Gwamnonin Yarbawa sun gabatarwa Majalisa jerin sababbin bukatu 6 da suke da su a Najeriya

Gwamnonin Yarbawa sun gabatarwa Majalisa jerin sababbin bukatu 6 da suke da su a Najeriya

  • Duka Gwamnonin Kudu maso yamma sun yi taro a kan sauya fasalin kasa
  • Gwamnonin shida sun yi tarayya a kan a zaftare karfin gwamnatin tarayya
  • Wadannan gwamnoni sun bukaci a canza salo da tsarin kananan hukumomi

A yunkurin yi wa tsarin mulki kwaskwarima, gwamnonin kudu na yamma sun kawo maganar a maida yankuna shida da ake da su a matsayin tarayyoyi.

Punch ta rahoto cewa kungiyar gwamnonin jihohin kudu masu yamma, sun kai wa majalisar tarayya takarda, dauke da jerin shawawarin da suka bada.

Gwamnonin suna so a rage karfin gwamnatin tarayya, sannan a kara wa jihohi da shiyoyyi iko.

KU KARANTA: Minista ya gana da Kungiyar Ibo a kan shari'ar Nnamdi Kanu

Jaridar ta ce gwamnonin sun gabatar wa ‘yan majalisa wannan bukatu ne a ranar Talatar da ta wuce, 6 ga watan Yuli, 2021, ba tare da kowa ya sani ba.

An yi wa takardar take da: ‘Proposals for the Review of the Constitution of the Federal Republic of Nigeria 1999 (As Amended): Presentation by South-West Governors’ Forum’

Kara karanta wannan

Malami ya amince Inyamurai su sa ido kan shari'ar Nnamdi Kanu, amma da sharadi

Gwamnonin da su ka halarci wannan taro su ne: Rotimi Akeredolu, Seyi Makinde, Kayode Fayemi, Gboyega Oyetola, Jide Sanwo-Olu, da kuma Dapo Abiodun.

Bayan taron, shugaban gwamnonin yankin, Rotimi Akeredolu SAN, ya ce kansu ya hadu a kan yadda za a yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya garambawul.

Gwamnonin Yarbawa sun gabatarwa Majalisa jerin sababbin bukatu 6 da suke da su a Najeriya
Gwamnonin Yankin kudu maso yamma Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Mun yi murna da Gwamnonin PDP su ka shigo APC - Buhari

Gwamnoni sun zauna da 'Yan majalisarsu, an kafa kwamiti

Gwamnan ya ce sun kafa kwamiti a majalisun tarayya a karkashin Sanata Opeyemi Bamidele da Hon. Femi Fakeye da kwamishinonin shari’a a kan wannan batu.

Gwamnonin suna so a sauya tsarin kananan hukumomi, a hana taba shugabannin kananan hukumomin. Sannan a hana gwamnatin tarayya kirkirar jiha.

Har ila yau gwamnonin suna so a bar jihohi su amfana da kudin da aka samu daga arzikin da ke cikin karkashin kasarsu, sannan a sake duban kason mai da gas.

Kara karanta wannan

Hotuna: Shugaba Buhari ya karbi gwamnonin PDP da suka sauya sheka zuwa APC

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya musanta rahoton dake yawo na nada gwamnoni a wasu yankunan jihar Borno da 'yan ta'addan Boko Haram suka yi.

Farfesa Zulum na jihar Borno ya jaddada cewa shi ke shugabanci a jihar Borno ba 'yan ta'adda ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel