Gwamna Abba Kabir Ya Ciri Tuta, An Zakulo Fannin da Kano Ta Zarce Sauran Jihohi
- Kano ta zama jiha ta farko a Najeriya da ta ware kashi 30 cikin 100 na kasafin kuɗinta na 2026 ga ilimi, wanda ya kai fiye da Naira biliyan 400
- Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ce kasafin zai mayar da hankali kan gine-gine, horar da malamai, da gyaran tsarin ilimi baki ɗaya a fadin jihar
- Taron kungiyar gwamnonin Najeriya ya yaba wa gwamnatin Kano tare da ba ta lambar yabo, tare da jinjinawa gwamnan jihar, Abba Yusuf
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Jihar Kano ta ba da babban mamaki a taron ilimi na Najeriya da kungiyar gwamnoni (NGF) ta shirya a Abuja, inda ta fito a matsayin jiha mafi zuba jari a fannin ilimi a shekarar 2025/2026.
A taron da aka gudanar a dakin taro na Ladi Kwali Abuja, an bayyana cewa Kano ta ware fiye da Naira biliyan 400, wato kashi 30 cikin 100 na kasafinta na 2026, ga bangaren ilimi.

Source: Twitter
Kano ta ciri tuta a taron ilimi
Jaridar Tribune ta rahoto cewa zuba Naira biliyan 400 a fannin ilimi ya sa Kano ta kafa sabon tarihi na zuba jari a fannin ilimi a duk fadin Najeriya.
Taken taron na bana shi ne: “Hanyoyin Tabbatar da Dorewar Kuɗaɗen Ilimi: Gina Haɗin Kan Mutanen Gari da Masana Ilimi a Najeriya.”
Mataimakin gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda shi ne kwamishinan ilimi na manyan makarantu, ne ya jagoranci tawagar Kano.
Tare da Kwamared Gwarzo akwai kwamishinan ilimi, Gwani Dr Ali Haruna Makoda, shugabannin hukumomin ilimi da wakilan kamfanoni masu zaman kansu.
Ilimi ya samu kaso mai tsoka a kasafin Kano
Kano ta kasance daya daga cikin manyan masu daukar nauyin taron a matakin Golden Sponsor, alamar jajircewar gwamnatin jihar wajen sauya tsarin ilimi daga tushe.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana taron a matsayin dandalin gano matsaloli da samar da mafita mai ɗorewa ga tsarin ilimi.
Wannan ya yi daidai da shirye-shiryen Gwamna Abba Kabir Yusuf tun bayan ayyana dokar ta-baci a fannin ilimi a jihar Kano da ya yi a 2024, kamar yadda Legit Hausa ta rahoto.
Kason kudi mafi yawa da Kano ta ware zai tafi wajen gina sababbin makarantu, gyara tsofaffi, samar da kayan aiki, da horar da malamai, samar da damarmaki da kuma haɗa kowa da kowa a tsarin ilimi na jihar.

Source: Facebook
Gwamnatin Kano ta nemi tallafin masu zuba jari
A nasa jawabin, kwamishinan ilimi, Gwani Dr Ali Haruna Makoda ya ce Kano na da makarantu sama da 12,000, tare da dalibai fiye da miliyan 5.2, adadin da ya zarce jama'ar wasu jihohi hudu zuwa biyar.
Ya yi kira ga masu zuba jari da abokan hulda na kasa da kasa da su kara himma wajen tallafawa Kano saboda yawan al'umma da girman tsarin iliminta.
Taron ya gudana na tsawon kwana biyu, inda ya ja hankalin shugabanni, masana, hukumomin duniya, masu zuba jari da abokan hulda na gida da waje.
A karshen taron, an ba jihar Kano lambar yabo ta zakaruranci, wanda ya kara tabbatar da ita a matsayin jihar da ke jagorantar sauran jihohi a zuba jari a ilimi.
Kanawa sun jinjinawa Abba, sun ba shawarwari
Legit Hausa ta tattauna da wasu matasan Kano game da wannan karramawa da aka yi wa Abba da Kano, don jin ra'ayinsu da kuma neman shawarwari.
Abba Hassan Gezawa ya ce:
“Wannan karramawa da kungiyar gwamnonin Najeriya ta yi wa gwamnatin Kano abin alfahari ne, domin ya nuna yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fahimci cewa ilimi shi ne ginshikin kowanne irin ci gaba mai dorewa.
“A ganina, abin da ya kamata a kara mayar da hankali a kai shi ne inganta yadda ake koyarwa, a ba malamai horo, da kuma tabbatar da cewa ana amfani da kudaden da aka ware yadda ya kamata.
Isma’il Janguza kuwa cewa ya yi:
“Ba shakka, Gwamna Abba Yusuf ya cancanci yabo saboda fifikon da ya bai wa ilimi, domin Kano jiha ce mai yawan jama’a da matasa, kuma ba za a iya cimma ci gaba ba sai an saka jari sosai a ilimin su.
“Amma a lokaci guda, ina ganin ya dace gwamnati ta hada gwiwa da masu zaman kansu wajen samar da guraben horarwa da aikin yi, domin ka da a bar mtasa da takardu ba tare da an sanya shi a aika ce ba."
Zahra Mohammed Tarauni ta shaidawa Legit Hausa cewa:
“Ni dai shawarata ita ce a tabbatar da cewa ana amfani da wannan kudade wajen gina makarantu masu inganci, samar da tsaro a makarantu, da kuma tallafawa iyalai marasa galihu domin ‘ya’yansu su ci gaba da karatu.
"Haka kuma, ya dace a kara saka hannun jari a fannin kiwon lafiya da jin dadin jama’a, domin ilimi ba zai yi armashi ba idan al'umma na rayuwa babu lafiya."
Da muka tuntubi Kabir Mustapha Yusuf, shi ma ya ce:
“Mu tuni Gwamna Abba Yusuf ya nuna mana cewa ilimi shi ne ginshikin gina nagartacciyar al'umma, kuma ya ba shi fifiko sosai a kasafin da ake yi na jihar.
“Duk da haka, ina ganin ya kamata a hada wannan kokari da bunkasa sauran muhimman fannoni kamar noma, masana’antu da samar da ayyukan yi. Idan aka hada ilimi da wadannan fannoni, Kano za ta iya zama cibiyar ilimi da tattalin arziki a Arewa."

Kara karanta wannan
Bakin Wike ya jefa shi a tasko, ana so ya biya Naira biliyan 40 kan sukar dan siyasa
Abba ya gyara fiye da makarantu 1,200
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Kano ta bayyana cewa tana kan bakarta na tabbatar da dawo da martabar ilimi a dukkanin sassan jihar.
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ce zuwa yanzu, ta gyara fiye da makarantu 1,200 a ƙananan hukumomi 44, bayan haka kuma ta yi gyara a sassan Kano.
Haka kuma ta ware Naira biliyan uku don gyaran makarantu 13 na ’yan mata da aka rufe a baya, a wani yunkuri na dawo da darajar ilimi a jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



