Sabon Kwamandan Sojoji Ya Kawo Tsarin Kakkabe 'Yan Bindiga Gaba Daya
- An nada sabon kwamandan rundunar Operation Fansan, Manjo Janar Warrah Idris, wanda ya ce zai kawar da ’yan bindiga baki ɗaya
- Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa sabon kwamandan “ɗan gida ne” wanda saninsa da lamarin ya kara masa karfin guiwa
- Sabon tsarin yaki zai mayar da hankali kan shigar da al’umma lamuran tsaro saboda wasu ’yan ta’adda na fakewa a cikin jama’a
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara - An nada Manjo Janar Warah Idris a matsayin sabon kwamandan Operation Fansan Yamma, rundunar dake yaki da ’yan bindiga a jihohin Arewa maso Yamma.
Rahotanni sun nuna cewa sabon kwamandan ya sha alwashin cewa bai je Zamfara domin rage laifuffuka ba, sai kawar da 'yan ta'adda baki daya.

Kara karanta wannan
Gwamnoni 19 za su tara Naira biliyan 19 duk wata, an jero abubuwan da za su yi a Arewa

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanai game da ganawar Dauda Lawal da sabon kwamandan a shafin gwamnan na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Janar Idris ya shaida wa gwamna Dauda Lawal cewa ya zo jihar ne da tsari na musamman da zai maida hankali kan ingantacciyar dabarar yaki da kuma hada kai da al’umma.
Sabon tsarin yaki da 'yan bindiga
Janar Idris ya bayyana cewa sabon tsarin da yake shirin aiwatarwa zai fi karkata ga inganci da nazari mai zurfi kan yadda ake gudanar da ayyuka.
Tashar AIT ta rahoto cewa ya ce zama tare da al’umma da jin matsalolinsu kai tsaye zai taimaka wajen gano tushen matsalar.
A cewarsa, akwai abubuwan da suka shaida cewa wasu ’yan bindiga suna rayuwa ne cikin al’umma ko kuma suna da alaka ta kusa da wasu mutane a yankunan.

Source: Facebook
Wannan, kamar yadda ya bayyana, babban kalubale ne da dole a shawo kansa cikin hanzari don a samu zaman lafiya mai dorewa.
Ya kara da cewa rundunar Fansar Yamma, wacce ke kula da jihohi bakwai, za ta kara kaimi wajen dakile hanyoyin sadarwa da dabarun ’yan bindiga domin rage tasirinsu cikin makonni masu zuwa.
Zamfara za ta ba sojoji goyon baya
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana farin cikin sa da nada sabon kwamandan, yana mai cewa kasancewar Janar ɗan asalin yankin zai taimaka wajen fahimtar dukkan sassan jihar da kuma hanyoyin da ’yan bindiga ke bi.
Ya tabbatar da cewa gwamnatin Zamfara ba za ta taba tattaunawa da ’yan bindiga ba, saboda irin barnar da suke yi a kauyuka.
Gwamnan ya ce wannan matsaya da gwamnati ta dauka na da cikin matakai da dama da za su kara karfafa kokarin jami’an tsaro.
Dauda Lawal ya tabbatar wa rundunar Fansan Yamma cikakken tallafi, musamman a bangaren hadin kai, bayanai, kayan aiki da kuma abin da ya shafi dabarun yaki.
An kama mai saya wa 'yan bindiga makami
A wani labarin, kun ji cewa rundunar 'yan sandan birnin tarayya Abuja ta kama wani matashi da ake zargi da safarar makamai.
Bayan fara bincike, an gano cewa mutumin ya nemi taimakon wani sojan Najeriya game da sayen makamai da ya so yi.

Kara karanta wannan
Gwamna Radda ya yabi sulhu da 'yan bindiga, ya fadi amfanin da aka samu a Katsina
Binciken farko ya nuna cewa ya samu umarni daga wani dan uwansa ne da ya saye makaman ya turawa 'yan bindiga a Zamfara.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
