Gwamnoni 5 Sun Hada Baki, Sun Gano Hanyar Kawo Karshen ’Yan Bindiga Gaba Daya

Gwamnoni 5 Sun Hada Baki, Sun Gano Hanyar Kawo Karshen ’Yan Bindiga Gaba Daya

  • Gwamnoni biyar da ke yankin Yarbawa sun samo mafita game da hare-haren yan bindiga a yankunansu
  • Sun goyi bayan kafa ‘yan sandan jihohi da kuma hukuncin kisa ga masu garkuwa, domin magance rikice-rikice
  • An bukaci gwamnoni su kafa tsattsauran dokar hana kiwo a fili, su ƙarfafa walwalar jami’an tsaro

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Gwamnoni a yankin Kudu maso Yamma sun gudanar da taro game da rashin tsaro da hare-haren yan bindiga.

Kungiyar da take a matsayin ta masu ruwa da tsaki kan lamarin tsaro a yankin, ta bayyana cikakken goyon baya ga bukatar kafa ‘yan sandan jihohi.

Gwamnoni 5 sun samo mafita ka yan bindiga
Gwamnonin yankin Kudu maso Yamma a taron da suka yi a Lagos. Hoto: Babajide Sanwo-Olu.
Source: Facebook

Gwamnoni sun gana kan matsalar tsaro

Rahoton Vanguard ya ce sun kuma amince da hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane, domin magance matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsaro: Malaman Musulunci, Kirista sun fadawa Tinubu gaskiya, sun hango barazana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron, wanda aka yi a Lagos, ya gudana ƙarƙashin jagorancin Aare Ona Kakanfo na Yarbawa, Iba Gani Adams, tare da sauran fitattun shugabannin yankin.

A cikin sanarwar da Gani Adams, Farfesa Kolawole Raheem da Amitolu Shittu suka fitar, shugabannin sun ce suna da ƙudurin ganin an shawo kan rikice-rikicen tsaro ta hanyar haɗin kai, sulhu da tsare-tsaren da suka haɗa al’umma.

Sun yi gargadin cewa akwai ci gaba da ƙoƙarin ‘yan bindiga na kammala mamaye yankin Kudancin Sahara duk da cewa yunƙurin ya fara tun karni na 1800.

Gwamnonin sun ce a yanzu garkuwa da mutane da ta’addanci sun zama makamin tarwatsa al’umma, tattara kuɗi don yaki, da kuma yunƙurin kwace gonakin noma da ma’adanan Yarbawa ta hanyar tashe-tashen hankula.

Gwamna ya jagoranci takwarorinsa domin magance tsaro
Gwamna Babaide Sanwo-Olu na jihar Lagos. Hoto: Babajide Sanwo-Olu.
Source: Getty Images

An bukaci kafa yan sandan jihohi

Shugabannin sun bukaci kafa ‘yan sandan jihohi nan take, tare da ɗaukar mazauna yankin da suka nuna ƙwarewa a harkar tsaro.

Kara karanta wannan

'Kisan Kiristoci': Tawagar Amurka ta shigo Najeriya, ta yi magana da Ribadu

Sun kuma yi kira da a inganta tsarin ‘yan sandan jihar ta hanyar haɗa dabarun gargajiya da sababbin fasahohi kamar jirgi marasa matuki, kayan sa ido na zamani, da sauran kayan yaki na fasaha.

Haka kuma, sun ba da shawarar a kafa shirin sa-kai na ƙwararrun Yarbawa a duk faɗin duniya, domin su ba da gudunmuwa ga tsaron yankin, cewar Punch.

Shugabannin yankin sun bada shawarar kafa 'Security Welfare Fund', domin inganta walwalar jami’an tsaro, da tabbatar da inshora, fansho da ƙarin tallafi.

Taron ya bukaci haramta kiwo a fili a duk faɗin Kudu maso Yamma, tare da cewa jigilar shanu ya kamata ya kasance ta manyan motoci ko jirgin ƙasa.

Gwamnatocin yankin sun kuma bukaci a gina katanga da shinge a bakin iyakokin Najeriya da Nijar, Chadi, Kamaru da Jamhuriyar Benin, domin hana shigowa ta haramtacciyar hanya.

Tinubu ya shawarci gwamnonin APC a Najeriya

An ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira da babbar murya ga gwamnonin APC kan halin da ake ciki a ƙasa.

Tinubu ya buƙaci gwamnonin na APC kan su ƙara ƙaimi wajen inganta rayuwar mutanen da suke ƙarƙashinsu a fadin kasar.

Kara karanta wannan

An buga rikici da Matawalle a ma'aikatar tsaro kafin Badaru ya ajiye aiki

Shugaban ƙasan ya nuna cewa wasu ƴan Najeriya sun fara ƙorafi kan yadda abubuwa suke tafiya a ƙasar tun kafin lokacin zabe.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.