'Hisbar Ganduje Za Ta Jawo Hallaka Rayuka a Arewa,' Tsohon Kwamishina Ya Yi Gargadi
- Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya gamu da suka kan kudirin kafa sabuwar Hisbah mai zaman kanta
- Injiniya Muazu Magaji Dansarauniya ya ce matakin na iya jawo rikicin addini da rarrabuwar kai a jihar Kano da Arewa gaba ɗaya
- 'Yan Najeriya sun yi martani inda wasu suka ce adawar siyasa ce ke haifar da irin wadannan zarge-zarge ga Ganduje
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, na shan suka bayan bayyana shirin kafa sabuwar Hisbah mai zaman kanta a jihar.
Lamarin ya zama abin ce-ce-ku-ce tun daga lokacin da aka fara magana game da sabuwar kungiyar a kafafen sada zumunta.

Source: Facebook
Tsohon kwamishinan Ganduje, Muaz Magaji Dansarauniya ya wallafa a Facebook cewa sabon tsarin zai iya tayar da tarzoma ko haifar da sabani tsakanin al’umma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A gefe guda, wasu masu tsokaci sun yi nuni cewa siyasa da jin haushi ne ke haddasa irin wadannan korafe-korafe game da kudirin Ganduje.
Kafa Hisbah: Muaz Magaji ya soki Ganduje
Tsohon kwamishinan ayyukan na Kano, ya ce kafa Hisbah da Abdullahi Ganduje yake shirin yi zai iya haifar da fitina a Kano da Arewa baki daya.
Ya ce matakin kafa sabuwar Hisbah tamkar tayar da hankalin jama’a ne a karshen rayuwar Ganduje, yana mai gargadin cewa hakan zai iya jawo rarrabuwar kai ga Musulmi.
Ya ce:
"Hisbar Ganduje wata sabuwar finita ce zai kunno a karshen rayuwarsa ga Kano da Arewacin Nigeria da za ta iya jawo hallakar rayuka da rarrabuwar kan Musulmi nan gaba!"
Sai dai Hamzeey Yakasai ya mayar da martani yana cewa Muaz Magaji yana magana ne saboda zafin cire shi daga mukamin kwamishina da Ganduje ya yi a baya.
Ra'ayin jama'a kan Hisbar Ganduje
Muhammad Salisu ya ce akwai wata manufa da ba ta da alheri ga Kano a cikin kungiyar Hisbah da Ganduje ya ke shirin kafawa.
A wani martani, Tijjani Murtala Zarewa ya yi kira da a guji yin adawa da take iya rikita al’umma a jihar Kano baki daya.
Ya ce rubutun Muaz Magaji bai dauke da wani abu illa tada hankalin jama’a, inda ya bukaci a yi taka-tsantsan wajen tsokacin da zai iya tayar da kura.
Wasu masu sharhi kamar Nura Abubakar sun yi nuni da cewa Ganduje ba ya neman zaman lafiya a jihar, yana mai cewa ya kamata gwamnati mai ci ta taka masa birki domin gujewa rikice-rikice.

Source: Facebook
Shi kuwa Faruk Garo ya tambayi dalilin da ya sa masu suka ba su yi irin wannan korafi ba lokacin da Ganduje ya kafa “Gidauniya” shekaru da suka gabata.
An bukaci a kama Ganduje kan kafa Hisbah
A wani labarin, mun kawo muku cewa wata kungiya ta yi kira ga 'yan sanda da hukumar DSS ta kama duk masu son kafa Hisbah a Kano.
Kungiyar ta ce abin da Ganduje ke son yi a jihar zai jawo tashin hankali da rusa hukumar Hisbah da gwamnati ta kafa.
Shugaban kungiyar ya bukaci gwamna Abba Kabir Yusuf ya fito fili ya nuna adawa da shirin kafa sabuwar Hisbar Ganduje.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


