"Ka Jefa Kanka a Matsala": PDP Ta Zargi Gwamna Fubara da Rauni bayan Komawa APC

"Ka Jefa Kanka a Matsala": PDP Ta Zargi Gwamna Fubara da Rauni bayan Komawa APC

  • Jam'iyyar adawa ta PDP ta ce sauya sheƙar Gwamna Simi Fubara zuwa APC rauni ne tare da jefa kansa a cikin matsala
  • PDP ta yi gargadi cewa wannan mataki da Mai girma Fubara ya dauka, ya fito da matsalar dimokuraɗiyyar Najeriya
  • Jam'iyyar ta bayyana fargaba a kan yiwuwar ko gwamnan na Ribas ya kamu da son wadanda suka uzzura masa a siyasa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Rivers – Jam’iyyar PDP ta bayyana sauya sheƙar da Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Rivers ya yi zuwa jam’iyyar APC a matsayin rauni da ya jawo wa kansa matsala.

Wannan martani na zuwa ne bayan da gwamnan ya sanar da ficewarsa daga PDP yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka yi a fadar gwamnati a Port Harcourt a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Awanni 24 bayan ganawa da Tinubu, Gwamna Fubara ya fice daga PDP zuwa APC

PDP ta yi takaicin sauya sheƙar Fubara
Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Source: Twitter

The Cable ta wallafa cewa lokacin sanarwar tasa, Simi Fubara ya yi zargin cewa bai samu kariya ko goyon baya daga PDP ba tun lokacin da rikicin siyasa ya dabaibaye jihar.

PDP ta caccaki sauya shekar Simi Fubara

Jaridar Punch ta wallafa cewa PDP ta ce wannan dalili da ya sa ya yanke shawarar komawa jam’iyya mai mulki ba dai-dai ba ne

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwa da Ini Ememobong, Jami’in Yaɗa Labarai na Kasa na PDP ya fitar, jam’iyyar ta ce Fubara ya dora kansa a kan hanya mara ɓullewa.

PDP ta ce duk wanda ya bi labarin rikicin siyasar Rivers zai gane cewa gwamnan ne ya jagoranci kansa zuwa halin da ya ke ciki a yanzu.

A cikin sanarwar, PDP ta yi addu’ar cewa Fubara kada ya fada cikin abin da ta kira "Stockholm syndrome" — wato yanayi da mutum ke nuna kauna ga wanda ya takura masa.

Kara karanta wannan

Ganduje ya hango matsalar da APC za ta iya shiga a Kano kan ayyana dan takara

Ta ce duk da haka, jam’iyyar tana fata alheri ga gwamnan a sabuwar tafiyarsa a sabuwar jam'iyyar da ya koma.

PDP ta yi Allah wadai da sauya sheƙar Fubara
Shugaban PDP na ƙasa, Kabiru Tanimu Turaki Hoto: Kabiru Tanimu Turaki
Source: Facebook

PDP ta ce dimokiraɗiyya ta samu matsala

PDP ta kara jaddada cewa sauya sheƙar Fubara ya sake tabbatar da koma bayan dimokuraɗiyya a Najeriya, musamman yadda jam’iyya mai mulki ke ƙoƙarin mai da kasar jam’iyya ɗaya.

Sanarwar ta ce:

“Shaidar gazawar tsarin dimokuraɗiyya ne, inda karfin mutane ya ɗara na cibiyoyi, sannan ana amfani da karfin gwamnati wajen murkushe masu adawa”.

PDP ta ja hankalin ‘yan Najeriya da al’ummar duniya cewa matsin lamba daga APC wajen takaita sararin siyasa wani sabon barazana ne ga dimokuraɗiyya.

Jam’iyyar ta ce wajibi ne kowa ya tashi tsaye don dakile abin da ta kira yunkurin maida kasar cikin danniyar lamurra da mulkin kama-karya na zabe.

Gwamnan Rivers ya sauya sheka

A baya, mun wallafa cewa Gwamnan Jihar Ribas, Siminialayi Fubara, ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP tare da magoya bayansa, inda suka koma APC.

Wannan sauyin jam’iyya ya faru ne sa’o’i 24 bayan da Gwamna Fubara ya kai ziyara ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnati da ke Abuja. Siminalayi Fubara ya bayyana sauya shekar nasa ne a lokacin da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a fadar gwamnatin Ribas da ke Fatakwal,

Kara karanta wannan

NNPP ta yi tsokaci game da muhimmancin kwankwaso, hadaka da APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng