Kuduri Ya Je Gaban Majalisa, Ana So a Ƙirƙiri Sababbin Ƙananan Hukumomi a Kwara

Kuduri Ya Je Gaban Majalisa, Ana So a Ƙirƙiri Sababbin Ƙananan Hukumomi a Kwara

  • Hon. Raheem Ajuloopin ya gabatar da kudirin ƙirƙirar sababbin kananan hukumomi a Kwara domin kusantar da gwamnati ga jama’a
  • Kudirin ya zo ne tare da wani gyara ga dokar kamfanonin tsaro masu zaman kansu, domin ba su damar taimaka wa wajen samar da tsaro
  • Idan aka amince da kudirin Ajuloopin, Kwara za ta samu sababbin kananan hukumomi a karon farko, tun bayan gyaran doka na 1976

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara – Ɗan mjalisar wakilai mai wakiltar Ekiti/Irepodun/Isin/Oke-Ero daga jihar Kwara, Hon. Raheem Ajuloopin, ya gabatar da sabon kudirin doka gaban majalisa.

Hon. Ajuloopin ya gabatar da kudurin dokar ƙirƙiri sababbin ƙananan hukumomi a Kwara domin inganta mulki a matakin ƙasa da kuma ƙarfafa tsarin tsaro a fadin jihar.

An bukaci majalisa ta kirkiri sababbin kananan hukumomi a Kwara
Rt. Hon. Tajudeen Abbas na jagorantar zaman majalisar wakilai da ke Abuja. Hoto: @HouseNGR
Source: Twitter

Ana so a kirkiri sababbin kananan hukumomi

Kara karanta wannan

Gwamnoni 5 sun hada baki, sun gano hanyar kawo karshen 'yan bindiga gaba daya

Dan majalisar ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin watsa labarai ta yanar gizo, Jamiu Balogun, ya fitar a Ilorin, in ji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar, an ruwaito dan majalisar ya ce kudirin wani bangare ne na yunkurinsa na kusantar da mulki ga al’ummar da yake wakilta da ma daukacin 'yan jihar Kwara.

Bugu da kari, sanarwar ta ce kudurin zai kuma sauƙaƙa gudanar da mulki ta hanyar samar da ƙarin ƙananan hukumomi da za su iya amsa bukatun jama’a cikin gaggawa.

Hon. Ajuloopin ya bayyana cewa wannan kudiri na cikin kudurori biyu da ya gabatar kwanan nan, inda na biyun shi ne gyaran dokar 'kamfanonin tsaro masu zaman kansu (PGC Act).

Dan majalisa ya kare kudurin da ya gabatar

Wannan kuduri na biyu, a cewarsa, zai baiwa kamfanonin tsaro masu zaman kansu ikon taka muhimmiyar rawa a harkokin samar da tsaro a kasar nan.

A cewarsa, gyaran dokar zai ba jami’an ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro damar maida hankali kan binciken manyan laifuffuka, leƙen asiri, da gurfanar da masu laifi, yayin da kamfanonin tsaro za su tallafa a matakin farko na tsaro.

Kara karanta wannan

An fara maganar neman cafke Ganduje kan shirin kafa sabuwar Hisbah a Kano

Sanarwar ta rahoto dan majalisar yana cewa:

“Ƙirƙirar sababbin kananan hukumomi zai bayar da babbar gudummawa wajen ƙarfafa tsarin tsaron Najeriya.
"Yawan jama’a da girman yanki na tilasta kananan hukumomi aiki fiye da karfinsu. Sababbin kananan hukumomi za su inganta isar da ayyuka cikin gaggawa ga jama'a.”
An yi yunkurin kara yawan kananan hukumomin jihar Kwara tun a shekarar 2014
Taswirar jihar Kwara, inda ake so majalisa ta kara ma yawan kananan hukumomi. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Bukatar karin kananan hukumomi a Kwara

A tarihi, Kwara ta yi ƙoƙari wajen faɗaɗa tsarin kananan hukumominta, kamar yadda Channels TV ta rahoto a watan Oktoba, 2014.

A 2014, gwamnatin jihar ta kafa kwamitin mutum 14 don nazarin yiwuwar ƙirƙirar kananan hukumomi na LCDAs saboda karuwar jama’a da yawan bukatun gudanar da mulki.

Kafin haka, a ƙarshen mulkin tsohon Gwamna Mohammed Lawal a 2002, an ƙirƙiri wasu LCDAs, amma gwamnatin Dr. Bukola Saraki ta rushe su a 2003 saboda matsalolin kuɗaɗe.

Yanzu Kwara na ci gaba da aiki da ƙananan hukumomi 16 da aka kafa tun gyaran kudin mulki da aka yi a shekarar 1976.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Amurka mai sukan Najeriya kan tsaro ya sassauto, ya yaba wa Tinubu

Idan aka amince da kudirin Ajuloopin, tsarin mulki a jihar zai canza sosai, domin hakan zai ƙara yawan rumfunan mulki, fadada wakilci, kuma zai inganta tsaro.

Bukatu 46 na kirkirar jihohi na gaban majalisa

A wani labari, mun ruwaito cewa, majalisar wakilai na duba buƙatu kusan 46 na ƙirƙirar sababbin jihohi da buƙatu 117 na ƙirƙirar ƙananan hukumomi a Najeriya.

Majalisar na kuma duba buƙatu biyu na daidaita iyakokin jihohi da kuma kusan kudurori 86 na sauya kundin tsarin mulki da majalisar ta riga ta amince da su.

Duk wadannan bukatu, suna karkashin kwamitin majalisar wakilan da ke duba sauye-sauyen kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 wanda Benjamin Kalu ke jagoranta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com