) da ta kafa.

ECOWAS ta nada Aliko Dangote shugaban sabuwar majalisar kasuwancinta.
Alhaji Aliko Dangote ya halarci wani taron 'yan kasuwa a Abuja. Hoto: Bloomberg
Source: Getty Images

Dangote ya samu babban mukami a ECOWAS

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an kafa sabuwar majalisar ne domin karfafa zuba jari daga masu zaman kansu da kuma inganta hadewar tattalin arziki a yankin.

Kara karanta wannan

Kuduri ya je gaban majalisa, ana so a ƙirƙiri sababbin ƙananan hukumomi a Kwara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ECOWAS, Omar Touray, ne ya sanar da hakan a yayin zaman majalisar ministocin ECOWAS karo na 95 da aka gudanar a Abuja ranar Laraba.

Omar Touray ya ce gogewar Dangote a harkokin kasuwanci a fadin Afrika ya sa ya dace ya ja ragamar majalisar, wacce manufarsa ita ce tattaro manyan 'yan kasuwa domin tattauna hanyoyin karfafa cigaban yankin.

Ya ce majalisar za ta taimaka wajen samar da muhimman tattaunawa tsakanin masu zaman kansu, gwamnatoci da hukumomin ECOWAS, tare da rage dogaro da jarin kasashen waje.

Omar Touray ya yi karin haske cewa idan aka ba bangaren kasuwanci dama, zai taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arziki da habaka hadewar kasashen Yammacin Afrika.

Muhimman ayyukan da ECOWAS ta sanya a gaba

Ya kuma nuna damuwa kan gibin kudaden wutar lantarki da ke gurgunta asusun makamashi na Yammacin Afrika (WAPP), inda ya nemi kasashe su tallafa wajen biyan bashin da ke hana cigaban kasuwar wutar lantarki ta yankin.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun sanya ƙafar wando ɗaya da NNPCL kan $42bn na kudin mai

A wani bangare kuma, ECOWAS tana ci gaba da kokarin cimma manufofinta na hada tsarin kudin yankin, karfafa kai daukin gaggawa a lokutan annoba da samar da sojojin hadin gwiwa don yaki da ta’addanci.

Ministan harkokin wajen Saliyo, Timothy Kabba, ya yi kira ga kasashen ECOWAS su dage wajen kare tsarin mulki da yin Allah wadai da duk wani yunkuri na juyin mulki a yankin, musamman a Guinea-Bissau da Jamhuriyar Benin, in ji rahoton Punch.

Haka kuma, Jakada Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta jaddada muhimmancin karfafa cinikayyar cikin gida, samar da damarmaki ga matasa da kare al’ummar yankin da suka kai fiye da mutane miliyan 400.

ECOWAS ta ce sabuwar majalisar kasuwancin da Dangote zai jagoranta za ta bunkasa kasuwancin Yammacin Afrika.
Shugaba Bola Tinubu ya halarci taron kungiyar ECOWAS da aka gudanar a Abuja. Hoto: @ecowas_cedeao
Source: Twitter

Tasirin Dangote a majalisar kasuwancin ECOWAS

Ana sa ran Dangote, wanda ya zama shugaban farko na cibiyar zai taka rawar gani wajen jawo hankalin masu zuba jari da daidaita ayyukan kasuwanci da manufofin hadin gwiwar tattalin arzikin ECOWAS.

Ana ganin yanzu ne aka fi bukatar kwarewar Dangote, la'akari da cewa Yammacin Afrika na fama da matsalolin tsaro da rikice-rikice a Mali, Nijar, Burkina Faso da Najeriya.

Sabon kwamitin zai taimaka wajen samar da dogaro da kai a tattalin arziki, inganta jari na cikin gida da karfafa ci gaba mai dorewa ga kasashen Yammacin Afrika.

Kara karanta wannan

'Za a iya kara fuskantar juyin mulki a Afirka ta Yamma,' Femi Falana

Benin: ECOWAS ta ayyana dokar ta baci

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ECOWAS ta sanya dokar ta baci a yankin Afirka ta Yamma bayan yunkurin juyin mulkin da sojoji suka yi a jamhuriyar Benin.

Yunkurin juyin mulki a Benin ya sake jefa nahiyar Afrika cikin fargaba, yayin da sojoji suka bayyana cewa sun kifar da gwamnatin Shugaba Patrice Talonm amma aka dakile su.

ECOWAS ta ce halin da ake ciki a Yammacin Afirka ya kai matakin “babbar barazana”, kuma ayyana dokar ta baci zai magance barazanar da juyin mulki ke haifarwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com