Zaben 2027: Sanata Ahmed Lawan Ya Yi Babban Hasashe kan Makomar Tinubu a Arewa

Zaben 2027: Sanata Ahmed Lawan Ya Yi Babban Hasashe kan Makomar Tinubu a Arewa

  • Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan, ya yi tsokaci kan zaben shugaban kasa na shekarar 2027
  • Sanata Ahmed Lawan ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai samu kuri'u masu tarin yawa a yankin Arewacin Najeriya
  • Tsohon shugaban majalisar dattawan ya yi hasashen tagomashin da Tinubu zai samu idan aka zo kada kuri'a a zaben 2027

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban majalisar dattawa ta tara, Sanata Ahmad Lawan, ya hango makomar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Sanata Ahmed Lawan ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai samu sama da kaso 75 na kuri’un Arewa a zaɓen 2027.

Ahmed Lawan ya yi hasashe kan Tinubu
Sanata Ahmed Lawan tare da Shugaba Bola Tinubu Hoto: Ahmad Ibrahim Lawan
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Dr Ezrel Tabiowo, ya fitar.

Kara karanta wannan

"Kar ku zama 'yan kallo": Atiku ya yi muhimmiyar nasiha ga matasana Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Ahmed Lawan ya samu mukami

Ya yi kalaman ne bayan naɗa shi a matsayin uban kasa na kungiyar Tinubu House-to-House Network a Abuja.

Naɗin nasa ya samu tabbaci ne a lokacin da shugabannin kungiyar suka kai masa ziyarar ban-girma a majalisar tarayya, ƙarƙashin jagorancin shugabanta na kasa, Kwamared Yahaya Muhammad.

Sanata Ahmed Lawan ya ce samun kuri'un ba zai yi wahala ba kasancewar ’yan Arewa sun ba Tinubu kashi 63 na kuri’u a zaɓen 2023.

Tsohon shugaban majalisar dattawan ya yaba da kokarin kungiyar yana mai cewa:

“Na ji daɗi ƙwarai da kuka ga na cancanci na kasance a cikin jagororin kungiyar. Fata na shi ne ku ci gaba da faɗaɗa ayyukanku a faɗin kasar nan, musamman a Arewa.”

Ya yi yabo sosai ga gwamnatin Tinubu, yana mai cewa:

“Ina ganin Shugaba Bola Tinubu yana iyakar ƙoƙarinsa, kuma gwamnatin APC na cimma abubuwa da dama. Tattalin arzikin Najeriya ya daidaita kuma yana tafiya a hanya madaidaiciya.”

Kara karanta wannan

Daga 1960 zuwa 2027: Shugaba Tinubu zai kafa tarihi irinsa na farko a Najeriya

Me Ahmed Lawan ya ce kan Tinubu?

Sanata Ahmed Lawan ya kuma yi kira da a ci gaba da marawa Shugaba Tinubu baya a zaben 2027, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar da hakan.

Ahmed Lawan ya hango nasarar Tinubu a Arewa a zaben 2027
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan Hoto: Ahmad Ibrahim Lawan
Source: Facebook
“A zaɓen 2023, Arewa ta ba da kusan kashi 63 na kuri’un da suka kai Shugaba Tinubu kan mulki. Ra’ayina shi ne a 2027, mu ba shi sama da kashi 75 na kuri’un da za su dawo da shi kan mulki.”
“Shugaba Tinubu yana kokarin tabbatar mana da adalci. Don haka ya fi dacewa mu ci gaba da tsarin da muka sani, maimakon gwada sabon mutum da watakila ba zai iya rabin abin da muke gani yanzu ba.”

- Sanata Ahmed Lawan

Tinubu ya umarci janye 'yan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada umarninsa kan janye 'yan sanda daga gadin manya.

Mai girma Bola Tinubu ya umarci Sufeto Janar na 'yan sanda ya tabbatar da janye jami'an da ke gadin manyan mutane.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi maraba da ceto daliban Neja, ya ba jami'an tsaro sabon umarni

Shugaban kasa ya bayyana cewa ba zai yiwu a ci gaba da barin jami'an 'yan sanda suna gadin wasu tsiraru ba yayin da ake fuskantar matsalar rashin tsaro.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng